University

Cikakken Bayani Gameda Inter Faculty Transfer (IFT)

• Me ake nufi da Inter Faculty Transfer ?

• Yaya akeyin Transfer din ?

• Kowace Jami’a tana yi ?

• Menene requirements din ?

Inter Faculty Transfer wani tsari ne da yake bawa dalibi damar canja tsangayar da yake karatu zuwa wata ta daban amma a cikin Jami’ar da yake karatun.

Akwai dalilai da dama da sukan iya haddasa yin Transfer din wanda suka hada da rashin gane karatu a wannan tsangayar (Academic Performance) kokuma ba zaka iya biyan kudin karatu a wannan tsangayar ba, ko makamancin haka, to idan ya zama haka ne zaka iya yin transfer kaje inda kake ganin zaka iya.

• Yaya ake yin Transfer din ?



1• Da farko zaka rubuta letter zuwa ga Rajistara na Neman yin Transfer din amma ta hannun Department dinka zaka Rubuta letter din, (Saboda haka abinda yafi shine ka samu level Coordinator/Program Coordinator dinka kayi masa bayani to shi zaiyi guiding dinka kawai)

2• Daganan su Kuma Academic Division zasu baka Form na transfer din saika cika, kudin sa yakan kai kusan dubu goma (N10,000)

3• Idan ka cika sai ka kaima Shugaban Department dinka form din (HOD)shine zai Cigaba da processdin

4• Sannan form na transfer din ana fara bayar dashi ne a Second Semester, ana rufewa Kuma a ranar da aka gama Jarabawar ta Second Semester.

5• A karshe, za’a sanar maka idan an karbi transfer din naka ko ba’a karba ba

6• Ba’a yarda kowanne Faculty (Tsangaya) ba ya bada transfer ga kashi 5% na daliban dake tsangayar

7• Sannan ba’a yin transfer din sau biyu. Idan kayi transfer sannan kuma kaga can din ma bai maka ba to shikenan saidai ka hakura kayi a hakan kokuma kabar Jami’ar.

8• Dole Sai an baka Official Letter daga Registrar shaidar cewa an yimaka transfer din.
See also  Cikakken Bayani Gameda Intra Department Transfer (IDT)

• Kowace Jami’a tana yi?


Ehh, kowace Jami’a tana yi saidai tsarin wannan Jami’ar ya bambanta Dana wannan ne amma duka sunayi.

•Menene requirements din ?


Akwai requirements da dama kusan duka daya ne inda suke da bambanci shine wajen CGPA, ga wasu daga cikin requirements din:

1• Dole ya zama SSCE dinka Jamb dinka Faculty dinka Department dinka su zama sunada alaka da inda kake so ka koma (Ba zai yuwu Kana Sociology ka koma Cyber Security ba)

2• Dole sai ya zama Carryover dinka basu wuce 2 ba

3• Dole sai idan kai dan aji biyu ne (Level 200)

4• Kar CGPA dinka yayi kasa da 1.00 .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button