University

Cikakken Bayani Gameda Inter-University Transfer (IUT)

• Me ake nufi da Inter-University Transfer (IUT)

•Kowace Jami’a ne take karbar Transfer din ?

• Yaya ake yin Transfer din ?

• Menene requirements ?

•Me ake nufi da Interuniversity transfer (IUT) ?

Interuniversity transfer wani sabon tsari ne da Jami’o’in Nigeria suka bullo dashi, wanda bai zama gama gari ba, Jami’o’i kalilan ne suka dauki wannan tsari.

Inter university transfer wani hanya ne da yake baiwa dalibi damar canja makarantar da yake karatun degree zuwa wata Makarantar ta daban dan Cigaba da karatun shi sakamakon wasu dalilai.
Kamar Misali: Mutum yana Karatu a Yusuf Maitama Sule University sai yayi Transfer ya koma Bayero University, Kano.

• Kowace Jami’a ne take karbar Transfer din ?

A’a ba kowace Jami’a bane take karba sakamakon wannan wani sabon tsari ne da ba kowace Jami’ar bane tayi adopting dinshi.

Ga Sunayen wasu daga cikin Jami’o’in da suke karba:

1• University Of Ibadan (UI)

2• Obafemi Awolawo University, Ile-ife (OAU)

3• Kaduna State University (KASU)

4• Federal University Of Technology, Akure (FUTA)

5• University Of Ilorin (UNILORIN)

6• University Of Nigeria, NSUKKA (UN)

7• Ladoke Akintola University Of
Technology, Ogbmoso (LAUTECH)

8• Osun State University (UNIOSUN )

9• University Of Abuja (UniAbuja)

10• Ahmadu Bello University (ABU ZARIA)

11• University Of Lagos (UNILAG)

12• Umaru Musa Yar’Adua University (UMYU)

13• Bayero University, Kano

14• Mafi yawan cin Private Universities (Jami’o’i Masu zaman Kansu)

• Yaya ake yin Transfer din ?

Akwai abubuwa Kamar guda uku da ya kamata kayi dan yin wannan transfer din, gasu Kamar haka:


1• Katattauna da Admission Officer na Jami’ar da kake so ka koma, domin ka samu tabbaci akan shin idan ka baro taka University din to su zasu amshe ka ? Idan sun tabbatar maka zasu amsheka sai ka tafi mataki na biyu, Shine:

2• Ka tattauna da admission officer din Jami’ar da kake karatu a wannan Lokacin dan kaji shin su zasu yarda su baka transfer din, domin kuwa idan basu gamsu da dalilan ka nayin transfer din ba zasu iya hana ka

3• Daganan kuma sai ka karbi form na transfer din ka cika anan Makarantar da zaka bari, sannan kuma ka cika na Makarantar da zaka koma.

Idan baka tabbatar da yarjejeniya tsakanin wadannan makarantun ba (Wacce zaka bari da wacce zaka koma) to zaka iya yin biyu babu.
See also  Cikakken Bayani Gameda Inter Faculty Transfer (IFT)

•Menene Requirements?

Kusan duka requirements din iri daya ne, in banda wurin CGPA kawai.


1• Ana bukatar transcript dinka

2• Sannan ya zama Course dinda ka baro a can anan ma shi zaka karanta. (Duk da zaka iya canjawa, amma idan kanada requirements na inda kake son canjawa din)

3• Ka tabbatar maki dinka na Jamb yakai adadin maki dinda Makarantar take bukata, sannan ka tabbatar maki din kuma yakai adadin wanda Department din suke bukata.

4• Sannan idan Makarantar ta amshe ka to aji biyu zata sanya ka, koda kuwa

5• Sannan dole ya zama kana Level 2 ne, idan ka kai level 3 to transfer din ba zai yuwu ba (Amma sai idan Course din naka mai Shekara 4 ne)

6• Zaka iya yin transfer din koda kana aji uku ne Level 3, idan course dinka mai Shekara 5 ko 6 ne.

Amma dai Mafi kyau shine ka tuntubi hukumar gudanarwa ta Jami’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button