LawShehu Rahinat Na'Allah

Hanyoyin da zaka bi idan kanaso ka zama kai ba Dan Nigeria bane

Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah
Nigeria kasa ce da take da dadin zama kuma kasa ce mai ‘yanci da walwala fiye da mafi yawa daga cikin kasashen Africa dama wasu kasashen turawa ko larabawa idan ka kalleta ta wasu bangarori, ka tambayi wasu ‘yan Nigeria da suke rayuwa a wasu kasashen duniya suyi maka Karin bayani akai.

Kamar yadda na fada a baya cewa Shugaban kasa yana da hurumin sallamar ka daga kasar shi sakamakon wulakanta ta ko zaginta, haka kaima kana da dama da hurumin da zaka fice daga kasar tashi daga lokacin da kaji tayi maka kuncin da kake ganin ba zaka iya Cigaba da rayuwa a matsayin dan asalin ta ba.

Mu duba Kundin tsarin Mulkin Nigeria na Shekarar 1999 da aka yiwa gyara inda Sashi Na 29 (Section 29) karamin Sashi na daya (Subsection 1) yace: “Duk wani Dan Nigeria baligi, da yake so yayi watsi da damarsa ta zama ɗan Asalin Nigeria zai iya yin hakan ta hanyar shelantawa a kafar da ta dace”

Har wayau dai karamin Sashi na (2) karkashin Sashi na (29) Babi Na Uku (Chapter 3) yace: “Da zarar shugaban ƙasa ya gamsu, ya kuma bayar da sanarwar watsi da wannan dama, to shikenan wanda yayi wannan Shelar (Renunciation) daga lokacin ya zama shi ba ɗan asalin Nigeria bane”

To Saidai kuma Shugaban Kasa yana da hurumi da damar kin amincewa da Shelar da kayi nason ficewa daga asalin dan kasar idan ya zama lokacin da kayi Shelar kayita ne lokacin da kasar take cikin halin yaki, ko kuma ka saba ka’ida wajen bayyanawa duniya cewa kanaso kayi watsi da damar ka ta zama dan Asalin Nigeria.
Don tabbatarwa mu duba Kudin tsarin Mulki Na Shekarar 1999 da aka gyara, Babi Na (3) Sashi Na (29) Karamin Sashi Na (3) (a) (b)

NB:
Wanda ake kira baligi a Kundin tsarin Mulkin Nigeria Shine: wanda yakai Shekara 18, ita Kuma mace da zaran tayi aure to kawai Shikenan ta zama Baliga a idon dokar Nigeria, domin tabbatarwa mu duba Babi Na (3) sashi na (29) ƙaramin sashi na (4) (a) (b) na Kundin tsarin Mulkin Nigeria.

Bissalam

See also  Idan naje Cire kuɗi sai suka Maƙale a POS ko ATM ko ONLINE zan iya zuwa kotu neman diyya ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button