Tarihin Khalid Ibn Al-Walid

Takobin Allah: Tarihin Khalid Ibn Al-Walid Kashi Na Uku (3)


A Zamanin Sayyadina Abubakar (RA)


Khalid ya kasance a Hajjat al-Wida’ Ya goyi bayan Sayyadina Abubakar (RA) bayan wafatin Annabi Muhammad (SAW) wanda ya ba shi matsayi babba; Abubakar ya kasance yana goyon bayansa.

A Yakin Ridda, Sayyadina Abubakar (RA) ya umurci Khalid da ya ziyarci kabilar Tay (Tey’) a Aknaf, sannan ya ziyarci Tulayha Ibn Khuwaylid al-Asadi a Buzakha kuma a karshe ya ziyarci Malik ibn Nuwayra a garin Butah domin ya gayyace su zuwa ga Musulunci, idan suka ki gayyatar sai aka umarce shi da ya yake su. Yayi Galaba akan Tulayha wanda ya yi iƙirarin annabta kuma ya danne mabiyansa.


Yakin Musaylama al-Kadhdhab


A karshen 11/633 Khalid ibn Walid ya tafi Yamama ya yaki Musaylama al-Kadhdhab mai da’awar Annabci, da mabiyansa a Banu Hudayfa a yankin ‘Aqraba’. An kashe Musaylama kuma an murkushe magoya bayansa da gaske. Bayan haka Khalid ibn Mujja’a Murara al-Hanafi ya yi sulhu da shi. Sannan ya auri ‘yar Mujja’a.


Yaki da Iran


A karshen 11/Fabrairu 633 ko kuma a watan Muharram 12/Maris-Afrilu 633 Sayyadina Abu Bakr (RA) ya umurci Walid da ya yi tattaki daga Yamama zuwa Iraki domin ya mamaye yankunan da ke karkashin ikon Iran (Mesopotemia).

A bisa umarnin Abubakar Khalid ya fara yakinsa a al-Abila da ke gabashin Basra kusa da kogin Tigris, kuma ya ci yankuna a Mesopotamiya da suka hada da Madhar, Walaja, Ullas (Nahr al-Dam) da Amghishiya. A shekara ta 12/633-4 bayan ya ci Al-Hira hedkwatar Lakhmids, ya yi nasarar kame wasu muhimman garuruwan Sawad ta hanyar yaki ko zaman lafiya.

A ranar 25 ga watan Zul-qa’da 12/31 ga Janairu 634 lokacin da Khalid ya dawo al-Hira, ya rabu da sojoji a asirce ya tafi Makka domin yin aikin Hajji . Daga nan sai ya koma cikin rundunarsa cikin gaggawa.
See also  Takobin Allah: Tarihin Khalid Ibn Al-Walid Kashi Na Biyu


Yakin Siriya (Levant)


Bayan ya ci yankuna a Iraki, Sayyadina Abubakar (RA) ya umarci Khalid ibn Walid ya sanya al-Muthanna ibn Harith mai kula da sojojin musulmi a Iraki kuma nan da nan tare da sojoji da yawa suka tafi Siriya (Levant) don tallafawa sojojin musulmi. Da isowarsa sai ya karbe ragamar rundunar.

A cewar masana tarihi da dama, Khalid da sojojinsa sun tashi daga al-Hira ko Aynul Tamr a watan Rabi’I ko Rabi’ na biyu 13/Mayu-Yuni 634. sun wuce cikin yanayi mai tsanani a cikin jejin Sham daga Qaraqir a gabas zuwa Suyi a yamma cikin kwanaki biyar ko takwas tare da shiryarwa ta musamman ta Rafi’u b. Umayr al-Ta’i ya isa kusa da Sham.

Khalid ya ci garuruwan da suka hada da Dumat al-Jandal , Tadmur da Marj Rahit a kan hanya sannan ya shiga rundunar musulmi a Basra. Sannan musulmi suka kewaye garin har suka mika wuya cikin lumana.


Yakin Yarmuk da Ajnadayn


Masana tarihi sun sami sabani game da ranakun muhimman yaƙe-yaƙen guda biyu na Ajnadayn da Yarmuk. Bisa ga rahotannin tarihi Khalid da sauran sojojin musulmi da ke kusa da Damascus sun koma yankunan kudancin kasar domin tallafawa sojojin Amr ibn al-‘As a Palastinu domin murkushe Rumawa da suka taru a Ajnadayn (wani gari a Palastinu). Sun kai wa Romawa hari a ranakun 18 ko 28 ga Jumada I (ko 2 ko 28 ga Jumada na biyu) a ranakun 13/20 ko 30 ga watan Yuli (ko 3 ko 29 ga Agusta) 634 suka yi nasarar fatattakar su da kakkausan Yaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button