Abu shida da suka kamata ku sani kan sallar tahajjud
Ɗaya daga cikin ibadun da Musulmi ke yi a watan Ramadana ya kunshi salloli da ake yi a cikinsa wadanda ba cika yi a sauran watanni ba. Sallar tahajjud na cikin salloli na musamman da ake yi, wadda yawanci ake farawa daga goman karshe na watan azumi.
BBC ta tattauna da wasu fitattun Malamai a Najeriya kan abubuwan da suka shafi sallar ta tahajjud.
Wace rana ake fara tahajjud?
Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke jihar Kaduna, Sheikh Halliru Maraya, ya ce ita sallar tahajjud ba sai a watan Ramadana kaɗai ake yin ta ba.
Ya ce ko da a bayan Ramadan ma ana iya yin ta.
”Sallar tahajjud na nufin sallar da mutum ya yi bayan tashi daga barci cikin dare. Ta fi yin karfi ne a goman karshe na watan azumi saboda a lokacin ne ake samun daren Lailatul-Qadri, daren da ya fi wata dubu,” in ji Malamin.
Ya ce ko da a farkon watan Ramadan ana iya fara sallar tahajjud.’ ‘Idan mutum ya dace da daren Lailatul-Qadri yana tahajjud, za a rubuta masa fiye da shekara 83 yana sallah cikin dare ba ya yankewa,” a cewar Malam.
Raka’a nawa ne ake yi a sallar tahajjud?
“Ita dai sallar tahajjud ba ta wuce akalla raka’a guda biyu. Idan mutum ya ga dama zai yi huɗu ko shida ko hamsin ko ɗari har ma raka’a dubu gwargwadon ikon mutum, a cewar Malamin.
Sheikh Halliru Maraya ya ce mafi ƙarancin ta shi ne raka’a biyu yayin da mafi yawa kuma ba shi da iyaka. Ya ce ko raka’a’ nawa mutum ya yi ya inganta kuma babu wata matsala saboda sallarsa ta yi.
Ko za a iya haɗa tahajjud da tarawi?
Malamin addinin musuluncin ya ce sallar tahajjud daban, sannan ita ma tarawihi daban take.
“Idan mutum ya yi tarawihi ya huta, sannan daga baya ya yi barci, sai ya farka ya yi alwala ya yi raka’a biyu, to ita ake nufi da tahajjud. Dukkansu salloli ne na nafila amma sun kunshi alheri mai yawa wanda Allah ne kaɗai ya san yawansa,” in ji Malam.
Malamin addinin musuluncin ya yi kira ga mutane da su dage wajen ganin sun riƙa yin nafilolin musamman ma a watan Ramadan da muke ciki.
“Idan mutum ya tashi tare da iyalansa cikin dare suka yi raka’a biyu, za a rubuta shi cikin masu ambaton Allah maza da yawa, sannan matansa kuwa a cikin waɗanda ke ambaton Allah a ɓangaren mata da yawa, su ko mata masu ambaton Allah da yawa, Allah ya tanadar musu gafara mai girma,” in ji Malam.
A ina tahajjud ta samo asali?
Fitaccen Malami Dakta Jamilu Yusuf Zarewa, Babban Malami a Cibiyar Nazarin Shari’ar Musulunci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya ce tahajjud ta samo asali ne a zamanin Annabi Muhammad S.A.W, inda ya fito ya yi sallah tare da jama’a a dare na farko da kuma dare na biyu na watan Ramadan.
“Amma a dare na uku ba a ga manzon Allah ya fito ba, ko da aka tambaye shi sai ya ce “baya son ya mayar da ita kamar ta farilla a kan mutane,” in ji Malamin.
Ya ce tun daga nan, ba a sake yin sallar dare a cikin jam’i ba, sai dai kowa ya je ya yi ta a gida.
Ya ce batun sallar tahajjud a gida dai an jima ana yin ta tun farkon musulunci saboda Allah ma Ya ambace ta a cikin Al-Qur’ani mai girma.
Dole ne sai an karanta doguwar sura?
Malam Jamil Zarewa ya ce ba dole ba ne sai mutum ya karanta doguwar sura a sallar tahajjud.
Ya ce Allah S.W.T ya faɗa a cikin Al-Qur’ani mai girma cewa “ku karanta abin da ya sauwaka daga Al-Qur’ani”.
Malamin ya ce duk abin da mutum ko limaman da ke jan jam’i a masallaci za su iya, shi za su karanta.
Shin mata za su iya yin ta a gida ko sai a masallaci?
Malamin addinin musuluncin ya ce abin da aka fi so a wurin mata shi ne su yi sallar a gida saboda hakan ya fi lada.
“Amma idan mace ta ga masallaci zai fi mata wajen yin sallar, to ya halasta ta je masallacin ta yi,” in ji Malamin.
“Manzon Allah S.A.W. ya ce kada ku hana mata musulmai zuwa masallaci, don haka ya halasta idan ta fita taje masallaci domin yin sallah. Amma idan ta yi sallar a gida, to ya fi lada,” in ji Malamin.
BBC HAUSA ✍️