Tech

YADDA ZAKA IYA JUYA KATIN DAKE LAYIN WAYARKA ZUWA KUDI

Sau da yawa mutane suna samun kyautar katin waya daga wajen abokai ko ‘yan’uwa amma sai suyi ta faman neman wanda zai siya amma su rasa.

Wasu kuma suna samun katin waya ne ta hanyar amfani da wasu manhajoji na waya (phone application) irinsu (Share it) (JumiaPay) da sauransu, wa’danda suke bada kyautar katin waya idan aka saukesu akan waya (install) ko kuma idan anyi wani aiki da sukace ayi (task), amma sai su gaza samun mai siyan katin a cikin sauƙi.

Sannan kuma mafi yawan hanyoyin da ake mayar da katin waya zuwa ku’di anayin transfer ‘dinshi ne kafin kuma ka jira a saka maka shi a cikin asusunka (wallet), wani lokaci yakan dauki tsawon lokaci kafin ku’din su shigo maka kamar yadda (DataWay) sukeyi, kuma sai wanda yake da register dasu yake samun damar yin hakan ma.

To ita wannan hanyar da zan nuna maku duk ba haka take ba, tana da sauki kuma kai tsaye ku’dinka zasu shigo cikin asusun bankin ka.

Da farko dai zaka je cikin playstore ‘dinka kayi download na wannan manhajar (app) mai suna “TINGTEL AIRTIME”.

Bayan ka saukeshi akan wayar sai ka bu’deshi, kafin ka fara komai sai ka tabbata kasan lamabar sirrinka ta transfer a layinka wanda kake da ku’din a ciki, kuma ka tabbata yana akan saman wayar da ka sauke manhajar (app) ‘din.

MTN suna saita lambar sirrin transfer ne kamar haka: idan baka ta6a yiba zaka danna *600 * 0000 * sabon lambar da kakeso * sai ka ƙara maimata ita lambar da ka za6a ‘din #, sai ka danna wajen kira.

See also  Menene Artificial Intelligence?

Su kuma Airtel zaka iya shiga ta cikin saitin “Sim Tookit” saika saita shi.

Hanyoyin da zaka bi wajen saita manhajarka na “TINGTEL” sune:

Gida na farko idan ka shiga zasu tambayeka yare, wanda zaka barshi akan “English” sai ka danna “continue”

Gida na biyu shine wajen da zasu tambayeka..
First name, last name sai username daga nan sai “promotion code” shi kuma za6i ne, zaka iya barinshi karka saka komai, daga nan sai ka danna “signup”

Gida na gaba kuma zasu ce maka ka saka “code” guda hudu na sirri wanda zaka kiyaye account ‘dinka dashi, idan ka danna “set passcode” zasu ce ka kara danna su lambobin da ka saka a baya, sai ka kara danna su, wato kayi “verify” kenan.

Gida na gaba shine wanda zakayi register na layin da zaka dunga tura ku’di dashi zuwa asusunka na banki “bank account”, zasu tambayeka kasa lambar layinka na gidan sim na farko (sim one) bayan ka gama idan kana buƙatar kayi ma layinka na biyu shima zaka iya, idan kaso kuma zaka iya wucewa gaba idan ka danna “skip”, zasu turo maka wasu lambobi a layinka wanda kayi ma register da app ‘din, idan ka saka lambobin shike nan ka gama.

Bayan ka gama komai zai bude maka wasu za6uka (options) anan kuma sai kaje wajen “airtime sell” idan ya wuce zai nuna maka wani waje da aka rubuta “credit to” ananne zaka saka lambar bankin da kakeso ka tura ku’din naka, sannan kuma sunan bankin, daga nan su da kansu zasu bayyana maka sunan mai asusun bankin da kasa lambar bankin, sai ka danna “next”.

See also  Maganin Barayin Waya, Da Masu Cire Maka Caji Su Saka Tasu Wayar Baka Sani Ba

Idan layukan da suke cikin wayarka biyu ne, sai ka za6i wanda ku’din suke ciki zaka tura, bayan ka za6a sai ka saka adadin ku’din katin da kakeson su tura maka a matsayin ku’di cikin bankin ka, ananma zasu nuna maka iya ku’din da su kuma zasu chajeka a matsayin aikin da za suyi maka, nan ma bayan ka gani idan ka amince sai ka danna wajen da aka rubuta “transfer”.

Daga ƙarshe zasu tambayeka “pin” wanda shine kadai abunda ya rage maka, wannan shine “pin” naka na layinka wanda kake transfer dashi, da zaran ka saka shi kuma sai ka sake danna inda aka rubuta “transfer” shikenan zaka ji ku’dinka sun sauka cikin asusun bankinka.
Masha Allah.

✍???? Abu Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button