Kimiyya da fasaha

Me Ya Sa Elon Yake Tsoron Google?Google kamfani ne da ya jima yana fafatawa a duniyar fasaha. Amma duk da duniya ta shaida cewa kowa yanada lokacin da yake tashe, Elon ya tsorata da lamuran Google duba da yadda suke gudanar da wani lamarinsu.

A shekarun 1990s Yahoo ne mafi girman kamfanin da yake mulkar duniyar fasaha, saboda sun kama kusan kowanne lungu da sako na shige-da-fice. Duk da ba a lokaci ɗaya suka zube ba, amma zubewar tasu ta zo kusan ɗaya ne da tashin da Google ya yi, kamar dai yadda duniya ta yi farat ta firgita a lokacin da ake ƙira “renaissance” na duk wani fannin cigaba musamman ma “economic revolution” da “industrial revolution” wanda ya haifar da duniyar fasahar da muke ciki a yanzu. To irin wannan farkawar kamfanin Google ya yi a lokacin da kamfanin Yahoo ya ki tsayar da cinikin sayan Google ɗin.

Fafatawa a duniyar kasuwanci kusan irin na siyasa ne, amma mu a nan ba a ɓata suna, cin zarafi, sharri, tunzura matasa wajen aikata ɓarna ko kashe-kashe, a’a a kasuwanci kawai fifiko ake nema ta hanyar wasu dabaru. Ka ɗauki misalin yadda Microsoft ya fafata da Netscape, da kuma yadda ya ƙara fafatawa da Apple, sai kuma yadda Google ya fafata da Yahoo. Amma kada mu manta, duk girman kamfanin Google ya kasa fafatawa da Facebook ta wani wuri. In Allah Ya yarda zan kawo wani bayani mai muhimmanci game da wannan ƙaulin wanda zai taimaka wa masu gina “new ideas.”

Yanzu idan za mu duba yadda Elon yake tashe a duniyar fasaha, duk da muna koyon manyan darussa daga gare shi kuma muke ganin yana ɗaya daga cikin manyan masu fiƙirar juya wannan zamanin na fasaha, amma yace kamfanin da ya ke shakku shi ne Google. Saboda me?

A zahirin gaskiya idan muka ajiye maganar ƙarfin ikon da Google yake da shi babu wani abu a zahiri da ya bayyana wanda za mu danganta ga wannan ƙaulin. Amma wanda ya bayyana a zahiri kuma shi ne ɗaya daga cikin ayyukan Google mai suna DeepMind. Wannan DeepMind ɗin ɗaya daga cikin “products” ɗin Google ko in ce Alphabet ne wanda yake da matuƙar ƙarfi a fasahohin zamani irin su “Artificial Intelligence.”

An gina DeepMind ne bisa fasahar AI mai matuƙar tasiri wacce take taimaka wa Google wajen ɗaura duniya a tafin hannunsu, ta yadda duk wani shige-da-fice da mutum zai yi da duk wani bayanansa za su sani. Na’urar za ta san me kake so, me ka yi a baya, me za ka yi nan gaba, me za ka iya aikatawa ko sabanin haka, da sauransu. Za ta san duk waɗannan ta hanyar koyon yadda kake mu’amala da shige-da-fice a yanar gizo da amfani da na’urori da fasahohin zamani.

Tirƙashi! To daman Elon yana ɗaya daga cikin waɗanda suke matuƙar jin tsoro da jan kunne kan fasahar AI, haka nan Prof. Hawking har ya mutu yana jiye wa duniya tsoro game da abun da wannan fasahar za ta iya yi a duniya, tare da hasashen cewa tana dab da yi wa Ɗan-Adam fintinkau ta ɓangaren fiƙira da basira da dogon nazari da hasashe da hangen nesa.

Da Elon ya yi tsam ya fahimci tasirin da DeepMind yake da shi a kamfanin Google, da kuma yadda shi Google ɗin yake da matuƙar ƙarfi a duniya gabaɗaya, sai yace tabbas wannan abun tsoro ne kuma zai iya zama wani ginshiƙi ko ingarman dokin da ba zai bugu ba.

Saboda me? A yanzu, aƙalla;
—Google yana da bayanan mutane sama da biliyan uku a duniya
—Ya san duk wani shige-da-ficen mutane sama da biliyan ɗaya
—Sun san inda kake zuwa, da wurin da kake rayuwa, da abun da ka fi so, da abun da za ka iya nema nan gaba (a yanar gizo)

Tasirin DeepMind a kamfanin zai wuce yadda kake ɗauka a yanzu, don inji ba ya gajiya da koyo da kuma nazari.

Don haka don wannan dalilin Elon yake tsoron Google!

Idan ba ku manta ba kwanaki na yi rubutu mai taken “Abun Lura…” wanda a ciki na ɗan yi gajeren tuni game da manyan kamfanoni da tasirinsu a duniya a dunƙule.

Mohiddeen Ahmad
31st January, 2022

See also  Muhimman Bayanai akan Artificial Intelligence

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button