Addu'o'i

Karanta Addu’o’in Tashi daga Barci

Yayi da ka tashi daga barci da akwai addu’o’i da manzon Sallallahu alaihi Wasallama ya koya mana mu riƙa yi.

A yayin da ka tashi daga barci sai kace:


“الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور”
Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba’ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi tashi yake.

(2)Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya farka da daddare ya ce;
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللّهُ وَحْـدَهُ لاَ شَـرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْـكُ وَلَهُ الْحَمْـدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، سُـبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْـدُ ِللهِ ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَاللهُ أكْبَرْ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوّّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ الْعَلِيِّ الْعَظِيمِ. رَبِّ اغْفِرْ لِي.
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa ala kulli shay-in kadeer, subhanal-lah, walhamdu lillah, wala  ilaha illal-lah wallahu akbar, wala hawla wala kuwwata illa billahil-aliyyil azeem. Rabbi ghfir li.

“Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara babu karfi sai da Allah, madaukaki mai girma, Ya Ubangijina! Ka gafarta mini”.
Wanda ya fadi wannan za a gafarta masa, idan kuma ya yi addu’a za a amsa, idan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za a karbi sallarsa.

“الحَمْدُ لله الذِي عَافَانِي في جَسَدِي ورَدَّ عَلَيَّ رُوحِي، وأَذِنَ لي بِذِكْرهِ”
Alhamdu lillahil-lathee AAafanee fee jasadee waradda AAalayya roohee wa-athina lee bithikrih.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya bani lafiya a jikina, kuma ya ya dawo mini da raina, kuma ya bani izinin ambatonsa.

See also  Addu'ar Wanda Ya Fitinu da Shakka a cikin Imani

إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلاَفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لآيَاتٍ لِّأُوْلِي الألْبَابِ *الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللّهَ قِيَاماً وَقُعُوداً وَعَلَىَ جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَذا بَاطِلاً سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّارِ*رَبَّنَا إِنَّكَ مَن تُدْخِلِ النَّارَ فَقَدْ أَخْزَيْتَهُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ *رَّبَّنَا إِنَّنَا سَمِعْنَا مُنَادِياً يُنَادِي لِلإِيمَانِ أَنْ آمِنُواْ بِرَبِّكُمْ فَآمَنَّا رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الأبْرَارِ * رَبَّنَا وَآتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَى رُسُلِكَ وَلاَ تُخْزِنَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّكَ لاَ تُخْلِفُ الْمِيعَادَ *فَاسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّي لاَ أُضِيعُ عَمَلَ عَامِلٍ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى بَعْضُكُم مِّن بَعْضٍ فَالَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخْرِجُواْ مِن دِيَارِهِمْ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَاتَلُواْ وَقُتِلُواْ لأُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلأُدْخِلَنَّهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ ثَوَاباً مِّن عِندِ اللّهِ وَاللّهُ عِندَهُ حُسْنُ الثَّوَابِ *لاَ يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُواْ فِي الْبِلاَدِ *مَتَاعٌ قَلِيلٌ ثُمَّ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمِهَادُ *لَكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْاْ رَبَّهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا نُزُلاً مِّنْ عِندِ اللّهِ وَمَا عِندَ اللّهِ خَيْرٌ لِّلأَبْرَارِ * وَإِنَّ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَمَن يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِمْ خَاشِعِينَ لِلّهِ لاَ يَشْتَرُونَ بِآيَاتِ اللّهِ ثَمَناً قَلِيلاً أُوْلَـئِكَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ إِنَّ اللّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ *يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اصْبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَاتَّقُواْ اللّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

