Tarihin malamaiTarihin Malaman Sunnah

TARIHIN IBN TAYMIYYA ( RA ) تقي الدين أحمد بن عبد الحليم بن عبد السلام النميري الحراني),[


Cikakken sunan Ibn Taimiyyah shine ‘ Taqiy al-Din ‘Abu al-Abbas ‘Ahmad ibn ‘Abd al-Hallim ibn ‘Abd as-Salam ibn ‘ Abdullah ibn al-Khiḍr ibn Muḥammad ibn al-Khiyr ibāllīr- ibn al-Khiḥr Ḥarrānī : أحمد بن عبد الحليم بن عبد السلام بن عبد الله بن الخضر بن محمد بن الخضر بن إبراهيم ب اللهن علي بن علي بن بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن عبد السلام .

Sunan Ibn Taimiyyah ( ابن تيمية ) ba a saba ganinsa ba ya samo asali ne daga wata mace daga cikin iyalansa sabanin namiji, wanda al’ada ce ta da a lokacin kuma har yanzu. Lakabin ” Taimiyya ” ya fito ne daga kakarsa wacce ake kira Taimiyyah. Ta kasance mai nasiha kuma an yi masa lakabi da ” Ibn Taimiyyah “. Taimiyya ta kasance fitacciyar mace, shahararriyar mai ilmi ta da takawa da sunan Ibn Taimiyya da yawa daga zuriyarta maza ne suka karba.

Ibn Taimiyyah, sunan haihuwa Taqī ad-Dīn ʾAḥmad ibn ‘Abd al-Hallim ibn ‘Abd al-Salam al-Numayrī al-Harrani, malamin Sunna ne, muhaddith, alkali, Salafist kuma masanin siyasa

Ahmad dan Abdulhalimu danAbdussalami dan Abdullahi dan Haliru dan Muhammadu dan Haliru dan Aliyu dan Abdullahi. Ya shahara da sunan Ibnu Taimiyyah saboda kakarsa da ake kira Taimiyyah. Ana kuma ce ma sa “Majduddini”. Sannan ana ce ma sa “Numairi” saboda shi dan kabilar Banu Numairi ne.

Sannan ce ma sa kuma “Harrani” saboda Harrana ne garin da aka haife shi. ( Yanzu Garin Yana Cikin Kasar Turkey ????????)Sannan
ana ce ma sa “Dimashki” saboda a garin Dimashka ( Damascus Syria ???????? ) ne ya girma, ya yi karatu.


ASALINSA


Ibnu Taimiyyah dan asalin kasarTurkiyyah ne. Don an haife shi a garin Harrana wadda take arewa maso gabascin qasar ta Turkiyyah.


Haihuwa


An haife shi ne a ranar litinin 10 ga watan Rabi’ul Awwal 661H Wanda Yazo Dai-Dai Da 22 Janairu 1263, Amma bayan shekaru shida sai iyayensa suka yi hijira daga kasar zuwa kasar Siriya inda suka sauka a babban birnin Dimashka, hedikwatar Sham.
Dalilin hijirar tasu kuwa shi ne kaucema fitinar ‘yan Tattar wadanda suka auka ma garuruwan musulmi suka yawaita
Barna da zubar da jinin bayin Allah. Game da mahaifansa kuwa, shi dan gidan malamai ne. Domin ya sami kansa a tsakanin iyaye da kakanni da ‘yan’uwa ma’abota karatu. A lokacin da zasu yi hijira kuwa babu abin da ya wahalar dasu kamar littafai da ke tare da su masu dinbin yawa, ga shi kuma suna gudun
makiya.

