Tech

YADDA ZAKU YI DOWNLOAD NA VIDEOS DIN PINTEREST DA WAYARKU

Yan’uwa idan baku san App na pinterest ba ya kamata ku sani, dan ina da tabbas a ko wane irin field kake Pinterest App zai baka gudunmuwa, imma kai mai sana’a ne ko ‘dalibi ko manomi ko makiyayi ne kai.

Indai kana da sha’awar koyon ilimi a online koma wane iri ne, to ya zamar maka dole kasan wannan application din na pinterest, dan duk wata sana’a da akeyi wadda ta shafi ƙirƙira ta fasaha dole zaka samu video na yadda ake yinta a cikin pinterest.

Ba’a iya koyan sana’a bidiyoyin pinterest suka tsaya ba, hatta koyan ilimin kula da lafiyar jikinka dana dabbobin da kake kiyo, da ilimin addinai dana tsirrai da sauransu.

A cikin pinterest akwai hanyar da ake bi ana samun kudi da ita wajen tallata hajar wasu ko saka videos da pictures da mutane suke buƙata na nishadi ko na design ko wasu ayyukan da zasu taimaki wasu wajen samun idea ko motivation. (Nan gaba kadan in sha Allah zanyi bayanin yadda ake samun kudi da pinterest)

Mun dai gane pinterest yana da amfani matuƙa a gare mu haka ma videos da suke a cikinshi, dan haka ga hanyar da ake bi wajen yin download nasu:

1- Bayan ka shiga cikin pinterest ka hau kan video dinda kake san kayi download ka bude ta, daga sama za kaga wasu 3dots sai ka shiga wajen.

2- A cikin 3dots din idan ya bude wasu za6uka zasu fito maka sai ka ta6a wajen copy link dan yayi copy.

3- Daga nan sai ka tafi cikin browser dinka ta waya kamar chrome browser sai ka rubuta Pinterest Video Downloader, sai ka danna search.

See also  Yadda ake tura Hoto, Video, Waƙa ko kuma wani file a matsayin document ta whatsapp

4- Idan ya bude daga farko zaka ga inda aka sake rubuta maka Pinterest Video Downloader da blue din rubutu sai ka shiga wajen.

5- Anan kuma zaka ga wani box da babu rubutu a ciki, daga ƙasanshi kuma an rubuta download, to sai kayi paste na link dinda kayi copy na video daga pinterest a wajen kafin nan sai ka danna wajen da aka rubuta download din.

6- Daga nan za kaga video din ya bude har zai baka damar da zaka iya kallo, a gefen dama na video din daga ƙasa za kaga wasu 3dots, sai ka danna su.

7- Bayan ka danna 3dots din zaka ga rubutu ya fito a wajen an rubuta download, sai ka danna.

8- Zasu baka za6i na download da kuma za6ar inda kake san video din ya tafi (Download Location) sai ka danna download din shike nan.

Allah ya taimaka.

© Abu Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button