LafiyaShehu Rahinat Na'Allah

Macen da ke Jinin Haila PAD Nawa ya kamata tayi amfani dashi kullum ?

Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah
“PAD” wani audugar mata ne da suke amfani dashi a duk lokacin da Jinin haila yazo masu, Sukan yi amfani dashi a madadin tsumma da aka dade ana amfani dashi a kasar Hausa.

Mata da dama basa iya amfani da wannan audugar a lokacin da suke Jinin, sakamakon talauci ko rashi da suke fama dashi, mafi yawancin Mata suna amfani ne da tsumma, a madadin wannan audugar.

Kamar yadda kwararru a harkar lafiya suka tabbatar shine anaso Macen da take Jinin al’ada ta rika canja Pad duk bayan awa hudu (4 hours) Idan kuma tana amfani da Tampons ne (Shima wani nau’in auduga ne da mace ke sakawa a gabanta wanda zai rika tsotse jinin hailan nata) to ya kamata duk bayan awa biyu (2Hours) ta canja wani.

Amma wannan ya danganta ne da yanayin yadda jinin nata yake zuba, da kuma yanayin wadatar ta, da quality din shi karan kanshi Pad din.

Na tattauna da wata akan hakan ta bayyana mun cewa indai Pad din na Naira 400 ne Mace ke amfani dashi to ya kamata ne kullum ta rika amfani da guda uku, (Safe da rana, da kuma idan zata kwanta barci) amma koma dai yaya ne ta tabbatar mun cewa kar mace ta bari ya dade a jikin ta, domin kuwa zai iya haifar mata da wasu cututtuka.

Dan haka Wannan Kalubale ne ga Maza wadanda suke da mata ko kuma diya mata, ko kannai mata kai har ma da yayyai mata.

A matsayin ka na Miji ko Uba shin ka taba siyawa diyar ka ko matar ka Pad din da zatayi amfani dashi a lokacin da take Jinin haila ?

Haka a matsayin ka na yayan ta, ko kanin ta, ka taba siya mata PAD ko ka bata kudin ta siya ?

Shin ka taba bincika kaji yaya takeyi idan jinin yazo mata ?

Shin da Pad din take amfani ko kuma da tsumma wanda an yarda cewa yana haifar masu da cututtuka sakamakon wasu basu San yadda zasuyi amfani dashi ba, dan tabbatar da tsabtar jikin su ?

Tunda dai ka tabbatar dole duk wata sai wannan Jinin yazo mata, idan baka taba bata kudi ta siya ba, baka taba siyo mata ba, baka taba bada kudi a siyo mata ba, to ya kamata ka tambayi kanka shin yaya take yi idan jinin yazo mata ?

Da tsumma take amfani ?

Idan dashi ne ba zai iya sa mata da cuta ba ?

Ko kuma da Pad din take amfani ?

Idan dashi ne to a ina ta samo ?

Idan siya tayi a ina ta samo kudin/wa ya bata kudin ?

Sannan waye ya siyo mata ?

Idan kuma siya mata akayi ba da kudinta ta siya ba, to wa ya siya mata ?

Saurayin ta ?

Dan haka ina bawa iyaye Shawara da wadanda suke da kannai mata ko yayyai mata da su rika kula dasu ta wannan bangaren, dan kuwa diyar ka, ko kanwar ka, ko yayar ka, babu yadda za’ayi tazo tace maka wai ka bata kudi zata siya Pad, ko kuma tace idan ka fita ka siyo mata Pad saboda kunya, to ashe kuwa kaga ya dace idan zaka iya tunda Jinin hailan nan sai wata wata ne, to duk sati ka siyo mata ko 3 ne ka bata, ta aje, ko kuma ka bata kudin ta siya, Saboda ba wani tsada ne dashi ba, kuma koma yana da tsada ai lafiyar ta yafi komai.

Nayi hira da wata akan hakan, ta bayyanamun cewa yayanta ne yake siyo mata Pad din duk bayan Sati biyu, sai ta rika ajewa koda Jinin yazo mata to tana dashi a aje.

Dan haka PAD mai saukin kudin ana siyar dashi N300 ne, mai tsadar kuma yana kaiwa N1000+, matsakaicin kuma N400.

Yanzu Fi-sabilillahi, idan Jinin ta yanai mata kwana 3 ne kaga akalla zatayi amfani da Pad guda 9, mudauka tayi amfani da na tsakiyar ne dan Naira 400 kaga kenan a kwana 3 dinnan zatayi amfani da Pad din Naira 3,600 ne to dan Allah a ina zata samu wannan kudin duk wata ?

Dan haka gaskiya dole sai mun taimaka masu, domin kuwa rashin siya masu Pad din yakan sa mafi yawancin ‘yan mata tambayar samarin su kudi dan su siya, kuma hakan bai kamata ba, Saboda wani abu ka iya Shigowa.

Allah ya Kyauta !

Bissalam

See also  Ɗaurin Wata 6 ne Hukuncin wanda ya canjawa Motar shi Penti

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button