Tarihi

Gwamna Zabiya Na Farko A Tarihin Najeriya



Mr. Umo Eno, zababben gwamnan jihar Akwa Ibom, A Jam’iyar PDP shi ne gwamnan zabiya na farko, ba a Najeriya kadai ba, Harma A Afirka.

Umo Bassey Eno Wanda Aka haife shi A Ranar 24 ga Afrilu, 1964 limamin Cocin Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda shi ne zababben gwamnan jihar Akwa Ibom mai Jiran Rantsuwa, Kuma Shi ne tsohon kwamishinan filaye da albarkatun ruwa a jihar Akwa Ibom, kuma wanda ya kafa All Nations Christian Ministry International.

An haifi Umo Eno a ranar 24 ga Afrilu 1964 Yanzu Yana Da Shekaru (59) A Ikot Ekpene Udo a karamar hukumar Nsit-Ubium ta jihar Akwa Ibom.

Ya halarci makarantar firamare ta karamar hukuma a jihar Legas, inda ya samu takardar shaidar kammala makaranta.

Ya kuma halarci Karamar makarantar sakandare ta St. Francis da ke Eket, Jihar Akwa Ibom da sakandaren Victory High School A Ikeja, Jihar Legas don karatunsa Na Babbar Sakandire.

Ya samu digirin farko a fannin harkokin gwamnati a jami’ar Uyo , sannan ya yi digiri na biyu a wannan fanni.

Bayan kammala karatunsa na Sakandare, ya yi aiki a bankin Union na wasu shekaru kafin ya koma Bertola Machine Tools Nigeria Limited sannan Daga Baya ya koma Norman Holdings Limited, inda ya zama babban jami’in gudanarwa kafin ya kafa Royalty groups, wanda nasa ne.

A shekarar 2021, Gwamna Udom Emmanuel ya nada shi kwamishinan filaye da albarkatun ruwa a jihar Akwa Ibom, daga baya kuma ya yi murabus daga mukaminsa Don tsayawa takarar gwamna.

See also  TARIHIN SAYYADINA UMAR ƊAN KHAƊƊABI RALIYALLAHU ANHU (KASHI NA DAYA)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button