Tarihi

Kisan Shugaban Kasar Nijar Ba a re Mainasara

A Ranar Juma’a 9 Ga Watan Afrilu 1999; Jami’an tsaron sa na fadar shugaban kasar suka kashe shugaban kasar Nijar Ibrahim Bare Mainassara a lokacin da yake hawa wani fili a Yamai babban birnin kasar ta Nijar. Nan da nan bayan faruwar lamarin, an rufe layukan sadarwa, gidajen rediyo da kan iyakoki. Sojoji sun kewaye birnin Yamai, sun killace filin jirgin saman kasa da kasa. An yi jana’izar sa kwanaki biyu bayan rasuwarsa a wani jana’izar da ‘yan uwa da jami’an diflomasiyyar kasashen ketare suka halarta.

Firai minista Ibrahim Assane Mayaki ne ya sanar da mutuwar Mainassara a matsayin wani mummunan hatsari, wanda A cewarsa Marigayin ya yi yunkurin rusa majalisar dokokin kasar tare da dakatar da duk wasu harkokin siyasa.

Sai dai jam’iyyun adawa sun yi watsi da jawabin na Mayaki bisa hujjar cewa shugaban majalisar ba zai iya rushe majalisar ba. Mayaki ya kuma bayyana cewa sojoji za su yi mulki har sai an yanke shawarar kafa sabuwar gwamnati ta “hadin kan kasa”.

Manyan hafsoshin sojan da ke da alaka da kisan, da kuma ‘yan siyasa da ke adawa da mulkin tsohon shugaban kasar, sun gana a karshen mako inda suka nada Manjo Daouda Mallam Wanke, kwamandan rundunar tsaron kasar ta Nijar a matsayin wanda zai gaji Mainassara. Gidan rediyon jihar Nijar ya sanar da cewa Wanke zai jagoranci majalisar sasantawa ta kasa tsawon watanni tara.

Marigayi Ibrahim Ba’are Mainassara wanda ya shugabanci Nijar a zamanin jamhuriya ta 4 mutun ne wanda ake yi wa kyakkyawar shaida.

General Ibrahim Ba’are Mainassara wanda ya hau karagar mulki bayan kifar da shugaba Mahaman Ousman a ranar 27 ga watan Janairu 1996 ya shirya zaben da ya ba shi damar doke abokan karawarsa.

See also  Tarihin Tsohon shugaban Nijar, Mirigayi Janar Ibrahim Bare Mai Nasara

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button