Tarihin Malaman Sunnah

TARIHIN SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI

Sheikh Abubakar Mahmud Gumi (An haife shi a ranar 5 ga watan Nuwamba a shekara ta 1922 ( Wanda Yazo Dai-Dai da ranar Juma’ar karshe na watan Ramadan shekara ta 1344 ) A Kauyen Gumi Yanzu karamar Hukuma A Jihar Zamfara ya kuma rasu a ranar 11 ga watan Satumba shekara ta 1992, a Landan) shahararren Malamin Addinin musulunci ne kuma Alkalin Alkalai (Grand kadi) na arewacin Najeriya. Shi ne uba, jigo kuma tushen Izala da Salafanci a Najeriya.

mahaifinsa Mahmud Ya Rasu a shekara ta 1937 a lokacin da yake makarantar sakandare. Ya yi aure bayan shekara 3 da Rasuwar mahaifin Da Maryam a shekara ta 1941 yana dan shekara 19

Karatu.

Ya yi karatu da rubuce-rubuce a kan addinin musulunci sosai, ya fassara Al Qur’ani zuwa harshen Hausa da kuma rubuta tarjama wato fassarar dai-daikun ayoyin dake Alkur’ani.

Kyautar Sarki Faisal

shekarar 1987, Gumi ya lashe kyautar Sarki Faisal Saboda hidimar da Yake Yiwa Muslunci Da tarjamar kur’ani mai tsarki zuwa harshen Hausa. Kyautar Ta Kai Dubban Daruruwan Daloli a haɗe a matsayin kyauta. ‘Yan Najeriya da yawa za su iya tsammanin Gumi Zai Gina Wani sabon gida mai Kyau don maye tsohon gidansa a Kaduna, wasu kuma sunyi tsammanin zai debi kudin ya zuba jari A bankuna ko kuma Ya sayi sabbin motocin Hawa.

Amma wannan tsamani na yan Najeriya bai samu tabbatuwa ba
Abinda Malam yayi shine tara yan’uwa da Abokan Arziki da Almajiransa ya raba musu Malam bai tsira da komai ba,
Wannan Ne Yasa Marigayi Yusuf Maitama Sule Yayi Masa Kirari Yake Cewa ( Ko Kayi Karatu Irinna Malam Ba Zakayi Hali Irinna Malam Ba! )

Kuma ya sami kyauttuka na girmamawa a lokacin rayuwarsa kamar Malamin nan mutumin Siriya (Sham) mai suna Shaikh Sa’ad Yaseem-Assuri, wanda Malam (Sheikh Abubakar Mahmud Gumi) ya koyi karatun Kur’ani da Tajwid a wurinsa ya ba shi Shahada, da kuma Firimiyaan Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakwato ya ba shi lambar yabo saboda da shi ne mai yi masa tarjama in ya je kasashen Larabawa a lokacin da yake raye.

See also  TARIHIN IBN TAYMIYYA ( RA ) تقي الدين أحمد بن عبد الحليم بن عبد السلام النميري الحراني),[

Kuma Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa mai suna (C.F.R), haka kuma Jami’ar Islamiyah da ke Madina a kasar Sa’udi Arabiya ta sa shi daga cikin Malamai masu ba ta shawara har sau uku. Haka nan mai girma Jamal Abdulnasir wanda yake shugaban hadin kan kasashen Larabawaa lokacin da yake mulki, ya ba shi takardar girmamawa saboda yada addinin Musulunci a duniya.

Abotarsa Da Sardaunan Sakkwato.

Malamin dai ya kasance babban aboki kuma mai ba wa Firimiya Ahmadu Bello sardaunan Sakkwato shawara. Shi ne mahaifin Dakta Shaykh Ahmad Gumi.

A lokacin da Gummi ya rasu yana da shekaru 70 a duniya a shekarar 1992, an kwatanta mutuwarsa da “karshen zamani”.
John Paden (1986) ya tuna cewa a lokacin Marigayi Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello na farko zuwa Makkah a shekarar 1955, Gumi ya zama mai fassara na Sardauna “tun Sarki Saudi A Lokacin Baya jin Turanci.

Gummi tare da Marigayi Sardauna, sune Su ka kafa kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) a shekarar 1962. Masallacin Sultan Bello da Sardauna Ya Gina shi ne cibiya Da jijiya ta JNI a shekarun da A Ka Kafata, A lokacin da aka fara tunanin Kafa JNI, Gummi da sauran su “sun hadu a gidan Abubakar Imam.. (sun gina makarantar firamare ta Sultan Bello, garejin Gummi a Unguwar Sarki ta zama makaranta” (shafi na 561). Gummi ya taba zama tsohon jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, tsohon mamba a hukumar kula da harkokin shari’a, Kum Gummi Ya zama  Grand Khadi na jihohin Arewacin Najeriya (har ya yi ritaya daga aiki a shekarar 1975) sannan kuma tsohon shugaban hukumar alhazai ta kasa.

A shekarar 1957 ya zama mai fassara ga gwamnatin Arewacin Najeriya kan al’amuran Saudiyya .

