Tarihin Annabi Isma'el (AS)

Tarihin Annabi Isma’el (AS) Kashi Na (1)



ʾIsma’īl (AS) ko kuma Isma’ila (Da Larabci: إسماعيل ), Ɗan Annabi Ibrahim (AS) ne da aka san shi a tsakanin musulmi da laƙabin Dabih (Sadaukarwa). A bisa hadisan Musulunci, zuriyar Annabi Isma’il (AS) Ta Kai Ga Annabi Muhammad (SAWW)

Hijira zuwa Makka tare da Mahaifiyarsa Hajar, bullar Ruwan Zamzam a matsayin falala saboda shi, Allah ya umarci Da Annabi Ibrahim (AS) Da Yayi Layya Da Dansa Annabi Ismã’ĩla (AS) da gina Ka’aba na daga cikin muhimman al’amura a rayuwarsa.

A cikin Alkur’ani mai girma ana kiran Isma’il (daya daga cikin manyan annabawan Allah da suka rayu a Hijaz) a cikin Alkur’ani mai girma, Annabi Isma’il (AS) shi ne dan fari Ga Annabi Ibrahim (AS) kuma manzo, Annabi kuma wanda ya kafa Isma’ilawa a Musulunci.

Wanene Annabi Isma’il (AS)?

Annabi Ismail (AS) dan Annabi Ibrahim (AS) ne dan Hajar (RA). A Musulunci ana daukar Annabi Isma’il (AS) a matsayin kakan Annabi Muhammadu (SAW) Ba wai kawai a cikin Alqur’ani mai girma ba ne aka ambaci labarin rayuwar Annabi Isma’il (AS) a cikin littattafan addini na Kiristanci da Yahudanci ma Akwai Ambatonsa.

Duk da cewa rayuwar Annabi Isma’il (AS) ta cika da wahalhalu, amma ya kasance mai bautar Allah SWT na gaskiya kuma dan Annabi Ibrahim (AS) mai kaunarsa. Ko dan ya yarda ya sadaukar da kansa ga Allah SWT ko kuma kasancewarsa a wajen Taimakawa mahaifinsa a lokacin gina Ka’aba mai tsarki, Annabi Isma’il (AS) abin Koyi ne ga daukacin musulmi a yau da kuma na zamanai masu zuwa.

Wane Abu Ne Na Musamman Game Da Annabi Isma’il (AS)?

Annabi Isma’il (AS) shi ne Ya raya Ka’aba mai tsarki kuma Uban Larabawa. Annabi Isma’il (AS) tun yana karami ya sadaukar da rayuwarsa wajen wa’azin Musulunci da kuma cika dokokin Allah SWT.

Daga kasancewarsa shi kadai a cikin sahara tare da Hajar (RA) a lokacin da Annabi Isma’il (AS) yake jariri, da barin mahaifinsa (Annabi Ibrahim (AS) ya yanka shi saboda Allah SWT, har ya zuwa tayar da harsashin Ginin Ka’aba mai tsarki, Annabi Isma’il (AS) ya tabbata a matsayin manzon Musulunci mai kwazo sau da yawa.

Annabi Isma’il (AS) ya rayu a Makka tsawon rayuwarsa. Wata Rana Annabi Ibrahim (AS) ya zo wajensa ya ce masa: “Ya Isma’ila, Allah SWT ya ba ni umarni.

Annabi Isma’il (AS) ya ce: “Ku aikata abin da Ubangijinku Ya umarce ku da ku Aikata.” Da jin haka, mahaifinsa ya ce, “Za ka taimake ni?” Sai Annabi Isma’il (AS) ya ce, “Ni zan taimake ka.” Kawai sai Annabi Ibrahim (AS) ya yi nuni da wani tsauni da ya ke kewaye da Su, ya ce, “Allah SWT ya umarce ni da in gina gida a nan.

Uba da dansa su biyu sai suka tayar da harsashin Ka’aba mai tsarki. A duk lokacin da ake aikin ginin, Annabi Isma’il (AS) ne ya dauki nauyin kawo duwatsun Gini, yayin da Annabi Ibrahim (AS) yake dora su a kan juna. Kamar yadda ruwayoyi suka nuna, Annabi Isma’il (AS) ne ya kawo dutse Mai Tsarki da aka ajiye a (Maqam-ibrahim).

Da yake bayar da labarin wannan lamari, Allah SWT a cikin Alkur’ani mai girma ya ce, kuma a tuna lokacin da Ibrahim ya tayar da harsashin ginin dakin tare da Isma’ila, dukkansu suna addu’a, “Ya Ubangijinmu! Ka Karbi wannan daga gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani.”

Manzon Allah (SAWW) ya ce, “Sai su biyun suka yi ta gini suna zagaya dakin Ka’abah, suna cewa: “Ya Ubangijinmu! Ka karɓi wannan hidima daga gare mu, lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani.” (Sahihul Bukhari)

Al’ummar musulmi suna bin koyarwar Annabi Muhammad (SAWW) wanda shi zuriyar Annabi Isma’il (AS), dan Annabi Ibrahim (AS) Ne. Allah SWT ya ambaci sunan Annabi Isma’il (AS) sau goma sha daya a cikin Alqur’ani mai girma, ya kuma saka masa suna “Dhabihullah” ma’ana wanda Allah ya yanka.

A cikin Alkur’ani sura ta 21:85, An Ambaci Annabi Isma’il (AS) tare da Annabawa, Idris (AS) (Enuhu) Da Dhul-kifli (AS) daga cikin masu hakuri, wasu masu tafsiri sun ambaci biyayyarsa wajen shimfida kansa kasa don sadaukarwa A Matsayin alamar hakurinsa.

Isma’il (AS), Sadiq Al-Wa’d

Wasu malaman tafsiri sun Bayyana Annabi Isma’il (AS), Da Sadiq Al-Wa’d (wanda ya kasance mai gaskiya a cikin Alkawuransa) Kuma sun ambaci wasu labarai Akan Cika Alkawuransa.

Mu’ujizar Annabi Isma’il (AS)

Rayuwar Annabi Isma’il (AS) cike take da mu’ujizai. Wasu daga cikinsu an jera su Kasa.

Zamu Ci Gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button