Addu'o'i

KARANTA ADDU’A YAYIN SADUWA DA IYALIManzon Allah SAW ya ce;”Da dai dayanku zai ce yayin da zai sadu da iyalinsa;

بسم الله ، اللهم جنبنا الشيطان وجنب الشيطان ما رزقتنا

Bismillaah. Allaahumma jannibnash-Shaytaana, wa jannibish-Shaytaana maa razaqtanaa

Ma’ana: (Ina Mai farawa da sunan Allah, ya Allah ka nisantar da shaidan daga garemu, ka kuma nisantar dashi daga abunda zaka azurtamu)

Idan Allah ya kaddara samuwar yaro awannan saduwar to shaidan bazai taba iya cutar dashi ba”.

Shaykh Uthaymeen (Rahimahullah) yake cewa akarkashin wannan hadisin “lalle wannan addu’ar mutum zai fad’e ta ne aduk lokacin da zai kusanci iyalinsa ne, adaren farkone ko kuma waninsa, kuma wannan addu’ar tana daga cikin sabubba da suke hana shaidan cutar da yaro” .

نور على الدرب /الشريط٧٧/النكاح والطلاق

See also  Karanta Addu’a Yayin Cire Tufafi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button