Tambayoyi a Musulunci

JANABAR GWAURAYE A LOKACIN SANYITambaya
السلام عليكم ورحمه الله
Fatan alkhairi.
Dama karin bayani ne nake so game da janaba, idan ta samu mutum a lokacin sanyi?
Jazakallahu khairan.

Amsa
Wa alaikum assalam
In har ya zama in ya yi wanka zai cutu, yana iya yin taimama saboda hadisin Amru Dan Ass lokacin da ya yi janaba ana tsananin SANYI, sai ya ki yin wanka, saboda tsoran lalura, ya taba kasa, ya shafawa fuskarsa da hannayansa zuwa ku’u, ya je ya yi sallah.
Da aka gayawa Annabi SAW sai ya yi murmushi, hadisin sai yake nuna halaccin taimama ga Gwauron da bai samu ruwan zafi ba lokacin SANYI.

Allah ne mafi Sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

18/1/2023

See also  SHARUDAN YIWA MARA LAFIYA OPERATION A ASIBITI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button