Tarihi

Tarihin Tsohon shugaban Nijar, Mirigayi Janar Ibrahim Bare Mai Nasara

Kanal Ibrahim Baré Maïnassara (An Haifeshi Mayu 9, 1948 a birnin Dogon Dutse Ya mutu Afrilu 9, 1999 a birnin Niamey) sojan Jamhuriyar Nijar ne wanda ya karbi mulkin kasar a wani shiryayyen juyin mulki a kasar Nijar a 1996 kuma ya shugabanci kasar har shekarar 1999. Maïnassara, dan kabilar Hausawa ne mai rinjaye a birnin Dogondoutchi wanda aka haifeshi a shekarar 1948, Maïnassara ya zama babban jami’in soja a 1995.

Yayi karatunsa na makarantar firamare a birnin Yamai, kafin daga bisani ya samu horon soji a kasashen Madagaska da kuma Faransa.

Sai a shekara 1974 ne a lokacin yana da shekara 25, ya koma bangaren shugaba Seyni Kuntche, inda suka jagoranci juyin mulkin da Ya Hambarar Da Gwamnatin Dior Hamani Wanda ya kai Seini Kuntse Darewa kan karagar mulki. A Shekarar 1976, aka nada Bare a matsayin kwamandan rundunar sojin tsaron fadar shugaban kasa.

Shekaru biyu bayan hakan kuma ya jagoranci bataliyar sojojin sama ta Yamai. A 1992, ya zama mai baiwa firaministan rikon kwarya na lokacin Amadu Chefu, shawara kan harkokin tsaro.

Bayan zaben farko bisa tsarin demukuradiyya Wanda da ya kai shugaba Mahaman Usman kan madafun iko, an nada shi babban hafsan soji na shugaba Mahamane Usman a watan Afrilu na 1993.

A Ranar 27 ga watan Janairu 1996, Kanal Ibrahim Bare Mainasara, ya jagoranci kifar da gwamnatin Mohamman Ousman bayan da aka samu rikicin Siyasa tsakanin shugaban kasa da Firaminista Hama Amadou a shekarar 1995, kan zaben majalisar dokokin da aka gudanar yana mai nuni da mawuyacin halin siyasa da aka shiga a matsayin hujja.

A watan Mayu na 1996, Kanal Bare ya nada wani kwamiti da zai sauya kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka amince da shi bayan kada kuri’ar jin ra’ayin jama’a, abinda ya kai kasar ga Kafa jamhuriya ta hudu.

See also  Tarihin Nunuk Nuraini Matar Da ta kirkiro Da Indomie

A karkashin mulkin Mainassara, an amince da sabon kundin tsarin mulki ta hanyar kuri’ar raba gardama a watan Mayun 1996, kuma an gudanar da zaben shugaban kasa a ranakun 7-8 ga Yuli, 1996. Mainassara Wanda Ya tsaya A karkashin tutar jam’iyyar RDP (Rally for Democracy and Progress-Jama’a) yayi Nasara da kusan kashi 52% na kuri’un da aka Kada, amma ana kallon zaben a matsayin Wanda Aka Tafka magudi. Sai ‘Yan adawa sun ki amincewa, domin a tunaninsu an yi aringizon kuri’u mafarin barkewar hayaniyar da ta yi sanadin hallaka shi da sunan juyin mulkin wanda Commandant Daouda Malan Wanke ya jagoranta.

A rana ta biyu da zaben ya sa aka rusa hukumar zabe tare da maye gurbinta da wata hukumar zabe ta daban. A wannan rana, ya sa an daure ‘yan takarar jam’iyyar adawa hudu a a gidan yari.

An rantsar da Mainassara a ranar 7 ga Agusta abinda ya bashi damar ci gaba da kasancewa shugaban kasa, har zuwa watan Aprilun shekarar 1999.

Mutuwa

A ranar 9 ga Afrilu, 1999, sojoji, wadanda rahotanni suka ce wasu jami’an tsaron fadar shugaban kasa ne suka yi wa Mainassara kwanton bauna, suka harbe shi har lahira a filin tashi da saukar jiragen sama na babban birnin Yamai a lokacin da zai hau jirgi mai saukar ungulu yana yunkurin tserewa daga kasar.
(Ba Tabbas)

Dalilin kisan da ba a bayyana ba; jita-jita na nuna cewa Mainassara na ƙoƙarin tserewa daga ƙasar. Da farko an kwatanta mutuwarsa a hukumance a matsayin wani “haɗari amma wannan da’awar ba a yi la’akari da ita a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

Jagoran juyin mulkin Daouda Malam Wanké ya gaje shi a matsayin shugaban kasa kuma ya kaddamar da sauyin siyasa wanda ya kare da zabe a karshen shekarar.

See also  Tarihin Annabi Hud (AS) Da Adawa

Kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a zaben raba gardama na watan Yuli na shekarar 1999 ya tanadi yin afuwa ga wadanda suka Aiwatar juyin mulkin 1996 da 1999. An fara gudanar da bincike kan mutuwar Mainassara a watan Yunin 1999, amma bayan afuwar an kawo karshensa a watan Satumba. Jam’iyyar RDP (Jama’a) ta bukaci a gudanar da bincike na kasa da kasa kan mutuwarsa a cikin shekarun da suka gabata.

A shekarar 2013 dangin marigayin su 11 suka kai kara kotun ta ECOWAS suna neman ta tilasta wa gwamnatin Nijar nemo wadanda suka kashe shi a shekarar 1999, a kuma hukunta su.

Shekara 24 bayan kisan General Ba’aré har yanzu dangi na jiran jin yadda abin ya faru don a san wadanda ke da hannu.

Yunkurin zakulo wadanda suka hallaka shugaba Ibrahim Ba’aré Mainassara ya citura a cikin gida domin wata ayar doka da ke kunshe a kundin tsarin mulkin kasar Nijar ta yin afuwa ga sojojin da suka yi juyin mulkin Janairu 1996 da na Afrilun 1999.

Dalilin kenan da ya sa makusantansa suka garzaya kotun CEDEAO wacce ta umurci gwamnatin Nijar ta biya iyalinsa diyya.

Mirigayi Bare Mai Nasara musulmi ne, yana da mata guda da ‘ya ‘ya biyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button