Tarihin Sahabbai

Tarihin Arkam ibn Abi Arqam (RA)



Abu Abd Allāh Arqam ibn ʿAbd Manāf (Da Larabci: أبوعَبْدُ الله أرْقَم بْن عَبْد مَناف ) (d. 55 / 674-5) sahabi ne ga Annabi Muhammad (SAWW). A wata ruwaya, shi ne mutum na bakwai da ya musulunta.

Bayan hijirar Manzon Allah (SAWW) daga Makka zuwa Madina, Annabi (SAWW) Ya kulla zumunci tsakanin Arqam ibn Arqam da Zaid ibn Sahl. Ya halarci yakin Badar, Uhud, da Ghazwas.

Arqam kuma ya ruwaito hadisi daga Annabi Muhammad (SAWW). Ya shahara Saboda gidansa dake gefen tsaunin Safa a Makkah, inda sababbin musulmi suka taru, A lokacin Da Manzon Allah (SAWW) ya gayyaci mutane zuwa ga Musulunci.

Zuri’a

Mahaifiyar Arqam, Umayma, ‘yar Harath ibn Hibala, Yar kabilar Khuza’a ne; da mahaifinsa, Abu l-Arqam, ‘Abd Manaf ibn Asad (Abu Jundab) ibn ‘Abdullahi ibn Amr ibn al-Makhzum dan kabilar Banu Makhzum ne, kabilar kuraishawa. Al-Arqam bn Abil-Arqam RA ya auri Hind bint Abdullah daga kabilar Asad, kuma ‘ya’yansu su ne Umayya da Maryam.

Daga cikin Musulmai na Farko

A wata ruwaya da aka ruwaito daga ‘ya’yan Arqam, Arqam shi ne mutum na bakwai da ya musulunta. Amma Wata bisa ruwayar Ibn Ishaq, Ya ambaci Arqam Ya musulunta bayan mutum takwas da suka musulunta bayan Sayyadina Abubakar (RA).

Arqam ya musulunta tare da Abu Salama, da Abu Ubaida al-Jarrah, da Usman ibn Maz’un.

Arqam ya shahara da kasancewar gidansa a gefen tsaunin Safa a Makka inda Musulmin farko suka taru kuma Annabi Muhammad (SAWW) ya gayyaci wasu zuwa Musulunci. An ce musulmi da dama ne suka musulunta a gidan Arqam.

Halartar Ghazwas

Arqam ya halarci yakin Badar da Uhud tare da sauran Ghazwa . Duk da cewa Manzon Allah (SAWW) ya ce wa musulmi su mayar da ganimar da suka tara a yakin Badar, amma ya baiwa Arqam takobi mai daraja. Arqam kuma ya halarci Sariyya da Abu Salama da ‘Abdullahi ibn ‘Abd al-Asad a cikin Watan Muharram, 3/Yuni-Yuli, 624.

A Madina

Bayan Hijirar Annabi (SAWW) daga Makka zuwa Madina, Manzon Allah (SAWW) ya kulla alaka ta ‘yan uwantaka tsakanin Arqam da Abu Talha Zaid ibn Sahl. Arqam ya zauna a yankin Banu Zariq a Madina a wani gida da Manzon Allah (SAWW) ya ba shi. Ya ruwaito hadisai daga Annabi Muhammad (SAWW).

Mutuwa

Arqam yana daga cikin sahabban Manzon Allah (SAWW) da suka halarci yakin Badar, wanda ya rasu yana da shekaru 80 a Madina ; lokacin da Mu’awiya yake mulki. Wasu majiyoyi sun ce ranar wafatin Arqam da Sayyadina Abubakar (RA) rana guda ce. Sa’ad ibn Abi Waqqas ne yayi masa Sallar Jana’iza.

Gidan Arkam

Gidan Arqam a Makka ya shahara yayin da Manzon Allah (SAWW) ya gayyaci mutane zuwa Musulunci a can, zuriyar Arqam ne ke tafiyar da shi har zuwa lokacin Abu Ja’afar al-Mansur.

Al-Arqam bn Abil-Arqam RA ya yi wasici ga dansa cewa gidansa kada a sayar. Sai dai kuma a zamanin Abu Jaafar al-Mansur, daya daga cikin jikokin Al-Arqam yayi Rarrashin ya sayar da kasonsa na gidan a kan dinari 17,000 domin a sake shi daga kurkuku; sannan kuma aka bai wa ‘yan uwansa damar sayar da nasu kason.

Yanzu ana kiran wannan gida da Daru’l-Khayzuran Yana daura da dakin Ka’aba kuma ana amfani da shi a matsayin makarantar addini a yau.

See also  Tarihin Sahabi Suraqa ibn Malik (RA)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button