Ba domin kiyayewar Allah ba ma ba zasu tsira da rayukansu zuwa Sham ( Syria ????????) ba. Isarsu qasar Sham ke da wuya mahaifin Ibnu Taimiyyah Shihabuddini ya fara koyarwa da wa’azi a babban masallacin Jum’ah na Dimashka wanda ake kira Al-
Jami’ul A’azam masallaci mafi girma. Daman shi fitaccen malamin furu’a ne a mazahabar Hambaliyya. Nan take aka
shugabantar da shi ga babbar makarantar hadisinnan da aka sani Darul Hadis As-Sukkariyyah, aka kuma ba shi gida a cikin makarantar in da nan ne Dansa Ibnu Taimiyyah ya girma. Kafin haka, kakan Ibnu Taimiyyah Majduddini sanannen malami ne da ya yi wallafe-wallafe a fannin hadisi da Usulul Fiqhi shine mawallafin littafin nan na Muntakal Akhbar wanda Imamus
Shaukani ya yi wa sharhi a cikin Naulul Audar. Haka ma baffansa Fakhruddini, malami ne fitacce daya wallafa babban littafin Tafsirin Alqur’ani. Shi ne kuma wanda ya gaji Ibnul Jauzi a kujerarsa ta karantarwa da babban mumbarinsa na Bagadaza.
Kuma IbnuTaimiyyah ya yi karatu a wurinsa.

Tashinsa da Iliminsa Ibnu Taimiyyah ya tashi a gidan ilimi kamar
yadda muka gani. Ya kammala hardar Alqur’ani tun a lokacin kuruciya. Sannan ya kula da sanin ilimoman Fikihu da Hadisi da Tafsiri da Arabiyyah.

Ya soma karantarwa da fatawa da rubuta littafai da tattaunawa da malamai Munazara tun bai wuce shekaru 20 Ba. Koda ya cika shekaru 30 an fara yi masa lakabin Mujtahidi kuma “Mairaya Sunnah”. Yana da matukar wuya a iya siffanta baiwar da Allah ya yi wa Ibnu Taimiyyah ta fuskar ilimi. Masu ba da labarinsa na
ganin kasawarsu wajen bayyana irin hikimomin da ke tattareda shi ta wannan haujin. An lisafta malaman da ya gurfana a gabansu don daukar karatu aka tarar sun zarce malamai 200.

Akwai kuma littafan da ya karanta su sau da yawa a wurare daban-daban kamar Musnad na Imamu Ahmad.

Game da nasa littafai shi kuma, Ibnu Taimiyyah ya wallafa sama da littafai hamsin a fannona daban-daban na addini, banda jananan wallafe-wallafensa da aka tara cikin Majmu’ul Fatawa mai sifili talatin da bakwai.

Ya ishi mai karatu misali abin al’ajabi cewa, duk da yake Ibnu Taimiyyah bai wallafa Tafsirin Alqur’ani ba, amma malamai daga bisani sun wallafa shi daga cikin littafansa. Ma’ana an tattara
wuraren da ya yi sharhi akan ayoyin Alqur’ani daga ciki littafansa a tsakankanin maganganunsa da kafa hujjojinsa, sai ga shi an samu kusan kammalallen Tafsiri mai Mujalladi hudu.

Mujaddadi Ibnu Taimiyyah Muna iya cewa, Allah gwanin sarki ya
tashi Ibnu Taimiyyah ne a wani lokaci da bukatar irinsa ta yawaita. Don kuwa a wancan lokaci al’umma tana fama da matsaloli da rikici da tashin hankula na ciki da na waje. Daga cikin gida musulmi na fama da rabuwar kai, da yawaitar kungiyoyi da yaduwar bidi’ah da raunin ilimin furu’a.

Ga kuma lalacin da ya yazo a cikin jama’a da zaluncin sarakuna da kwadayin malamai. Tsibbace-tsibbace da bokanci da duba sun zama gama-gari a cikin al’umma. Daga waje kuma ‘yan mishan sun kaima musulmi farmaki, ‘yan Shi’ah masu kiran
kansu Fadimawa sun hada kai da su. Sannan ga Tattar sun shelanta mummunan Yaki da musulunci da musulmi a duk in da suke a wancan lokaci.

Shaihun musulunci ya fuskanci duka wadannan matsaloli da nufin magance su. Ya kuma samu taimakon Allah matuka a wajen cimma wannan gurin nasa.