See also  TARIHIN IBN TAYMIYYA ( RA ) تقي الدين أحمد بن عبد الحليم بن عبد السلام النميري الحراني),[

Shahara.

Gumi ya shahara tun lokacin mulkin mallakar turawa a matsayin mai fada a ji, yana sukar salon Mulkin Turawa cewa ya karya lagon sarakunan Musulmi kuma hakan yana kara karfafa al’adun Turai a kasashen musulunci. A farkon shekarar 1960s an samu barkewar rikici tsakanin shi da malaman sufaye wanda daga baya rikicin ya koma muhawara a gidajen rediyo da talabijin a shekarun 1970 zuwa shekarar 1980. Ya riƙa amfani da ranakun Juma’a a matsayin lokutan yada akidunsa a babban masallacin juma’a na Kaduna mai suna Masallacin Sultan Bello.

Gudunmawar Sa Ga Gwamnatin Janar Yakubu Gowon A lokacin Yakin Basasar Najeriya.

Janar Yakubu gawon yace a lokacin yakin basasar Najeriya, yana takawa a cikin sirri har zuwa Kaduna domin ya nemi shawarar shiek Abubakar gumi, kuma yace Gumi yana bashi shawarar da idan an aiwatar kwalliya na biyan kudin sabulu.

Kiransa ga yan Arewa da su shiga siyasa da aikin soja

Allah ya jikan Abubakar Gummi A Cikin wa’azin sa yasha Nanawa Yan Arewa musammam Musulmi da Shiga Aikin Soja Da Yansanda da Sauran ma’aikatun Gwnati da siyasa, wannan fatawa tasa tayi mutukar amfani ga yan Arewa,  Da ba dan Marigayin ba da tazarar da za’a yiwa yan Arewa tafi wacce ake gani yanzu.

Uban Kungiyar izala.

Abubakar gumi wanda ake yi wa lakabi da mahaifin izala kamar yadda ya saba ambata a lokacin da yake koyar da addinin musulunci, ya samu nasarar kafa kungiyar a shekarun 1970s mai suna izalatul bidi’ah wa iqamatussunah, A aikin da ya yi a baya a matsayin malamin makaranta a makarantar koyon harshen Larabci ta SAS da ke Kano, duk da cewa ya ci gaba da zama a jam’atu nasrul Islam (JNI) wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da karantarwar Musulunci a masallacin kaduna Central da aka mika masa.

Gumi ya yi imanin cewa, Musulmin Nijeriya bai kamata su taba yarda da wanda ba Musulmi ba, amma kuma ya bayar da shawarar a zauna lafiya da kungiyoyin da ba Musulmi ba.

See also  TARIHIN IBN TAYMIYYA ( RA ) تقي الدين أحمد بن عبد الحليم بن عبد السلام النميري الحراني),[

Gudunmawarsa A Bangaren Ilmi

Kadan daga wallafaffun littafansa akwai littafi mai suna Nazamul Kadidatu Lamiya wacce ya yi don ta’aziyyar Abdullahi Bayero Sarkin Kano.

Da wata kasida ta Kafiya wacce ya yi ta a lokacin da yake dalibta a kasar Sudan mai baitoci 34.

Kuma ya yi tafsiri mai Suna RADDUL-AZHAN ILA MA’ANIL-KUR’AN, da kuma littafinsa mai suna AKIDATUSSAHIHATBI MUWAFAKATUS SHARI’A.

Haka kuma akwai Tarjamar Al-Kur’ani Zuwa Harshen Hausa. Da kuma Tarjamar littafin Arba’una Hadis, zuwa harshen Hausa. Da kuma Tarjamar littafin Usuluddeen da Tauhid zuwa harshen Hausa, da kuma wani littafi maisuna Mir’atul Dullab Fee Masnadil Abwab, da dai sauransu.

Kuma ya fassara wasu littattafai masu yawa a cikin kasakasai da sidi da DVD kamar irin su Ahdari, Ashmawi, Iziyya da Risala da Mukhtasar Halil da Bukhari da Fatahul Majid da sauransu.

Da kumalittafinsa mai suna WURDINL-AZIM MINAL KUR’ANIL KARIM WAL-AHADISIL SHARIF.

Mutuwarsa.

Sheikh Abubakar Mahmud ya rasu ranar Juma’a 11 ga watan 9 a shekarar 1992, sakamakon rashin lafiya.

Shugabanni da yawa sun halarci Jana’izar sa wanda aka yi a garin Kaduna, kamar su shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da Ministoci da Sarakuna da Talakawa na kasar nan da kuma ketare.

Iyali

Ba a san takamaiman yawan ƴaƴansa ba, amma mafi shahara a cikinsu shi ne Dr. Ahmad Gumi Wanda shi ne ya gaji Mahaifinsa a matsayin mai gabatar da wa’azi a masallacin na Sultan Bello. Dr Ahmad Gumi kwararren likita daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Kuma tsohon jami’in sojin Najeriya ne, ya bar aikin soja inda ya tafi zuwa Saudiyya domin karanta ilimin fikihu, a jami’ar Ummul Quraa da ke birnin Makka inda ya samu shaidar digirin digir-gir.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button