Amfanin Bishiyar Darbejiya (Neem Tree) Ga Dan Adam
Azadirachta indica, wanda aka fi sani da neem, nimtree ko Indian lilac, bishiya ce a cikin dangin mahogany Meliaceae. Yana ɗaya daga cikin nau’ika biyu a cikin Azadirachta, kuma Yar asalin ƙasar Indiya ne kuma yawancin ƙasashe a Afirka. Yawanci ana girma a yankuna masu zafi da na wurare masu zafi.
Darbejiya tana ƙunshe da sinadarai waɗanda zasu iya taimakawa wajen rage matakan sukari na jini, warkar da ulcers a c hana daukar ciki, kashe kwayoyin cuta, da kuma kumburi a baki.
Kofi daya (gram 35) na ganyen neem ya ƙunshi:
45 kcal
2.48 grams na gina jiki
8.01 grams na carbohydrates
0.03 grams na mai
178.5 MG na calcium
5.98 MG iron.
Ba makawa idan ana batun darbejiya sai an danganta ta da kasar India. Tarihi ya nuna cewa India ce tushen wannan bishiya mai amfani ga dan adam.
Hakanan tarihin ya nuna cewa fiye da shekaru 4500 da suka gabata al’ummar India ke amfani da wannan bishiya a fannoni daban daban na rayuwa. Misali suna amfani da ita wajen maganin kwari, maganin tsutsar ciki, maganin Amosani, gyaran fata da na gashi da dai sauran cututtuka.
Ana amfani da duk sassan darbejiya, kamar ganye, yaya, rassa, saiwa, Kai Harda Man Darbejiya, da sassakenta don samar da magunguna masu amfani ko dai ga lafiyar ko muhallinmu.
Ba komai yasa muke kawowa mai karatu ire-iren wannan bincike na masana ba sai don fa’idar da ake samu, sannan a gefe guda kuma Alllah ya kawo mu wani zamani da aka fara karkata hankali wajen amfani da tsirrai don samar da magani. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da illolin da ake samu daga amfani da magungunan zamani ba. Sanin ku ne cewa dukkan magungunan wannan zamani na dauke da abin da suke kira “side effect”. Shi kuwa amfani da abubuwa na dabi’a musammanma abincin da muke ci basu da wata illa ga lafiyarmu.
A yau za mu duba irin amfanin da darbejiya ke da shi ga rayuwarmu.
1. Lafiyar Hakora.
Mu al’ummar Musulmi mun yi dace da ALLAH ya kawo mu duniya zamanin Annabin karshe. Ba komai ya sa nayi wannan magana ba sai don idan mutum mai yawan bincike ne, to zai sha cin karo da mu’ujizojin Manzomu (S.A.W), kuma a kowanne fage na rayuwa. Misali idan aka zo fanni lafiya Dole duniya ta sallama masa a matsyinsa na kwararran likita. Sai ka ga yayi bayani game da wani abu shekaru fiye da dubu da suka shuda, amma yanzu kuma binciken zamani ya tabbatar da shi.
Tuni dai mun san Yadda Manzonmu (S.A.W) ya ke son aswaki da yawaita amfani da shi, harma da umartar al’ummarsa da amfani da shi. To tsaya ka ji.
Binciken masanan wannan zamani ya tabbatar da cewa yawan yin aswaki da icen darbejiya, ban da sanya hakora suyi fari, kuma yana kara karfin dasashi, ya hana ciwon hakori, ya kuma hana warin baki da kurajen baki. Bugu da kari yana riga-kafin wasu cutukan baki.
2, Gyaran Gashi.
Man yayan darbejiya na taimakawa wajen hana gashi yayi ja, hakanan yana hana karyewar sa. Don haka kenan yawan shafa man a gashi zai sa shi yai tsayi kuma ya kasance baki wuluk.
3, Maganin Zazzabin cizon sauro.
Ko da yake har zuwa yau din nan ba wani bincike da ya tabbatar da wannan ikirari, to amma shekaru da yawa da suka gabata ake amfani da ganyen darbejiya wajen maganin sauro. To sai dai kuma mun san cewa sauro ne ke haddasa wannan zazzabi.
Masana dai sun dukufa don gano gaskiyar wannan batu. Mu dai fatan alheri muke musu da fatan Allah yasa a dace.
4, Bushewar Fata.
Ga wadanda suke fama da bushewar fata idan suka juri amfani da man yayan darbejiya za su ga canji mai inganci. Haka nan amfanin da wannan mai na yin garkuwa ga fata don kareta daga kamuwa daga wasu cutukan fata.
5, Amosanin Ka.
Shi ma dangane da wannan matsala ta amosanin ka, za ai amfani da man darbejiyar ne. Za’a shafe kai ne da shi man sannan a wanke bayan kamar awa guda.
6, Maganin Ciwon Ido.
A lokacin da ake jin rashin dadin ido ko yayi ja, ko kaikayi sai a samu ganyen darbejiya a tafasa shi sannan a bar shi ya huce a wanke idon da shi, za’a ga abin mamaki.
7, Ciwon Kunne.
Idan ana fama da ciwon kunne sai a matse ganyen darbejiya a samu ruwan a hada da zuma a digawa a kunne.
8, Maganin Kurajen Fuska (funfus).
Ga mai fama da wannan matsala sai ya samu danyen ganyen darbejiya ya shanya shi idan ya bushe sai a dake shi don a samu garinsa, a kwaba shi da dare a shafe fuska da shi, idan gari ya waye a wanke.
Allah Yasa A Amfana