Tambayoyi a Musulunci

YADDA AKE WARWARE SIHIRI




Tambaya
Assalamu alaikum Dan Allah malam a fitar dani cikin duhu game da abin da yake damuna Mahaifiya ta ce ta je gurin malami ai mata naganin ciwon mara dz yake damunta, tace tana da ciki yakai shekara, amma likitoci sun yi scanning sunce ba komai to sai malamin ya ce mata asiri aka yi mata, kuma zai yi mata magani nan take ta haife abinda yake cikinta amma za ta kawo tunkiya da dubu bakwai, sai take min magana in kawo kudi a sayi tunkiyar kuma akai masa dubu bakwan, to gaskiya malam zuciyata ba ta aminta da malaman ba ne shi yasa ! Na keso ka bani fatawa shin irin wannan hanyar ta magani ta halatta a addini? Idan bata halatta ba wacce hanya zan bi wajen qin biyan kudin da kuma sanar da ita, saboda ina da matsala , ta bangaren aqeeda mun banbanta? Wassalam na gode malam Allah ya qara basira.

Amsa
Wa’alaikumus salam, To ‘yar’uwa tabbas ba a warware sihiri ta hanyar sihiri, saidai ana iya warware sihiri ta hanyar ayoyin Alqur’ani, wasu malaman sun yi bayani cewa: ana iya warware sihiri ta hanyar karanta Ayatul-kursiyyu da Kuliya da Iklas da Falaki da Nasi, da kuma aya ta: 117 zuwa ta 122, na suratul A’araf, sai kuma aya ta: 79-81 a suratu Yunus, sannan sai a hada da aya ta: 65-70 a suratu Dhaha, za’a karanta su, sai a tofa a ruwan da aka zuba magarya guda bakwai.

Amma bai halatta ki taimaka mata ba, wajan bada wadannan kayan da boka ya nema, saboda ba’a yiwa iyaye biyayya a wajen sabon Allah.

Ya wajaba ki yi mata nasiha cikin hikima, ki sanar da ita cewa: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:” “Duk wanda ya je wajan boka, ya tambaye shi wani abu, Allah ba zai amshi sallarsa ba, ta kawana arba’in” kamar yadda muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2230.

Kin ga in mutum ya mutu a wadannan kwanaki akwai matsala, musamman ma tun da akwai hanyar da shari’a ta yarda da ita, a wani hadisin kuma yana cewa: “Duk wanda ya je wajan boka ya gaskata abin da ya fada, to tabbas ya kafurce da abin da annabi Muhammad ya zo da shi” kamar yadda ya zo a Sunanu-abi-dawud hadisi mai lamba ta: 3904, kuma Albani ya inganta shi.

INA GANIN DA IRIN WADANNAN HADISAN ZA KI IYA GANAR DA ITA, TA DAWO KAN HANYA.

Allah ne mafi sani.

12\4\2014

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

See also  SHIN WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button