FacebookTarihi

Cikakken Tarihin Facebook

TARIHIN FACEBOOK.

Meta Platforms, Inc., yana kasuwanci kamar Meta kuma wanda aka fi sani da Facebook, Inc., da TheFacebook, Inc., kafanin fasaha Ne na Amurka da ke da alaƙa da ke Menlo Park, California. Kamfanin ya mallaki Facebook, Instagram, da WhatsApp, da dai sauran kayayyaki da ayyuka.

Zuckerberg ne ya kafa shafin sadarwa ta Facebook a ƙasar Amurka a shekara ta 2004.

An dai kafa shafin sadarwa ta Facebook ne a watan fabairun shekara ta 2004 a ƙasar Amurka. Kuma wasu matasa uku wato Zuckerberg da Chris Hughes da kuma Moskovitz ne suka ƙirkiro shafin a wannan shekarar. Wanda dai a kace ya jagoranci kafa shafin na Facebook tsakanin matasan dai shine Mark Moskovitz ɗan shekaru 23 a duniya dake karatun Sanin halayan ɗan Adam wato Psychology, a lokacin da yake ɗalibta a jami’ar Harvard dake ƙasar ta Amirka domin anfanin ɗaliban jami’ar.

Kafin kace kwabo wannan shafi ya samu ƙarɓuwa wajen sauran ɗalibai kimanin 1200 na jami’ar ta Harvard. Kuma cikin wata guda rabin ɗaliban dake karatun ƙaramin digiri na jami’ar sunyi rajista da shafin na Facebook. Haka dai wannan shafi ya rinƙa samun karɓuwa daga ɗalibai daga wannan jami’a zuwa wancan.

A shekarar 2005 ne kuma aka yiwa shafin rajista a matsayin facebook.com akan kuɗi Dalar Amurka dubu ɗari biyu. A watan satumban shekara ta 2005 kuma shafin na facebook ya isa ƙasar Birtaniya kafin zuwa sauran ƙasashen duniya. Kuma kyauta ne dai ake rajistan shafin na facebook.

A cikin 2008 Facebook ya zarce Myspace a matsayin gidan yanar gizon kafofin watsa labarun da aka fi ziyarta. Tare da gabatarwar Live Feed.

Facebook ya zama wani makami mai karfi a yunkurin siyasa, tun daga zaben shugaban kasar Amurka a shekara ta 2008 , lokacin da aka kafa kungiyoyin Facebook ( Facebook Group ) sama da 1,000 don goyon bayan ko dai dan takarar Democrat Barack Obama ko dan takarar Republican John McCain.

A Kolombiya an yi amfani da sabis ɗin don yin gangamin dubban ɗaruruwan mutane a zanga-zangar adawa da tawayen FARC da ke adawa da gwamnati. A Masar, masu fafutuka suna zanga-zangar adawa da gwamnatin Pres. Hosni Mubarak a lokacin boren 2011 su kan shirya kansu ta hanyar kafa kungiyoyi a Facebook.

A watan Oktoba 2021 Facebook ya sanar da cewa yana canza sunan kamfanin iyayensa zuwaMeta Platform. Canjin suna ya nuna fifiko kan “metaverse,” wanda masu amfani za su yi mu’amala a cikin mahalli na gaskiya.

Amma kuma don gane da hanyoyin samun kuɗi kuwa. Shafin wanda ya zama kamfani na samun kuɗaɗen sa ne daga tallace tallace da manyan kanfanoni da ƙanana keyi domin sayar da hajar su ga masu anfani da shafin ta facebook. Yanzu dai kanfanin da aka fara da Dalar Amurka dubu ɗari biyu, kanfanonin sadarwa irin su Google da Yahoo sun taya shi akan kuɗi Dala biliyan 2, A Shekarar 2010 wanda kuma Mr. Zuckerberg yace albarka.

A Shekarar Nan 2022 Darajar Kamfanin Ya kai Dala Biliyan Dari Biyar Da Talatin Da Takwas ( $538bn )

See also  TARIHIN SHIEKH MUHAMMAD NASURUDDIN ALBANI. مُحَمَّد نَاصِر ٱلدِّيْن ٱلْأَلْبَانِي الأرنؤوط)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button