Tarihi

Tarihin Musulman Japan Da Musulunci a kasar Japan


Musulmai nawa ne a Japan?


Adadin musulmin da ke zaune a kasar Japan, ko da yake kadan ne, ya ninka fiye da ninki biyu a cikin shekaru goma da suka gabata, daga 110,000 a shekarar 2010 zuwa 230,000 a karshen shekarar 2019 (ciki har da wadanda suka tuba daga kasar Japan 50,000), a cewar Tanada Hirofumi na jami’ar Waseda. Kasar na da masallatai sama 200.

A shekarar 1970, masallatai biyu ne kawai aka yi a kasar, amma yanzu fiye da 200

Tarihin Musulunci a kasar Japan takaitacce ne dangane da kasancewar addinin da ya dade a wasu kasashe na kusa da kasar Kafin Ya Shiga Japan, Musulunci daya ne daga cikin tsirarun addinai a kasar Japan, inda suke da mabiya a kasar fiye da addinin Baha’i, amma kasa da Yawan Kiristoci. Musulman kasar Japan suna kusan 230,000 wanda ya hada da sama da 50,000 na Jafanawa da suka musulunta, sauran kuma baki ne (Yawancinsu ‘yan asalin kasashen kudu maso gabashin Asiya ne).

Tokyo, Japan – Tokyo Camii, ko Masallacin Tokyo, abin ban sha’awa ne, da ban mamaki An Ginashi Da Zayyanar Gini irinna Masallatan Turkiyya, masallacin yana nan ne tsakanin rukunin gidaje a unguwar Yoyogi Uehara.

A shekara ta 2000 ne aka kammala aikin gina masallacin amma masallacin yana da dogon tarihi. A cikin 1930s ne lokacin da Japan ta fara ganin yawan musulmai mazauna Kasar Shine Aka ginashi a Matsayin masallaci na farko. An gina masallacin Nagoya ne a shekarar 1931 da kuma masallacin Kobe a shekarar 1935 da ‘yan gudun hijirar Indiya da musulmi suka gina.

Musulman Tatar da suka tsere daga juyin juya halin Rasha sun zama kabila mafi girma a Japan a shekarun 1930 kuma sune suka kafa ainihin Masallacin Tokyo a 1938.

Hans Martin Kramer, farfesa na Nazarin Jafanawa a Jami’ar Heidelberg kuma kwararre a kan addinai a Japan, yayi bayani a kan wannan babban masallacin da yayi fice a Japan, wanda “ba wai kawai gwamnatin Japan ta tallafa masa ba, har Kamfanonin Kasar Sun tallafa masa. kamfanoni, musamman Mitsubishi, kuma bikin budeshi ya samu halartar manyan baki da jami’an diflomasiyya na Japan da na duniyar Musulunci”.

Yayin da masallacin Tokyo Camii bai sami goyon bayan tuntuɓar juna da gwamnatin Japan da kuma manyan ƙungiyoyin jama’a a wannan zamani ba, an sake gina masallacin ta hanyar amfani da kuɗi daga gwamnatin Turkiyya.

Masallanci Camii An Ginashi da Makarantar mai cike da yara. Makarantar tana Aiki a Ranar Asabar ne Kawai kuma makarantar tana Bada da darasi daga karfe 10 na safe zuwa 8 na yamma. Yayin da jagorancin makarantar ke sa ido a kan bayar da cikakken ilimin da suka hada da karatun Islama da Larabci, zuwa kira’at da kuma Geography.

Cibiyar Islama ta Japan (ICJ) ce ke tafiyar da makarantar, cibiyar musulmin da Aka kafa bayan yakin duniya na biyu da aka kafa a 1966. Omer – mai ba da shawara ga Jakadan Saudiyya kuma wanda ya taba zama jakadan Sudan a Japan sau biyu – shi ne shugaban riko.

See also  Gwamna Zabiya Na Farko A Tarihin Najeriya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button