Nasir I. MahutaTech

ZABABBUN WEBSITE 10 DOMIN DALIBAN ILIMI



Kimiya da fasahar zamani sun sama mana sauki a kowanne bangare na rayuwa, musamman bangaren ilimi inda yanzu koyan karatu yake da sauki ba kamar da cen ba. Baka bukatar sayen littafi ko zuwa extra lesson ko karin bayani a wajen wani, abinda kawai kake bukata shine shiga website din Ilimi nan take sai ka samu dukkanin amsoshin tambayarka da kuma karin bayanin da kake bukata.

A cikin tarin websites da nasani wanda suke taimakawa dalibai na zabo guda goma.

1. http://Www.Instructables.com

Website ne da masana na sassan duniya suke yada bidiyon koyon abinda ya shafi, kimiyya, sana’ar hannu, karatu, girki da dai sauran su.
A wannan website din akwai bidiyoyi marasa adadi da za su koya maka duk abinda kake son koya, sannan akwai littattafai da takardun ilimi.

2. http://Www.mentalfloss.com
wuri ne da zaka iya koyon abubuwa masu ban sha’awa daga ko’ina cikin duniya, akwai darusa masu kayatarwa da suka shafi abinci, al’ada, da kimiyya sannan Kana iya binciken abubuwa daban-daban na Trivia, Quizzes, Brain Teasers, da sauransu.

3. http://Www.careerGuide.com
Wani dandali ne wanda zai taimaka maka wajen fahimtar CAREER Naka. Misali idan kana son zama Engineer to a wannan website din zaka samu dukkanin ilimi da matakan da ya kamata kabi wajen zama Engineer, ba iya Engineer ka dai ba duk abinda kake burin zama a rayuwarka .

4. http://academicearth.org
Website din na dauke da dukkanin darussan tun daga kan secondary har zuwa University , ma’ana duk wani course ko topics da ake koyawa a makaranta to zaka sami bidiyon LECTURE din da handout din a kyauta. Sannan tanan zaka iya yin DEGREE naka ba tare da kaje makaranta ba, sannan suna da hadin gwiwa da manyan Universities na duniya kamar Oxford University, Columbia University da sauran su.

5. http://www.archive.org
A nan ne zaka sami dukkanin littafin da kake bukata ko handout ko projects.
Suna dauke da kusan dukkanin abinda kake nema na ilimi.
-Shafin Internet fiye da billion 330.
-Littattafai da Rubutuna fiye da million 20.
– AUDIO File na ilimi fiye da 4.5 million.
-Bidiyoyi fiye da million 4.
-Hotunan fiye million 3.
Softwares da programs fiye da 200,000.
Idan kana bukatar gurin da zaka samu ilimi kyauta to INTERNET ARCHIVE nan ne zaka.

6. http://Www.SkillShare.com
Websites ne da ke kunshe da bidiyoyi na courses daban daban, suna da Dalibai fiye da million 4 da suke koyan karatu ta ciki sannan akwai AJI na karatu fiye da 22,000 na kudi da na kyauta, sai ajin da kaga dama ka shiga domin kwankwadar Ilimi.

7. https://www.brightstorm.com
Website ce ga DALIBAN da suke bukatar fahimtar ilimi English, Mathematics da Science. Suna da:
-Dalibai fiye da 800,000 a kasashe 120.
– Makarantu 800 ne ke amfani da website din wajen koyar da Dalibansu.
Suna samar da ingantattun bidiyon darusa sannan suna da kwararrun malamai da suke koyarwa.

8. http://www.explania.com
Website ce ta musamman da aka tanade ta domin samun cikekken bayani akan abinda ya shafi yadda ake sarrafa wani abu, Ilimi ko kuma yadda ake amfani da wata software.

9. http://Www.Coursera.Org
Website ce dake koyar da online course na sassan Ilimi daban-daban. Komai kake karanta a makaranta a cikin Website din nan zaka iya karantar abin kyauta, zaka iya yin karatun ka batare da kaje makaranta ba.

10. http://Www.KhanAcademy.Org
Wannan makarantar Yanar gizo ce dake koyar da darussa da courses kala-kala irin wadanda ake koyawa a University. Idan kana ziyartar wannan website din tabbass baka bukatar zuwa makaranta ma, domin duk abinda ake koyawa a makaranta akwai a Khan Academy.

See also  Yadda Zaka Gano Wayar ka Ta Amfani Da IP-Address Dinta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button