Addu'o'i

Addu’a Ga Mara Lafiya Idan Aka Ziyarce Shi

Addu’a Ga Mara Lafiya Idan Aka Ziyarce Shi:

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai yace masa;
لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .
La ba’asa tahoorun in sha’al-lah.
Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda.


أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)
Asalul-lahal-‘azeem rabbal-‘arshil-‘azeem an yashfeek (7).
Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al’arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).

Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu’a) sau bakwai face ya sami lafiya”.

See also  Addu'ar Da Mutum Zai Fada Idan Wani Al'amari Ya zo Masa na Farin Ciki ko na Bakin Ciki

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button