Tambayoyi a Musulunci

ALAMOMIN BALAGAR NAMIJI



Tambaya:
Assalamu alaikum,
Allah ya Ya saka ma Dr da alkhairi, ina da yaro ne mai kimanin shekara goma sha uku (13) yana da girman jiki don ya fi ni tsawo na dauka girman a tsayi ne kawai sai larurar basir ta same shi na zo in yi masa tsomen magani sai mamaki ya kamani yaron halittarsa kamar na magidanci na yi wa mahaifinsa bayani ya ce in tambaye shi yana mafarki na tambaye shi ya ce ba ya yi. Tambayata a nan shi ne hukunchin baligi ya hau kansa ko kuwa?.

Amsa
Wa alaikumus salaam, alamomin balagar namiji guda uku ne:

1. Yin mafarki, kamar yadda aya ta: 59 a suratu Annur ta tabbatar da hakan.

2. Tsirowar gashin mara, kamar yadda kissar Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Banu-Kutaitha ta nuna hakan na daga cikin alamomin girma.

3. Cika shekaru (15), kamar yadda Malamai suka fahimci haka a hadisin Ibnu-Umar lokacin da za’a fita yakin Uhudu.

Duk alamar da ta fara zuwa ma Da namiji daga çıkın alamomi ukun da suka gabata, to ya zama baligi kuma shari’a ta hau kansa, ba shi daga çıkın alamomin balaga girman mazakuta, zai yı kyau ki sake tuntubar yaronki don tabbatar da daya daga cikin abin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa.
30/04/2016.

See also  MAGANIN QARFIN MAZA

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button