Tambayoyi a Musulunci

MAI AZUMIN NAFILA ZAI IYA KARYA AZUMINSA DA GANGAN !Tambaya:
Assalamu alaikum. Na wayi gari da Azumi sai aka kawo abinci sai na fasa Azumin naci abincin, Malam yin hakan akwai laifi na Shari’a?

Amsa:
Wa alaikum assalam. Ya halatta abin da kayi, saboda faɗin Annabi (S.A.W.): “Mai Azumin nafila sarkin kansa ne, in yaso ya ci gaba da Azumi, in yaso kuma ya karya”, kamar yadda Tirmidhi ya rawaito..
Allah ne mafi sani.
25/07/2016

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

See also  INA YAWAN SAƁON ALLAH, MENENE SHAWARA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button