Inna fi khalki s-samawati wa-l-ardi wa khtilafi l-layli wa n-nahari la-ayatin lu-uli-l-albab, al-ladhina yadhkuruna l-laha kuyaman wa ku’udan wa ala junubihim, wa yata fakkaruna fi khalki s-samawati wa-l-ardi, rabbana! Ma khalakta hadha batilan subhanaka fa-kina adhaba n-nar.
Rabbana! Innaka man tudkhili n-nara fa-kad akhzaytahu wa ma li-zalimina min ansar, Rabbana! Innana sami’na munadiyan yunadi li-l-imani an aminu bi-rabbikum fa-amanna. Rabbana! Fa-ghfir lana dhunubana wa kaffir ‘anna sayyi’atina wa tawaffana ma-‘a-l-labrar. Rabbana! Wa a’tina ma a’dtana ‘ala rusulika wa la tukhzina yawma-l-kiyamati, innaka la tukhlifu-l-mi’ad.
Fa-stajaba lahum rabbuhum anni la udi’u amala amilin minkum m-min dhakarin aw untha, ba’dukum min ba’din, fa-l-ladhina hajaru wa ukhriju min diyarihim wa udhu fi sabili wa katalu wa kutilu, la-ukaffiranna ‘anhum sayyi’atihim wa la-udkhilannahum jannatin tajri min tahtiha-l-anharu, thawaban min ‘indi l-lahi, wa l-lahu ‘indahu husunu-ththawab.
La yaghurrannaka takallubu l-ladhina kafaru fi-l-bilad, mata’un kalilun, thumma ma’wahum jahannamu wa bi’sa-l-mihad.
Ladini l-ladhina t-takaw rabbahum lahum jannatun tajri min tahtiha-l-anharu khalidina fiha, nzulan m-min ‘indi l-lahi wa ma inda l-lahi khayrun li-l-abrar.
Wa inna min ahli-l-kitabi la-man yu’minu bi-l-lahi wa ma unzila ilaykum wa ma unzila ilayhim, khash’ina li-l-lahi, la yashtaruna bi-ayati l-lahi thamanan kalilan. Uwla’ika lahum ajruhum ‘inda rabbihim, inna l-laha sari’u-l-hisab.
Ya ayyuha l-lahdhina amanu-sbiru wa sabiru wa rabitu wa t-taku l-laha la’allakum tuflihun. [Suratu Ali’imran 190-200)

See also  Karanta Addu'ar Sanya Sababbin Tufafi

Hakika a cikin halittar sammai da kassai, da sabawar dare da rana, lallai akwai ayoyi ga ma’abota hankula. (Su ne) wadanda suke ambatyon Allah a tsaye da kuma zaune da kuma kishingide, suke kuma tunani a kan halittar sammai da kassai (suna cewa): “Ya Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan abu a banza ba. tsarki ya tabbata gareKa, Ka kiyashe mu azabar wuta. Ya Ubangijinmu! Hakika Kai, duk wanda Ka shigar das hi wuta, babu shakka Ka kunyata shi. Azzalumai kuwa ba su da wasu   mataimaka. Ya Ubangiji! Hakika mu, mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa: “Ku yi imani da Ubangijinku”. Sai muka yi imani. To, ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, Ka kuma kankare mana miyagun aiyukanmu, Ka kuma karbi rayukanmu tare da mutane na gari. Ya Ubangijinmu! Ka bam u abin da Ka yi mana alkawari da shi a kan harshen Manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alkiyama hakika Kai ba Ka saba alkawari”. Sai Ubangijinsu ya amsa musu (cewa): “Hakika Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace; sashinku daga sashi yake. To, wadanda suka yi hijira, aka kuma fitar da su daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yaki, kuma aka kasha su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu; (wannan) sakamako ne daga Allah. Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai-komon wadanda suka kafirta a cikin garuruwa ta rude ka. Jin dadi ne dan kankani; sannan sakamakonsu wutar Jahannama ce, tir da wannan makwanta. Amma wadanda suka ji tsoron Ubangijinsu, suna da aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga wajen Allah; abin da kuwa ya zo daga wajen Allah shi ya fi ga managarta. Kuma hakika akwai daga ma’abota littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar zuwa gare su, suna masu kankan da kai ga Allah ba sa musanya ayoyin Allah da dan tamani kankani. Wadancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Hakika Allah mai hanzarta hisabi ne. yak u wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri, kuma ku rinjayi kafirai a cikin hakuri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta”. [Ali-Imran, 190 zuwa karshen surar].

See also  Karanta Addu'ar da ake Wa wanda ya sanya sabuwar tufa

Ku cigaba da kasancewa a cikin wannan shafi na edu.karatunturanci.com.ng domin samun ilimin addini har ma da na zamani

Allah ya sa mu dace! Ameen

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button