Mutum ne da aka suffanta shi da kaifin basira da karfin kwakwalwa, har wasu ma na ganin bai taba sanin abu ya manta
da shi ba. Yanada karfin tuna ayoyin Alkur’ani da nassosan hadissai da maganganun malamai na kowane fanni. Don haka ya kasance mai kaifin hujja wadda take yanke wuyan abokin gaba nan take.

Ga shi kuma jarumi da ba ya tsoron ko-ta-kwana. Don haka ba ya da ja da baya ga abin da ya sa gaba. Sannan yana da kwarjini a idon jama’a da kyawawan dabi’u da suka dada soyar da shi ga mutane. Ga shi mutum mai kishin gaskiya da kokarin yada ta. Hada da halinsa na gudun duniya da rashin kula da jin dadinta. Irin wannan malami Allah ya dora shi a kan kyakkyawar hanya irin ta Annabawa wane irin canji kake tsammanin al’umma ba za ta ci moriyarsa ba ta hanyarsa?

Dan Taimiyyah nan take ya rurrusa akidun da suka zame ma musulunci tsutsar goro ta hanyar rubuce-rubucensa da wa’azozinsa da karantarwarsa. Ya kece raini a wajen wargaza akidun Yahu-dawa da na ‘Yan mishan. Ya yi fada da kungiyoyi mabiyan son zuciya irin mulhidai da zindikai da ‘yan Shi’ah da
wadanda suka wuce wuri a Sufanci.

Ya yi kira ga koma ma littafin Allah da Sunnar Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ba tare da ta’assubanci ga wani mutum ko kungiya ko mazhaba ba. Sa’annan ya kira sarakuna da talakawa zuwa ga yakar kafi’-rai wadanda suka keta hurumin musulmi, musamman dai Tattar. Ya kuma fita ya yi Yaki a matsayin daya daga cikin sojoji. Tare da haka kuma Ibnu Taimiyyah ya kafa wata makaranta da Allah ya yawaita almajiranta tun daga wancan zamani har zuwa yau, kuma tana ci gaba da bunkasa har a nade kasa.

Wannan makaranta tasa tana mutunta magabatan Sahabbai da Tabi’ai da wadanda suka biyo bayansu, da shugabannin mazhabobi, tana kuma la’akari da ra’ayoyinsu da fatawoyinsu
baki daya.Tana kuma rinjayar da nassi ingantacce idan ya zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan maganar kowa kome darajarsa.

Wannan makaranta dai tana da daruruwan littafai da Dubbanin malamai a cikinta. Dukkaninsu suna jingina kansu ga Sunnah da biyar magabata ba ga shi Ibnu Taimiyyah din ba. Jarabawar Da Ibnu Taimiyyah ya Gamu da Ita Yana da wuya Allah ya daukaka wani bawansa ba tare da ya gamu da wata jaraba ba a rayuwarsa. Wannan ita ce sunnar Allah ga Annabawa da
malamai mutanen kirki.

Shehun musulunci ya gamu da jarabce-jarabce da dama a sakamakon jiha-dinsa na makami da na alkalami wadanda suka dagula ma sa jin dadin rayuwa.

Zan fadi wasu daga cikinsu a takaice kamar yadda suka zo a tarihinsa daga littattafai da dama. A shekarar 696H ya gamu da kyashin Daga abokan tafiya, malamai, wadanda suka Dauki littafinsa Al-Fatwal Hamawiyyah suka kai kararsa da shi a wurin
mahukunta. Sun bi duk hanyoyin da suke iyawa wajen murza maganarsa da ba ta irin ma’anar da suke so su jingina ma sa. A wannan lokaci sarki Saifuddin Jagan ya goyi bayan Ibnu Taimiyyah, ya kuma husata da wadanda suka kafa adawa da
shi. Don haka wannan jarrabawa ba ta dade ba ta Gushe.

