Nasir I. Mahuta

KA GWADA WANNAN SANNAN KA BANI LABARI

HAUSA

KA GWADA WANNAN SANNAN KA BANI LABARI.


Mafi yawancin mutane suna shiga mayuwacin hali ne sakamakon fifita abin da zuciyarsu ke so fiye da abin da tunaninsu ya nuna masu.

Idan kana son abu to so din na fita ne daga zuciyarka, amma tunanin dacewar ka so abin ko rashin dacewar wannan aikin kwakwalwa ne. Zuciya a gangar jiki kamar Driver ne mai tuka mota wanda duk inda motar nan za ta shi driver din ne ke tuka ta. Kwakwalwa a jikin mutum tamkar mirror, dashboard da glass din da ke jikin motoci ne. Duk yadda diver ya kai ga kwarewarsa bai iya tukar motar da ba a yi mata inda driver zai ke kallon hanya ba. Idan kuma drivern ya takura sai ya tuka to a karshe hadari zai yi. Kamar haka, duk yadda ka ke son abu matukar dai ba za ka yi amfani da kwakwalwa wajen gane ko abin ya chanchanta da kai ko bai chanchanta ba to tabbas za ka jefa kanka a halaka.

Ya kai dan uwa, ka sani zuciya makauniya ce ba ta da ido ba ta da kunne. Idanu da kunnuwan da ke jikinka dukkansu kofofi ne na kwakwalwa. A duk lokacin da ka ke son abu ka tuna cewa kila son abin kawai ka ke ba lallai idan ya dace da kai ba. Yi amfani da Kwakwalwarka sannan ka tambayi kanka wadannan tambayoyin:

Shi me ya sa ma ka ke son abun?
Ma ye amfanin abin a tattare da kai.
Shin mai ya sa dole rayuwarka na bukatar abin?
Mai tarayyarka da abin zai iya haifar maka?

Ba iya abin da ka ke so ba, ko wani abu za ka aikata, ka tuna da cewa zuciyarka ce ke tunzuraka ka aikata abin. Ita kuma zuciya iya so da tunzurawa ta iya ba ta iya gane daidai da rashin daidai ba. Yi amfani da kwakwalwarka wajen gane ya dace ka yi ko kuma bai dace ba.

Na sani, ba kowanne mutum ne ke iya aje soyayya ko kiyayya a gefe guda yayin da zai yi hukunci ba. Mafi yawan mutane suna bin umurnin zuciyarsu ne sai daga baya su dinga regret. Abokina, idan kana bukatar samun nasara tare da kawar da yin danasani a rayuwa, to dole ka koyi ba wa zuciyarka umurni ba wai ka zama mai yi wa zuciyarka biyayya ba.

Shin ka taba jin kana bala’in son wani abu kuma kana son ka daina son abun amma ka gagara ka daina?

Domin na fi karfin zuciyata ta yadda zan iya ba ta umurni akwai hikimar da na ke amfani da ita kuma na jima ina gwadawa ina samun sakamako mai kyau: Idan na ji ina son abu sosai to zan shawarci kwakwalwata ta hanyar yi wa kaina tambayoyin da na lissafa a baya. Idan kwakwalwata ta nuna mini abin da na ke so din nan bai chanchanta ba to nan ta ke za ka ji ina magana da kaina.

Tabbas na kan yi magana da kaina ta hanyar dora hannuna a zuciyata yayin da na ke kallon mirror, sannan na fada wa zuciya cewa”ke zuciya! Kina ta rudani akan son abin da bai chanchanta ba, to na gane kuma ba ki isa na biye maki ba”. Matukar na yi haka kuwa, to maganar son da na ke yi wa abin zai ragu kuma na daina.

Idan akwai abin ka ke so ko ka ke ai katawa mara kyau, don Allah ka gwada tsayawa gaban mirror ka dora hannunka a kirjinka sai tin zuciyarka sannan ka yi mata kashedi akan ta daina sanya ka son abin ko kuma ta daina tursasa maka aikata abin mara kyau.

Ka gwada wannan sannan ka ba ni labari.

See also  BAYANIN AKAN YADDA RAI YA KE .

ENGLISH

GIVE IT A TRY AND SHARE YOUR EXPERIENCE


Many people find themselves in trouble because they tend to follow their heart rather than their mind. When you want something, it’s your heart that desires it, but it’s your brain that evaluates whether it’s good for you or not. The heart can be seen as the driver of a car, while the brain is like the car’s dashboard and mirrors. No matter how skilled the driver is, they cannot drive a car that isn’t designed for them to see where they’re going. If the driver is too distracted to pay attention, they’ll eventually crash. Similarly, if you don’t use your brain to understand whether something is good for you, then you’ll likely bring about your own destruction, no matter how much you love it.

Dear friend, the heart is blind and has no eyes or ears. The eyes and ears in our body are the doors to our brain. When you want something, remember that it may not necessarily be good for you. Ask yourself questions like “why do you love it?” or “what’s the use of it in your life?” Use your brain to evaluate if you really need it or if it will bring about negative consequences.

Before you pursue something, remember that it’s your heart that drives you. The heart is motivated by desires and may not always differentiate between what’s right and wrong. Use your brain to evaluate what’s good or bad for you.

I understand that not everyone can separate their emotions from their judgment. Most people tend to follow their heart and later regret it. If you want to be successful and avoid laziness in life, you need to learn how to give orders to your heart instead of following it blindly.

To control my heart, I use a wisdom that has helped me. If I really like something, I ask myself the questions mentioned earlier. If my brain tells me that it’s not good for me, I talk to myself in front of the mirror with my hand on my heart, telling it to stop pressuring me and stop loving something that’s not good for me. Doing this helps me to let go of things I don’t need.

If there’s something you like or something you’re doing that’s harmful, try standing in front of the mirror and putting your hand on your heart. Tell your heart to stop pressuring you to do something bad or to stop loving something that’s not good for you. Give it a try and let me know what you think.

See also  IYA TURANCI BA YA NUNA KAIFIN BASIRA.

Nasir I. Mahuta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button