Education

Ranar mathematics ta duniya mun tuna muku da bayanin mu a kan ilimin Maths

Ranar mathematics ta duniya mun tuna muku da bayanin mu akan Ilimin Maths..

Karatun Ilimin Kimiyyar Lissafi a Nigeria
(Bsc. Mathematics)

(Ƙashin Bayan ilimin Kimiyya Da Fasaha)

Ilimin Lissafi ya ƙunshi jigogi da yawa; Don haka, zaku iya zaɓar kowane babban jigo kamar statistics, operation Management, accountancy, actuarial sciences,
Dasauran Ɓangarori Masu yawa.

Kasancewa daliɓin Lissafi, zaku iya yin aiki a Data Analysis wanda a halin yanzu ake buƙatar fannin sosai.

Ilimin Lissafi yana ba da damammaki da yawa a kusan dukkan fannoni komai saida Ma’auni Dakuma lissafi.

Ilimin lissafi batu ne da ɗalibai suka daɗe suna tsoronsa a ko’ina a faɗin duniya, ƙaruwar guraben ayyukan yi ga waɗanda suka kammala karatun ilimin lissafi, yasa ansamu ƙarin ɗalibai Masu zaɓin yin BSc Maths; babban zaɓi ne na aiki, kuma ba shi da iyaka, Idan kai mutum ne mai son warware daidaito da matsaloli, to BSc. Mathematics shine zaɓinka!

Idan Ilimin Kimiyyar Lissafi Yanada wahala Abun tambayar Shine shin amfanin ilimin Kaɗan Ne?

Wataƙila SBD Muhimmancin sa dakuma tsadar zata iya sawa yayi wahala Kamar yanda muka Sani a kasuwa Duk Mai amfani dayawa yana tsada; tayuwu ilimin lissafi yana biyan tsadar sa ne dawuya kasancewar sa ilimin da Babu Abunda baya shiga cikin sa, da ilimin lissafi za’a iya warware kowacce Irin Ta ƙaddama da matsala.

Kamar kowane fanni, BSc. Mathematics yana buƙatar Jajircewa da aiki tuƙuru, Ko da yaushe an san ilimin lissafi abu ne mai wayo, wanda ya sa ɗalibai da yawa kuka, Duk da haka, ba duka bane yake Basu wahala, Da zarar an maida hankali dakuma Fayyace Fomulolin warware jimlar zai zama mafi sauƙi.

See also  Tasirin Fasahar ‘Artificial Intelligence’ a Duniyar Zamani

•Ko akwai wani Mutum Na musamman dayakamata yanemi BSc. Mathematics?

✓Amsar ita ce duk wanda ke da sha’awar gaske da batun ilimin lissafi, ko ilimin yaren computer, zasu iya shiga wannan fannin.

Daliban da ke tunanin yin BSc. Maths ya kamata su tabbatar da cewa suna da halayen Juriya a karatu dakuma Naci da yawan bibiya, ga Wasu matakai:

Mai da hankali: Shin za ku iya tsayawa mai da hankali a wani wuri na musamman? Math jigo ne da ke buƙatar mayar da hankali, bawai kawai Abu me wuya bane
Sauran sun haɗa Da:
Calmness
Patience
Confidence
Observation Skills.

Wasu daga cikin Darussa ko subjects a matakin Farko:
Algebra
Differential Calculus & Vector Calculus
Vector Analysis & Geometry
Integral Calculus & Trigonometry
Advanced Calculus
Mathematical Methods
Differential Equations
Mechanics
Probability Theory
Linear Programming and Optimization.

Koda Yake Ga Tsarin Jadawalin ga kowacce Shekarar Karatu a Nigeria: (Wasu Daga Ciki muka ambata a Dunƙule bamu fayyace Elective Da Core ba)

♦Level 100 Both First And Second Semester:

Introduction To Computing

Sets and Number

Trigonometry and Coordinate Geometry

Differential and Integral Calculus 2

Mechanics

Heat and Properties of Matter

Algebra 2

Conic Sections and Applications of Calculus

Vectors and Dynamics

Statistics Introductory

♦Level 200 Both First And Second Semester:

Mathematical Methods I

Real Analysis I

Abstract Algebra I

Linear Algebra I

Numerical Analysis I

Discrete Probability Distributions

Elementary Differential Equations I

Real Analysis II

Abstract Algebra II

Linear Algebra II

Continuous Probability Distributions and Distribution Techniques

Fortran and Structured Programming

♦Level 300 Both First And Second Semester:

Mathematical MethodsII

Advanced Real Analysis I

Theory of Rings & Fields

See also  BSC. PHYSICS; ilimin Kimiyyar Ƙwayoyin Halitta Da Makamashi

Complex Analysis I

Analytical Dynamics I

Mathematical Modeling 3

Axiomatic Set Theory

Number Systems and Algebraic Structures

Numerical Analysis II

SIWES (Tsawon Second Semester)

♦400 Level Both First And Second Semester:

Differential Equations

General Topology I

Theory of Finite Groups

Advanced Real AnalysisII

Hydrodynamics I

Quantum Mechanics

Biomathematics

Graph Theory and Combinatorics

Functional Analysis

General Topology II

Group Representations and Characters

Measure and Intergration

Partial Differential Equations

Hydrodynamics II

Complex Analysis II

Differential Geometry

Electromagnetic Theory and Waves

Analytical Dynamics II

Operations Research

Note: Mu Lura Cewa wannan Tsakure ne mukayi kuma abubuwan na iya chanjawa Bisa ga La’akari Da makarantun.

Bugu Da Ƙari Ga Kuma Wasu Ɓangarori Da Ɗaliban Math Zasu iya Karatu a matakin karatu na Gaba:

Master of Computer Applications

Master of Business Administration

PG Certification in Data Science

Master of Science in Data Science

PG Certification in Machine Learning

PG Certification in Machine Learning & Deep Learning.

Batun Aiki kuwa abun Ba’a Cewa Komai Domin kuwa ko ina kuma ko yaushe ana Rububin Ɗaliban daskayi Bsc mathematics Matuƙar sun kammala karatun Da Ƙwarewar su.

Ga Kaɗan Daga Cikin inda Ɗaliban Math Zasu iya Aiki:

Accountancy & Professional Service
Management Consultant
Underwriter
Actuarial Profession
Bank PO
Investment Banking
Retail Banking
Multimedia Designer
Public Administrator
Policy Analyst
Lecturer/Professor
Meteorologist
Computing & IT
Engineering Scientist
General Management
Operational Research
Space Scientist
Developer
Portfolio Manager
Statistician

©ASOF 2023(updated)
WHATSAPP
08086251045

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button