A shekarar 705H lokacin da farin jinin Ibnu Taimiyyah ya gama bayyana, bayan an ga rawar da ya taka a yakin da aka yi da Tattar, har kuma ya samu kusanci da hukuma abin da ya ba shi damar sa a kawar da wasu barnace-barnace. Nan take sai kurjin hasada ya sake Tashi a zukatan wasu malamai daga cikin sufaye. Sai wani malami da ake kira Nasrul Mambiji da wani malami bamalike ana ce ma sa Ibnu Makhluf suka tafi hedikwatar masarauta da ke kasar Masar ( Egypt ???????? ) su ka kai karar Ibnu Taimiyyah suna tuhumar sa da gurbata akidun jama’a. Suka kafa hujja da littafinsa na Al-Akidatul Wasiziyyah. A nan ma sarki ya ba da umurni aka zaunar da shi tare da manyan malamai in da aka karance littafin nasa, daga karshe kuma aka barrantar da shi daga sabama magabata. Sai ma a wannan karon ya samu takardar yabo daga Sarkin Musulmi. Wata daya bayan faruwar wannan, sai wadannan malaman suka sa sarki ya
rubuta ma sa wata takarda ana neman sa da zuwa Misra ( Egypt ????????) don ya bayyana a gaban sarki. A wannan karon da tuhumar yana neman sarauta!

An dai zaunar da shi a gaban Ibnu Makhluf don ya yanke ma sa
hukunci, abin da dan Taimiyyan ya ki yarda dashi, kasancewar shi ne abokin mai husumar da ya kai kararsa. Shehul Islami sai da ya share wata goma sha biyu Cif a gidan kurkuku kafin a nemi ya fita, in da shi kuma ya ki fita ya ce, sai an bayyana ma sa laifinsa. Daga karshe ya fita daga kurkukun bayan ya cika watanni goma sha biyar da sati biyu da kwana daya bisa ga nacewar wani basaraken garinsu.

Wata bakwai bayan fitowarsa sai aka sake mayar da shi a cikin watan Shawwal na 707H saboda ya ci gaba da zama a Masar mutane na amfana da shi. A wannan karon sai ya kasance mutane suna tururuwa a gidan kaso don gaishe shi da yin fatawa a wurinsa, abin da ya dada cinna wutar gaba a tsakaninsa da wadanda ke bibiyarsa da bakar Aniya.

Bayan fitowarsa ma, dan Taimiyyah bai fasa abin da yake yi na karantarwa da fallasa miyagun akidu ba. Wannan ya sa aka dauke shi daga Alkahira zuwa Iskandariyya da nufin ya hadu da ‘yan dabar garin su kashe shi.

Ana haka ne sai aka samu canjin gwamnati lokacin da sarki Muhammad dan Kalawun ya sake koma ma kujerar sarauta sai ya mayar da Shehul Islami zuwa hedikwatar ta Masar. Daga nan kuma suka fita a shekarar 712H da nufin yakar kafi-ran Tattar, sai Allah ya mayar da makiyan garuruwansu ba tare da an yi yaki ba. Don haka, sai Ibnu Taimiyyah ya koma gida Sham, in da ya hadu da tarba wanda ba a taba ganin irinta ba!

bayan ya yi shekara bakwai da sati bakwai a kasar Masar tun wancan kiran da aka yi ma sa. Ko bayan komawarsa gida Shehul Islami ya ci gaba da samun matsaloli da malamai masu karamin sani da taurin kai. Kamar yadda suka yi caa akansa wai
don ya ce, in mutum ya yi rantsuwar saki kaffara kawai zai yi, aurensa na nan. Haka ma don cewar da ya yi saki uku na komawa daya idan an yi su zama guda. Wadannan malamai ba su samu sukuni ba sai da suka sa aka hana shi fatawa a
shekarar 719H.

A shekara ta 720H aka sake iza keyar babban malamin zuwa gidan kaso in da ya share wata biyar da kwana goma sha takwas.

