Tambayoyi a Musulunci

HUKUNCE-HUKUNCEN MAI TAKABATambaya:
Assalamu alaikum wa rahmatullaah. gafarta Malam pls ayi mana bayani koda a takaice ne dangane da hukunce – hukuncen takaba… Na shiga wajen mahaifiya dazu, take cewa in tambaya mata Malamai tanadin shari’a akan wannan al’amari. Nagode

Amsa:
To dan’uwa ina rokon Allah ya jikan mahafinku, akwai hukunce-hukunce da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki:
1. Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba, har sai ta gama iddarta, wacce take wata hudu da kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan .
2. Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304, ya yi bayanin hakan.
3. Shari’a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar da hakan,
4. Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali ba , kamar yadda hadisin Nasa’i mai lamba ta: 3565 ya bayyana hakan.
5. An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304.
6. Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko da rana ne ko da dare.
7. Za ta iya yin Magana da mazan da ba muharramanta ba, idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul-ahzab ta hana sanyaya murya ga wadanda ba muharramai ba.
8. Babu wani launi na kaya na musamman da aka shar’anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su .
9. Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi ba .
10. Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har ma za ta iya bude gashin kanta, idan su duka muharramanta ne .
11. Bai halatta wani ya nemi auranta ba, har sai ta gama idda, saidai za’a iya yin jirwaye mai kama da wanka, kamar yadda aya ta 235 ta yi nuni zuwa hakan.
12. Idan mai takaba tana da ciki, to iddarta ita ce: haife abin da take dauke da shi, kamar yadda hadisin Subai’a mai lamba ta: 5014 a Sahihul Bukhari ya tabbatar da hakan.
Allah ne mafi sani.

Jamilu Zarewa
27\3\2015

See also  JININ BARI BA YA HANA AZUMI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button