YADDA ZA KUYI BOLD NA TEXT A FACEBOOK
Wasu mutanen suna da bukatar suga sunyi bolding na text dinsu a facebook, musamman ma heading, wasu kuma italic suke so su saka ma text din nasu, hakan yasa wasu har sai sunyi downloading na wani keyboard da zai basu damar chanja font.
Ga hanya mafi sauki, wadda ba sai anyi amfani da wani keyboard app ba:
1- Da farko za kuje cikin browser sai ku rubuta Bold text generator sai kuyi search, bayan result din ya fito sai ku shiga na farkon.
2- Zai nuna maku wani filin rubutu guda biyu kamar yadda kuka gani a hoto na 2, sai ku danna filin na farko, domin yin rubutu.
3- Misali sai mu rubuta “Facebook” a filin na farko, za kuga ya fito a fili na 2 da siffa ta bold, sai ku za6i wanda kuke so, sai kuyi copy nashi.
4- Sai ku tafi cikin facebook dinku wajen post sai kuyi paste na rubutun da kuka yi copy din, sai kuyi posting, za kuga ya fita da siffar bold style.
Shima italic style haka ake yin shi, kawai dai shi za kuyi search na Italic text generator ne tun daga farko.
Allah ya taimaka.
© Abu Ibrahim