FacebookTech

YADDA ZA KUYI PIN NA POST DINKU A FACEBOOK

Wani adadin kaso mai yawa daga cikin mutanen da suke amfani da facebook suna da wannan tambayar ta: Ya ake yin pin na post?

A dayan bangaren kuma akwai wasu da basu ma san menene pin na post dinba, haka kuma basu san amfanin shi ba, amma a wasu lokutan idan suka shiga profile na wasu, suna ganin anyi pin na post amma duk da hakan basa kawo ma ransu cewa shine pin din.

Idan aka ce pin na post a facebook, ana nufin rataye ko maƙale wani post domin ya zamo farko a koda yaushe a cikin sauran post da mutum yayi, ma’ana duk lokacin da wani ya kawo ziyara a cikin profile na mutun dole wannan post din zai fara gani.

Yin hakan yana da matuƙar amfani musamman ga mutanen da suka dauƙi facebook da muhimmancin da har zasu iya adana wani post da suke san duk wanda ya shiga profile dinsu ya gani, domin sanin wani abu akansu ko akan sana’arsu ko sanarwa. Kuma hakan yana taimakawa musamman ga masu yin kasuwanci domin ajiye bayanan da wani zai duba dan ya amince dasu kafin ya nemi yin kasuwanci dasu.

Yadda ake yin pin na post abune mai sauki kamar haka:

1- Zaka shiga cikin browser dinka misali chrome browser, sai kayi search na facebook.com domin yin login zuwa account dinka, idan kazo wajen login din kafin kayi sai ka danna wani arrow daga can hannu dama a browser din, hakan zai sa wasu bayanai su fito a jere a gefen damar, sa kaje kan inda aka rubuta Desktop Site, ka danna wajen.

See also  YADDA ZAKU IYA DAWOWA DA DUK WANI MESSAGE NA WAYARKU DAYA GOGE

2- Daga nan sai ka saka details naka kayi login na facebook account dinka a cikin browser din.

3- Bayan account din ya bude sai ka danna wajen da aka saka profile inda hoton profile dinka yake daga hannun dama.

4- Anan ne zaka ga duk wani posts naka sun bayyana, sai ka duba post dinda kake son kayi pin nashi din, daga gefen hannun dama na ko wane post za kaga 3dots, sai ka danna wajen.

5- Kana danna 3dots da suke a gefen dama na post din, za kaga za6uka sun fito sai ka danna na farko wanda aka rubuta pin post.

Allah ya taimaka.

© Abu Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button