Tambayoyi a Musulunci

IDAN MIJI MAI MATA BIYU YA YI TAFIYA, A INA ZAI SAUKA IN YA DAWO ?Tambaya*
Assalamu alaikum malam
Don Allah fatawa nake da ita, Wai gaskiya ne Shari’ah ta ba namiji mai mata fiye da daya dama idan ya dawo daga tafiya ya sauka dakin duk wacce ya ga damar sauka a dakinta cikin matanshi??

Amsa
Wa alaikumus salam
A zahirin nassoshin Sharia ana gina hakan ne akan yarjejeniyar da take cike da adalci, duk abin da kuka cimma na daidaito tsakaninka da matanka mutukar ba a cuci kowa ba ya Yi daidai .

Wasu malaman suna cewa in miji mai mata biyu ya yi tafiya in ya dawo zai dasa daga inda ya tsaya, in kuma matar ce ta yi tafiya a ranar girkinta to ta sarayar da hakkinta.

Allah ne mafi Sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa
28/3/2022

See also  ZAN IYA DORA RIBA, IDAN AKA WAKILTA NI SAYO ABU ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button