Tambayoyi a Musulunci

MATSAYAR MAGABATA GAME DA YAZIDU D’AN MU’AWIYYA !



Tambaya
Assalamu Alaikum
Dan Allah abani Amsar wannan tambayar:
Yazeedu d’an Mu’awiya ya matsayinsa yake a musulunci ?
Daga mai bibiyarku Masoyinku daga Nijar. Bis salam sai na ji ku.

Amsa
Wa alaikum assalam wa rahmatullhi
Yazidu D’an Muawiyya an haife shi ne a zamanin sayyadina Usman, don haka ba ya cikin sahabbai wadanda Allah ya tabbatar da adalcinsu.

Magabata nagari ba sa yabon Yazidu ba Kuma sa zaginsa.
Abin da yasa ba sa yabonsa saboda shekaru uku da watanni ya Yi Yana Mulki, a shekarar farko aka kashe Hussain jIkan Manzon Allah, duk da cewa ba shi ya Yi umarni a kashe shi ba, a ta biyu kuma aka jefi Ka’aba har sai da wani bangare ya Kone, ya karkare mulkinsa da yakar mutanen Madina, an kashe sahabbai da yawa a cikin yakin.

Abin da yasa ba sa zaginsa shi ne saboda fadin Annabi SAW: “Farkon rundunar da za ta yaki Kusd’and’aniyya an gafarta mata”, Bukhari ya rawaito wannan hadisin a sahihinsa, Kuma shi Yazidu Yana cikin wannan runduna, wannan yasa malaman suka tsaya cak akan lamuransa, suka fawwala su zuwa ga Allah, shi zai Yi hukuncin da yaga dama da shi .

A takaice dai Yazidu yana da kurakurai wadanda suka hada da kashe mutanen Madina da kuma shan giya a wajan wasu maruwaitan, sannan Yana da kyawawan ayyuka Kamar yakar Birnin Sarki Kaisar, Wanda hadisi ya tabbatar da gafara ga rudunar da yake ciki, wannan yasa tsunduma shi a wuta kacokan yake da wahala.

Don neman Karin bayani duba Majmu’ul fatawa 4/481 da Kuma Siyaru a’alamin nubala’i 4/38.

Allah ne mafi sani

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

27/12/2021

See also  MAGANIN DAMUWA DA BAKIN CIKI !

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button