Tambayoyi a Musulunci

DAN ZINA ZAI GAJI MAHAIFIYARSA ?Tambaya:
Assalamu alaykum. Malam don Allah Malam innada tanbaya, Malam mace ce tayi cikin batare da aure ba, ta haihu kuma tana da kudi sai Allah yamata rasuwa toh malam yaron zaici gadonta.
Amsa:
Wa’alaikum assalam, idan mace ta yi cikin shege kuma ta haifi Da, daga baya ta mutu Dan zinar da ta haifa zai gaje ta, saboda Allah madaukakin sarki a cikin suratun Nisa’i aya ta: 10 ya yi wasiyya a bawa ‘ya’yaye gado, Dan zina kuma yana cikin jerin ‘ya’yayen mahaifiyarsa, wannan yasa zai gaje ta.

Dan zina ba ya gadon mahaifinsa a wajan mafi yawancin malamai, ko da kuwa ya yarda dansa ne.

Allah ne mafi sani.
23/5/2016

-Dr. Jamilu Zarewa

See also  JININ BARI BA YA HANA AZUMI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button