A shekara ta 726H wasu alkalai sun tsoma bakinsu a cikin rikicin Ibnu Taimiyyah da makiyansa, in da aka wallafa wata fatawa ta karya aka jingina ta gare shi, wai ya haramta ziyarar kabarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da na sauran Annabawa. Alhalin shi kuwa ya rarrabe tsakanin ziyararsu ne ita kadai da kuma hada ta da yin tafiyayya. Ya labarta sabanin
magabata a kanta, sannan ya nuna karkata ga hanawa idan ya kasance an yi tafiyayya saboda ita. Ya kuma bayyana hujjojinsa na ingantattun hadissai.

Wannan rikicin ma dai sai da ya sake mayar da wannan bawan Allah a gidan maza, in da ya samu damar da ya yawaita wallafe-wallafe gami da bautar Allah Ta’ala.

A shekara ta 728H aka fitar da duk littafan da ke tare da shi da alkalumma da tawadar da aka samu a wurinsa, saboda wani malami da ake kira Ikhna’i ya kai karar sa, don ya yi ma sa raddi, kuma wai ya jahiltar da shi.

A nan ya zama dole Ibnu Taimiyyah ya hakura ya dukufa ga zikiri da sallah da karatun Alkur’ani da yake wadannan suna a
kansa tun zamanin quruciya.
See also  TARIHIN SHIEKH IBRAHIM INYASS


RASUWARSA


Ya fara rashin lafiya a farkon Satumba 1328
Allah ya karbi ransa a gidan kurkuku na birnin Dimashka ( Damascus Syria ???????? ) yana da shekaru 67 wadanda suke cikeda karantarwa da hakuri da jiha-di. Ya rasu kafin wayuwar garin litinin 20 ga watan Zul Qi’ida 728H. Wanda Yazo Dai-Dai Da 26 Satumba 1328.

Da wannan labari ya isa ga jama’a, sai aka yi ta nuna goyon bayansa ga jama’a. Bayan da hukumomi suka ba da izini, an ba da rahoton cewa dubban mutane sun zo don nuna girmamawa. Sai suka taru a cikin Kagara suka yi jerin gwano har zuwa masallacin Umayyawa. An gudanar da sallar jana’izar a cikin kagara wanda malami Muhammad Tammam ya yi, kuma an yi na biyu a masallacin. An yi sallar jana’iza ta uku kuma ta karshe ta dan’uwan Ibn Taimiyyah, Zainul-Din. An binne shi a Damascus, a Maqbara Sufiyya (“makabartar Sufaye”). An binne dan uwansa Sharafuddin a makabartar da ke gabansa.

An ruwaito cewa maza dubu dari biyu da mata dubu goma sha biyar zuwa goma sha shida ne suka halarci sallar jana’izarsa. Ibn Kathir ya ce a tarihin Musulunci, jana’izar Ahmad bn Hanbal ne kadai ya samu halartar Kamar Wannan taron.


IYALI


Bai yi aure ba ballantana ya bar zuri’a. Bai kuma taba furta kalma daya da take nuna rashin sha’awarsa ga auren ba.

To, ko me ya hana shi cin moriyar
wannan Sunnah?

Sanin gaibu sai Allah.


Dalibai


Da yawa daga cikin daliban Ibn Taimiyya sun zama malamai a nasu bangaren. Dalibansa sun fito ne daga wurare daban-daban kuma sun kasance a makarantu daban-daban (mahabbai). Shahararrun dalibansa su ne Ibn Qayyim Al-Jawziyya da Ibn Kathir. Sauran dalibansa sun hada da:

1, Al-Dhahabi
2, Al-Mizzi
3, Ibn Abdil-Hadi
4, Ibn Muflih
5, ’Imad al-Din Aḥmad al-Wasiti
6, Najm al-Din al-Tufi
7, Al Ba’labakki
8, Al Bazzar
9, Ibn Qadi al-Jabal
10, Ibn Fadlillah al-Amri
11, Muhammad Ibn Al-Manj
12, Ibn Abdus-Salam al-Batti
13, Ibn al-wardi
14, Umar al-Harrani

See also  TARIHIN SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button