Tarihi

LABARIN SARKI DA BABBAN AMININSA MAI TAKEN “YAYI KYAU”



Abu-asid-az-zinayya, sarki ne dake mulkin daular Zinayya a can kudu maso gabashin sahara, wato bangaren tekun Nilu daga bangaren dama.

Abu-asid ya kasance sarki mai adalci ga al’ummar da yake mulka, ga tausayin talakawa da karrama baki, wannan dalili yasa koyaushe baki sai tururuwar zuwa wannan kasa suke yi, wasu na zuwa domin fatauci, wasu kuma na zuwa don yawon bude ido da shakatawa.

Sarki Abu-asid mutum ne mai sha’awar fita farauta tun yana karami, hakan tasa bayan ya hau kujerar sarauta mai bai daina fita wannan farauta ba. Yakan shirya fita yawon farauta lokaci – lokaci don debe kewa da nishadi, koyaushe idan zai tafi farauta suna tafiya ne da abokinsa mai suna Usudul-azman, wanda suka taso tare tun lokacin kuruciya. Saboda saukin kan sarki Abu-asid daya zama sarki ma bashi da abokin zuwa farauta da shawara kamar shi. Usudul-azman yana da wata dabi’a da ta zame masa jiki, wanda shi duk abinda ya faru a gare shi mai kyau ko akasin haka sai yace “YAYI KYAU”

Wata rana sarki da abokinsa sun fita farauta, sai suka ci karo da barewa, a kokarin harbin wannan barewa, sarki bai seta bundigar daidai ba, hakan ta jawo ya harbi hannunsa na hagu, nan take babban dan yatsan sarki ya fadi kasa cikin jini. Duk da irin wannan hali da sarki ya tsinci kansa, budar bakin Usudul-azman abokin sarki, sai yace “YAYI KYAU” Nan take sarki cikin fushi da kunan rai, yana gurnani kamar tsohon zakin da ya shekara baici nama ba yace karya ne baiyi kyau ba.

Saboda wannan magana da Usudul-azman ya fadawa sarki, bayan sun dawo daga farautar, sarki yayi umarnin a kaishi gidan kurkuku a daure shi, kowa yayi mamakin wannan hukunci na sarki, domin kuwa ba’a taba gani ya yiwa wani bawansa irin wannan hukunci ba tare da yin wani laifi ba, bare kuma Usudul-azman babban amininshi. Haka dai kowa ya gama fadin albarkacin bakinshi yayi shiru, domin ba mai iya zuwa yace sarki bakayi daidai ba.

Bayan kusan shekara daya da faruwar wannan al’amari, sarki yana cikin wani kungurmin daji mai nisan gaske yin farauta, wanda duk jarumtaka irin tashi amma hankalinshi bai kwanta da wannan daji ba. Kwatsam! Sai jin ihun arnan daji yayi ta gaba da bayansa, kafin yayi wani kokarin kubuta daga wurinsu tuni sun kamashi, suka daddaure shi hannu da kasa, suka nausa cikin daji dashi, sun ihun samun nasara. Da isarsu gida aka fara shirye – shiryen watanda, daman kuwa sun dade basu ci naman mutum ba sai dabbobi. A lokacin da sarkin wannan arnan daji yazo yanka sarki sai ya gane ashe babban dan yatsansa na hannun hagu ya gutsere. Nan take cikin bakin ciki yayi kururuwa yace ba cikakke bane, wato wani bangare daga jikinsa bai cika ba. Kuma daman a al’adarsu idan suka kama mutane da nakasa a jikinshi basa ci, nan take sarkin nasu ya bada umarni a sake shi ya kama gabansa.

Tun akan hanya sarki Abu-asid ya tabbatar lalle maganar da amininsa, Usudul-azman ya fada lokacin daya harbi hannunsa abune mai kyau, domin kuwa da badon hakan ba da tuni anyi wadanta da namansa yau. Saboda haka yana isa gida yayi umarnin a saki abokin nashi, kuma ace yana son yin magana dashi. Bayan Usudu ya fita sai yazo wurin sarkin don jin mai ya faru. Sarki ya fada masa duk abinda ya faru gare shi, kuma ya roki afuwar abokin nasa saboda sawa da yayi a daure shi.

Budar bakin Usudul-azman sai yace “YAYI KYAU” Nan sarki ya tambaye da mai yake nufi da hakan? Kai da kasha wahala a kurkuku amma kace yayi kyau? Sai Usudu yace “eh mana da badon ina cikin kurkuku ba da tuni ni anyi watandar nama na, saboda da tare da ni za’a kama mu, kuma ni cikakke ne. Nan sarki shima da kansa yace lallai “YAYI KYAU”

See also  Farkon Karatun Ƙur’ani a rediyo

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button