Jamb

Abubuwan Da Yakamata Kasani Game Da DE

Cikakken bayani Akan Direct Entry (D.E)


•Menene Direct Entry (D.E)

Direct Entry ko D.E a takaice wata dama ce ko hanya wacce idan kabita zata kaika kowacce irin jami’a dake fadin Najeriya, Sannan kuma zaka fara karatunka ne daga Aji biyu (Level 200/ UG 2), duk da akwai wasu Departments a wasu jami’o’i wadanda su idan sun baka admission din to dole daga Aji daya zaka fara (Level 1) tare da wadanda suka shiga ta hanyar Jamb.

Hakanan kuma Direct Entry anayin Rijistar ta ne sau daya a shekara itama kamar JAMB, Sannan Kuma Mafi Yawancin Makarantun Basa Shirya Wata Jarrabawa, Akan D.E, Sai de Tantancewa ta internet(online screening) Dakuma Physical screening, Wasu Makarantun Kuma suna Shirya Jarrabawa, ko interview.

Kamar Jami’ar Bayero a Shekarar Data Gabata ta Shirya Jarrabawa Ga Daliban Dasuke Neman Makarantar, ta Hanyar D.E Amma a Faculty Daya Kadai (Allied Science) banda Sauran.

—Su waye Suke da Damar Neman Jami’a ta Hanyar Direct Entry?


•Direct Entry din (D.E) Ba kowanne dalibi yakeda damar zuwa jami’a ta hanyarsa ba, sai Wanda yakeda daya daga cikin wadannan takardun shaidar kammala karatu, kamar haka:-

1• Ordinary National Diploma Certificate (OND)

2• Higher National Diploma Certificate (HND)

3• GCE A Level, HSC, DALF Certificate

4• Nigerian Certificate Of Education (NCE)

5• Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN)

6• National Diploma (ND)

7• First Degree (Bsc, B.A, BAEd, LL.B)

8• National Innovation Diploma (NID)

•Necessary Requirements

Sannan kuma dole sai ka cancanta ta hanyar samun:-

1• Credit Biyar a SSCE dinka, kuma kar ya wuce zama biyu (Two Sittings)

2• Mafi karanci kaci Lower credit a ND, ko NID tareda Requirement na O’level

3• Hakama Wanda yakeda 3rd Class a digiri dinshi na farko shima ana bashi
See also  Tambayoyi (20) da suke yawan fitowa Physics a jarabawar JAMB tare da amsa

FADAKARWA:-


Anan zaka iyayin applying Direct Entry da certificate din Digirinka na farko, Misali; kayi digirinka na farko a Law LL.B to kuma kanaso kayi wani digirin a fannin ilimin kimiyar siyasa (Political Science) to ba sai kayi Jamb ba, kawai sai kayi amfani da wannan certificate din digirin naka na law LL.B saika siya D.E form kacika shikenan zasu baka level 2.

•Post Graduate Diploma;


Sannan akwai banbanci tsakanin wannan da postgraduate diploma, ita postgraduate diploma kamar misali kagama digirinka na farko a Political Science to amma kuma kanaso kayi master’s degree dinka ne a Public Administration, to madadin ace bazakayi masters dinba saikaje tukuna kayo degree, a public administration din to shine sai aka sama maka sauki cewa kaje kayo wannan postgraduate, diploma din sannan bayan ka gama saikazo kayi masters degree dinka a public administration saboda idan kun lura zakuga sunada alaka da juna sannan kuma suna faculty daya ne.

•Post Graduate Diploma a Law Da Medicine;

Amman Ba’ayin postgraduate diploma a law da medicine, sai idan degree din naka na farko kayishi ne a wani course dayake karkashin faculty of law din, kamar misali kayi Degree dinne a private law, to zaka iyayin postgraduate diploma din domin kayi Master’s dinka awani law din na daban.Ina Fatan Masu Tambayoyi Akan Direct Entry (DE) yanzu Sun Samu cikakkiyar Amsar Su?

Mungode Musha Ruwa Lafiya Daga National Coordinator Shehu R. Na’Allah.

Domin aikowa da tambaya ko Neman Karin bayani Ku nememu a:

Arewastf@gmail.com

Call/Kira:- 08088119753WhatsApp:- 08038485677


Daga Ni Naku A Kullum : Miftahu Ahmad Panda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button