Kimiyya da fasahaTarihi

Tarihin shafin intanet na kamfanin Google

Kalmar Google ta samo asali ne daga ‘googol’, wacce ita ce ta farko da ta biyo bayan sifili 100. Wadanda suka kirkiri shafin sun zabe ta ne don ta dinga nuna bayanai masu dumbin yawa da suke nema ta hanyarta.

Google LLC kamfani ne na fasahar kere-kere na kasar Amurka da ke mai da hankali kan tallan akan Online, fasahar injin bincike, (Search) software na kwamfuta, kasuwancin e-commerce, da na’urorin lantarki Ga mabukata Da Sauran Su.

Ana kiran shelkwatar Google da ‘Googleplex’ wanda ke a Silicon Valley da ke California A Kasar Amurka.

A Googleplex din, akwai wani katon gunkin dabbar Dinosaur, wanda yawanci yake kewaye da balbelu. Ana rade-radin cewa hakan na tunatar da ma’aikatan Google din kar su bari a manta da kamfanin ko ya zama tarihin kamfanin ya shafe.

Larry Page da Sergey Brin ne suka bijiro da shafin google a shekararta 1996 lokacin da suke karatunsu na digiri na uku wato Ph.D a jami’ar Stanford da ke California ta kasar Amurka.
Da fari dai Page da Brin sun radawa shafin na Google Maisuna BackRub kafin daga bisani su sauya masa suna zuwa wanda yanzu aka sanshi da shi wato Google. Da dai shafin na Google na karkashin mallakin jam’iar Stanford inda Page da Brin suka yi karatu kafin daga bisani su yi masa rijista a matsayin kamfani mai zaman kansa a cikin watan Satumban shekara ta 1998.

Kamfanin na shafin Google na gudanar da aiyyukansa a cikin wani gareji na abokin guda daga cikin wanda suka kirkireshi sannan kuma daga bisani masu kamfanin suka yanke hukuncin daukar ma’aikata. Ma’aikacin farko da aka dauka a kamfanin kuwa shi ne Craig Silverstein wanda shi ma lokacin dalibi ne na digiri na uku a jami’ar Stanford inda Page da Brin suka yi karatu.

See also  Tarihin Musulman Japan Da Musulunci a kasar Japan

Bayan da kamfanin na Google ya girku, an kuma samu sabon ofishi a Alto da ke jihar ta Carlifornia kuma daga bisani aka sayar da hannun jarinsa ga jama’a batun da ya sanya shi habaka sosai bayan da mutane da dama daga sassa daban-daban na duniya ke shigarsa domin neman bayanai.

A cikin shekara ta 2000 ce kamfanin na Google ya yanke shawarar fara sanya talluka a shafin nasa domin samun kudaden shiga baya ga hannun jarin da ya sayar tun da fari, to sai dai tallukan da shafin ke sanyawa suna kunsar bayanai a rubuce ne kawai saboda hanzarin da masu kamfanin suka bada a wannan lokacin cewar suna so ne ya kasance tsarin shafin ya cigaba da zama yadda yake ba tare da an jirkita masa kamanni ba.

Da tafiya ta tura, shafin na komai da ruwanka na Google ya yanke shawarar samar da Imel wanda ake yiwa lakabi da Gmail wanda ya fara aiki a farko shekara ta 2007 wanda kuma ya samu miliyoyin masu amfani da shi kuma har kawo wannan lokacin jama’a ke cigaba da yin amfani da shi.

Baya ga Gmail, kamfanin na Google kuma ya bada dama ta neman hotuna da litattafai da dama wanda ya kan sanya kadan daga cikin abubuwan da littafi ya kunsa. Kazalika kamfanin ya samar da wata fasaha a jikinsa ta fassara rubutu daga wani harshe zuwa wani duka dai da nufin taimakawa ma’abota shafin samun bayanai cikin sauki.

Dangane da bayanan da shafin ke da su kuwa, bisa binciken da muka yi, ma’aikatan kamfanin kan tattara bayanan ne daga cibiyoyi da dama wanda suke adanawa a cibiyoyin adana bayanai da kamfanin ke da su guda shidda a kasashen Amurka da Belgium da kuma Finland. Kazalika a shekarar 2013 kamfanin ya ce ya ware dalar Amurka miliyan dari biyu domin gina wasu cibiyoyin na adana bayanai a Singapore da Hong Kong da kuma Taiwan.

See also  Muhimman Bayanai akan Artificial Intelligence

Kamfanin Google dai ba wai a fannin bada bayanai kadai ya tsaya ba, ya na yin aiyyukan raya kasa musamman ma dai abubuwan da suka danganci yaki da gurbata muhalli har ma ya kafa kungiyar da ba ta gwamnati ba mai suna Google.org wanda kamfanin ya sanya tsabar kudi dalar Amurka biliyan guda don gudanar da aiyyukansa. Yanzu haka dai kamfanin Google na da ma’aikata da yawansu ya kai dubu kusan Dubu 135 yayin da a kulli yaumin miliyoyin mutane ke ziyartar shafin don neman bayani.

Abin da zai ba ku mamaki shi ne cewa Google ne shafin da aka fi ziyarta a duniya – ko a takwaransa shafin Bing ma Google din ne abin da aka fi dubawa.

Kashi 15% cikin 100 na binciken bayanai da ake yi a kullum a Google ba a taba bincike a kansu ba.

Youtube ya zama cikin daya daga cikin manhajojin Google a 2006, bayan an sayar da shi fiye da dala biliyan daya da dubu 500. A yanzu haka, shafin YouTube na da masu amfani da shafin kusan mutum biliyan biyu a kowane wata, ana kuma shafe fiye da awanni 400 ana sauke bidiyo a kowane minti.

A zamanin yanzu, Google ya zarce injin din nema ko tattara bayanai kawai, a nan gaba ana shirin kara abubuwa kamar su basirar na’urori, da sabon wasanni na intanet har ma da motocin da basu da matuka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button