Tambayoyi a Musulunci

SHIN ALLAH YANA YIN ABUBUWA DA HIKIMA ?



Wannan mas’alar tana daga cikin mas’aloli masu wuyar gaske. Ana iya taƙaita maganganun mutane a wannan mas’alar zuwa maganganu guda biyu:

1. Duk abin da Allah zai yi, yana yinsa ne da hikima da kuma manufofi na musamman. Wannan shine ra’ayin mafi yawan mutane daga cikin
Ahlussunnah da Mu’utazilah da Falāsifah.
2. Ayyukan Allah da hukunce-hukuncenSa ba su da sababi ko manufa; in yayi niyyar abu kawai yana yi ne. Wannan ita ce maganar Zahiriyya da kuma da yawa daga cikin Asha’irah da ƴan Shi’a.

Masu mazhabar farko sun kafa hujja da cewa: Allah ya siffanta kansa da mai hikima a wurare mabanbanta a cikin Al’Qur-ani, sannan idan yayi abu, yakan faɗi hikimar da tasa yayi, har aiko Manzanni da halittar mutum da Aljan sai da ya faɗi hikimar hakan, ta yadda yayi bayanin cewa ya aiko Manzanni ne saboda kafa hujja.
Sannan yana daga cikin abin da masu hankali suka cimma daidaito akai: duk mutumin da zai yi abu da dalili ya fi wanda zai yi ba dalili, duk abin da yake kamala ne ga ɗan Adam ta kowace fuska, to Allah ne yafi cancanta ya siffantu da shi.

Masu ƙauli na biyu sun kafa hujja da faɗin Allah Madaukaki a cikin Suratul Anbiya’i, aya ta 23: “Ba’a tambayarSa game da abin da yake aikatawa su kuma ana tambayar su”. Suke cewa duk wanda ba’a tambayar shi in yayi abu, to zai iya yi da manufa ko ba da ita ba.
Sannan suka ce akwai abubuwa da yawa waɗanda Allah yayi su babu hikima a ciki, kamar halittar Shaiɗan da kuma sanyawa yara masassara.

Zance mafi inganci shine na farko, saboda a cikin Al’Qur-ani akwai dalilai sama da guda dubu waɗanda suke nuna cewa Allah yana yin abu da hikima. Haka nan Annabi (S.A.W.) ya yi bayanin hikimomin mas’aloli masu tarin yawa

Daga cikin hikimomin halittar Shaiɗan akwai samun ladan neman tsari da shi, ana sanyawa yara masassara saboda su shirya ɗaukar wahalhalun rayuwa da na addini a can gaba.

Tsakire daga littafin Manufofin Sharia na Dr. Jamilu Zarewa

See also  ZAN IYA AURAN WACCE KISHIYAR MAMANA TA SHAYAR ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button