Ramadan
(DAUSAYIN RAMADAHAN) WAJABCIN AZUMI
WAJABCIN AZUMI
Azumi rukuni ne daga cikin rukunan musulunci biyar (5). Don haka yana da sharaɗin da ake yin sa.
Wajibi ne ga wanda yake yin azumi ya nesanci duk wani abin da zai ɓata mas azumi. Misali, kamar cin abinci,
- Shan abin sha,
- Saduwa da iyali da gangan.
- Kakaro amai da gangan,
- Janye niyyar azumin da gangan bayan an ƙullata.
5.Haka kuma yin ridda, wato fita daga musulunci.
Waɗannan abubuwa duka suna ɓata azumi. Don haka wajibi ne ga mai azumi ya nisance su. Kamar yadda Ibn Hazam da Ibn Abdil Barri da Ibn Taimiyyah suka hakaito ijma’in malamai a kan haka.
Wajibi ne mai azumi ya nisanci duk abin da zai ɓata masa azumi, tun daga ketowar alfijir na biyu wato alfijir na gaske, kamar yadda mafi yawan malamai suka tafi a kan hakan, kuma aka yi ijma’i a kansa.
Wanda alfijir ya keto yana cikin cin abinci ya zai yi? Sai ya furzar da wannan abincin da yake bakinsa, idan ruwa ne kuma sai ya zubar da su ka fin ya haɗiye, sai ya kurkure bakinsa ya ci gaba da azuminsa, amma idan kuwa ya ganganta yin hakan, to azuminsa ya ɓaci, wajibi ne ya rama shi bayan sallah.
Wannan shi ne ra’ayin malaman mazhabobin nan guda huɗu ma’abota sunnah, wato malikiyyah, shafi’iyyah, hambaliyyah, da hanafiyyah. Haka kuma shi ne ra’ayin Ibn Hazamin.
Hujjarsu ita ce fadin Allah ﷻ a cikin suratul baƙarah inda yake cewa :Ma’ana: ”ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana gare ku daga bakin zaren, (wato alfijir kenan sannan) sai ku cigaba da azuminku zuwa dare.” Wato kenan Allah ﷻ ya halatta a ci a sha tun daga faɗuwar rana har zuwa fitowar alfijir na biyu. Haka nan ya halattawa ma’aurata saduwa da junansu a wannan lokacin kai tsaye. Haka kuma ya tabbata a sunnah cikin hadisin Abdullahi Ɗan Umar wanda yake cewa, Ma’aiki ﷺ yana cewa, “lallai haƙiƙa bilalu yana yin kiran sallah ne da daddare (kafin alfijir ya fito) ku cigaba da cin abincinku ku sha abin shanku, har sai kun jiyo kiran sallar Ibn Ummi Maktum domin shi makaho ne baya kiran sallar har sai an ce masa kira sallar alfijir ya fito.”