BSC. PHYSICS; ilimin Kimiyyar Ƙwayoyin Halitta Da Makamashi
BSC. PHYSICS; ilimin Kimiyyar Ƙwayoyin Halitta Da Makamashi..
‘Arewa Students Orientation Forum’
Physics Duniyar Science..
Babu ko Tantama kan Zamowar ilimin Physics Uba ga duniyar Science Dan haka nema Ɗaliban BSC. PHYSIC Kan zamowa na musamman kuma zaƙaƙurai a fannonin Kimiyya , Bsc. Physics maɓuɓɓuga ne ga dukkan Wani Nau’in Ƙere-ƙere a duniya Da Samar da ababen rayuwa na zamani shekaru aru-aru.
Bsc. Physics Kimiyyar ƙwayoyin halitta da makamashi da kuma mu’amalar da ke tsakanin su biyun, an rarrabe zuwa traditional Field (fannonin Physics na gargajiya) kamar su acoustics, optics, mechanic, thermodynamics, da electromagnetism, haka nan kuma akwai ɓangaren modern Physics (na zamani) da suka haɗa da atomic da nukiliya physics, da cryogenics, solid-state physics, particle physics, da kuma plasma physics dasauransu.
Kimiyyar Physics kimiyya ce da ke da alaƙa da Properties, canje-canje, hulɗa, da dai sauransu na Ƙwayoyin halitta da makamashi wanda ake ɗaukar makamashi a matsayin ci gaba (classical physics), ciki har da wutar lantarki, zafi, na’urorin gani, makanikai, da dai sauransu, kuma yana hulɗa da ma’aunin atomic na yanayi wanda a cikinsa ake ɗaukar makamashi a matsayin mai discrete (Ƙwayoyin kimiyyar lissafi), gami da irin waɗannan rassa kamar su atomic, nuclear, da sulfur-state physics ka iya zamowa Gagara badau da sai dai ace mutum yayi iyakar iyawar sa.
a fannonin da suka haɗa da injiniyoyi, acoustics, optics, zafi, wutar lantarki, magnetism, radiation, da kimiyyar atomic da nukiliya Physics shine kimiyyar yadda abubuwa ke aiki da wanzuwa a duniya da tsarawa da sarrafa yadda za’a ci moriya da ƙirƙire-ƙirƙiren zamani dana da can baya
Bsc. Physics shine kimiyyar daɓi’a da ke nazarin ƙwayoyin halitta, ainihin abubuwan da ke tattare da su, motsinsu da halayensu da sararin samaniya da lokaci, da abubuwan da suka danganci makamashi da kuzarin Motsawa, Physics yana ɗaya daga cikin mafi mahimmancin ilimin kimiyya, tare da babban burinsa shine fahimtar yadda duniyar Kaunu ke wanzuwa.
Ga Jerin Wasu Daga Cikin Courses Ɗin da’akeyi a Physics:
1st Semester Level One:
Mechanics
Electricity And Magnesium
Physic Practical 1
Elementary Mathematics ¡
Elementary Mathematics ¡¡
Introduction to Computer science
Organic chemistry
2nd
Behaviour Of Matter
Physic Practical 1
Probability 1
Elementary Mathematics 3
Physical Chemistry
Practical Chemistry
200 level 1st
Renewable Energy
Physic Practical
Electric Circuits and Electronics
Elementary Modern Physic
Mathematical Method
2nd
Electronic Practical
Waves and optics
Thermal Physic
Elementary Differential Equation
Probability 3
300 level 1st
Vector And tensors
Solid State Physics
Energy and Environment
Physics and Electronic laboratory
Complex analysis
Analytical Mechanic 1
Quantum Physics
Electricity And Magnetism
Design Studies
Introduction to acoustics
Introduction to geophysics
Semiconductor device
Electronic circuits
Siwes
Level 400:
Quantum Mechanics 1
Mathematical Methods in Physics1
Computational Physics
Statistical and thermal Physics
Electromagnetic Waves
Analytical Mechanic 2
Dss.
(a Lura cewa Courses suna iya sauyawa Daga Makaranta zuwa makaranta, kuma wannan mun tsakuro kaɗan ne)
Wasu Kaɗan Daga cikin Branch Na Physics:
Classical Physics
Modern Physics
Nuclear Physics
Atomic Physics
Geophysics
Biophysics
Mechanics
Acoustics
Optics
Thermodynamics
Astrophysics
Wasu Kaɗan Daga cikin Ɓangarorin Da za’a iya cigaba da karatu bayan Bsc. Physics
MBA in Data Science
MBA in Information Technology
MSc in Materials Science and Engineering
M. Sc Vacuum Sciences
M. Sc Acoustics
MSc in Applied Physics
MSc in Physics
M. Sc Applied Electronics
MSc in Atmospheric Science
MSc in Nanotechnology
MSc in Astronomy/Planetary Science/Astrophysics
MSc in Aeronautics
Master in Atomic and Molecular Physics
MSc in Particle/Nuclear Physics
MSc in Geophysics
MSc in Molecular Physics
MSc in Optical Physics
MSc in Medical Physics
MSc in Biophysics
Wasu Daga cikin Short-term Courses/ Training Bayan BSc Physics:
PG Diploma in Data Science
PG Diploma in Astronomy
PG Diploma in Nanotechnology
Diploma in Medical Lab Technology
PG Diploma in Community Health Nursing
Certificate in Lab Assistant/Technician
Diploma in Operation Theatre Technology (OTT)
PG Diploma in Machine Learning/Artificial Intelligence.
•Shin BSc Physics Yanada tasiri a wannan zamanin?
A wannan zamanin, ana amfani da Physics a kowane fanni na rayuwa, Bayan kammala wannan kwas, ɗalibai suna da damar aiki daban-daban ga kaɗan Daga Ciki:
Petroleum and gas
Science
Engineering
Business and finance
Technology
Construction
Physicist
Physics Lecture
Lab Assistant
Research Associate
Subject Matter Expert
Technician
Radiologist Assistant
Quality control manager
Research associate
Statistician
technician
academic counselor
Dss.
©ASOF-2023
Whatsapp 08086251045