Kimiyya da fasaha

Muhimman Bayanai akan Artificial Intelligence


Kamar yadda na fada jiya cewa Insha Allahu zan rubuto wasu muhimman bayanai akan AI, to sai yanzu Allah cikin ikonsa ya nufa.

Na Farko
Wato AI a matsayinsa na fasaha mai zaman kansa yanada ire-ire da kuma nau’uka. Ire-irensa sun hada da:
i. Weak AI – wannan yana nufin fasaha ta AI mai rauni wato wacce batada karfin daidaita fikira da basira kusan irin na dan Adam. Misalin weak AI shine kamar irin wasu applications da zamu iya hadawa, zai iya cika sharuddan zama AI amma bazai iya cika sharuddan yin abu kamar dan Adam ba, to wannan shine fasahar AI mai rauni

ii. Strong Ai – wannan kuma ba kamar na saman bane, wato wannan yana nufin mai karfi. Yana kokarinsa wajen ganin ya kwaikwayi abubuwa irin na dan Adam misali sakaguwa (robot) Sophia. Wannan wata robot ce da kamfanin Hanson Robotics ya kirkira karkashin jagorancin Dr. David Hanson a Hong Kong a shekarar 2016, kuma anyi taruka da dama da ita ciki har da GITEX technology week da akayi a Dubai a shekarar 2017 da kuma wani event da akayi a Saudi Arabia wanda anan ne ta samu katin shaidar zaman yar kasar Saudi Arabia.

Anan zamu iya fahimtar cewa fasahar AI tana iya zama mai rauni ko mai karfi, amma fa duk da abubuwanda Sophia zata iya yi kamar na dan Adam kamar yanke shawara, tunani, nazari, mu’amala da jama’a, taimako da sauransu wasu masana suna cewa har yanzu fasahar AI dinta mai rauni ne (weak AI). Ga kuma su Harmony ta US wacce takan iya jin feelings ma, da yar uwarta.

Na Biyu
Nau’ukan AI. Bayan da mukaga ire-irensa yanzu kuma akwai wasu abubuwa da ake ce musu nau’ukansa kamar su:
i. Artificial Intelligence (AI) – shi din da kansa anan shine wanda muke magana wato fasahar da akeso tayi kwaikwayon dabi’un dan Adam kamar yadda mukayi bayani.

ii. Artificial General Intelligence (AGI) – wannan ma duk yana daga cikin nau’ukan AI wato shi kuma so akeyi a fadada bincike akan AI ta yadda zai zama cewa duk wani abunda mutum zai iya yi to wannan fasahar ma tayi, wato daidai da dan Adam ba kamar AI ba – cewa anaso yayi KAMAR dan Adam, shi wannnan AGI din zaiyi DAIDAI da dan Adam ne. Wato fasahar ta zamanto cewa zata iya cin nasara ta wajen samun fikira, basira, tunani, nazari, mu’amala, da sauran dabi’un dan Adam.

iii. Artificial Super Intelligence (ASI) – wannan kuma itace babbar. Wato wannan so akeyi tafi dan Adam komai. Tafi dan Adam ilimi, basira, nazari, tunani, hikima da duk wata fikira da Allah ya bawa mutum. So akeyi ta kere dan Adam a komai.

Sai dai har yanzu muna Artificial Intelligence (AI) ne dan bamu zo ko AGI ba balle ASI. (nayi bayanin wannan kwanaki a cikin rubuta na “Menene Asalin Mission na Boca…”). A yanzu haka manyan masana akan fasahar AI kamar su Peter Norvig, Stuart Russell (marubutan littafin AI: The Modern Approach) Andrew Ng, Nick Bostrom da sauransu suna kara ingiza masu bincike kan wannan fasaha wadanda suke a bangarori da dama kamar su computer science, mathematics, brain science da cognitive psychology domin fadada bincike don ganin an cimma matsaya kan developing din AI.

Shugaban Russia yace duk kasar da tayi nasarar jagorantar duniya wajen gina AI to babu shakka ita zata mulki duniya. Haka kafin Prof. Hawking ya mutu ya sha nuna hatsarin wannan fasaha matukar akaci gaba da bincike akanta. Yace fasaha ce da matukar duniya ta cigaba zata iya fin mutum fikira da komai, to a lokacin ne kuma zatayi kokarin samar da tata rayuwar ta karan kanta ta daina yiwa dan Adam bauta. A lokacin ne zata rikita duniya kamar yadda Elon Musk yace fasaha ce da take da hatsarin gaske matukar an juya ta ta zama makami. Za’a iya amfani da fasahar AI wajen yakar al’umma tunda za’a iya sanya mata karfin da zai ninka na dan Adam fiye da mizani ta kowane fanni.

Sai dai kuma fasahar AI zata iya taimakonmu a kowane fanni na rayuwarmu ta yau da kullum kama daga gwamnatoci, kasuwanci, banki, tsaro, kiwon lafiya, karatu da makarantu da sauransu. A yanzu haka akwai wani AI robot na kamfanin IBM mai suna Watson wanda yake taimakawa likitoci idan ana operation. Yana taimaka musu ne da shawarwari da abunda ya kamata suyi a kowane step da sukeyi na operation din tunda dan Adam ajizi ne zai iya manta wani abu ko makamancinsa. Amma shi wannan Watson din yanada basirar sanin abubuwa da dama da kuma sanin yadda zai taimaka wajen yin wani abu.

Zaka iya samun bayani sosai akan wannan fasaha a yanar gizo ta hanyar karanta littatafai, rubuce-rubuce, kallon videos da sauransu.

Allah ya taimaka, ameen

✍ Mohiddeen Ahmad
17th May, 2020.

See also  Me Ya Sa Elon Yake Tsoron Google?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button