NYSC

NYSC : Cikakken Bayani Gameda Monthly Clearance Status

National Youth Service Corps (NYSC)• Me ake nufi da Monthly Clearance Status, kuma menene amfanin sa•Me yasa nake ganin Absent a Dashboard dina, bayan kuma nayi Clearance• Absent daya yana da illa ko kuwa ?

___________________________________________________

>Monthly Clearance wani feature ne da hukumar NYSC ta kara shi a Portal din ta, wannan feature din zai bawa Corps Member damar ya duba Monthly Clearance Status din sa.


Corps Member zai rika yin wannan Clearance din ne a duk wata, sannan duk lokacin da kayi clearance din to zai nuna maka PRESENT a dashboard din ka, idan kuma bakayi ba to zai nuna maka ABSENT a watan da baka yiba din.>Dan ka sami ABSENT daya ba zai hana a baka Monthly allowance dinka ba, idan yakai biyu ko fiye da haka zai sa a rike Certificate din naka ta hanyar kara maka daga Sati daya zuwa wata Uku kuma ba za’a baka Monthly allowance ba a wannan watannin da aka yimaka kari.

Yanayin yawan Absent dinda ka samu yanayin hukunci (Punishment) dinda za’a yimaka.Dan haka a matsayin ka na Corps Member yana da kyau ka rika duba matsayin ka (Status) a kowane lokaci.

Idan kaga Absent a dashboard dinka hakan yana nuna kenan bakayi Clearance na wannan wata din ba.Amma kar ka damu dan kaga Absent a watan da ka bar Orientation Camp, wannan ba wani matsala bane, saidai idan kaga Absent din a sauran wasu watanni banda watan da kabar Orientation Camp din to wannan kam kayi gaugawar sanarwa (Reporting).


Sannan idan kaga an saka maka Absent kuma alhali kasan kayi Clearance din to abinda yafi kamata shine kaje ka sanar (Reporting) zuwa ga Local Government Inspector (LGI’s) dinka kafin lokacin ka ya kure.Dan haka yanada kyau Corps Member ya saka ido sosai akan Matsayin Clearance dinsa (Clearance Status).Monthly Clearance yana da matukar amfani domin kuwa yana cikin abubuwan da ake bukata (Prerequisite) don ka sami alawus dinka na kowane wata daga gwamnatin tarayya (FG).Bissalam

ASOF_2021

12/02/2021

Arewastf@gmail.com

See also  NYSC : Cikakken Bayani Gameda Banbancin Remobilization da kuma Revalidation

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button