Lafiya

Amfanin da Ganyen Lamsur ke yi a Jikin Mutum



Lamsur daya ne daga cikin ganyayyakin da wasu da yawa ke amfani da shi a fannoni da dama, musamman ma a tafasa shi a rika sha kamar Tea, ko a yayyanka ganyen a sanya a abinci Arika ci da dai sauransu.

Wasu na amfani da shi ne kawai ba tare da sanin tarin amfanin da yake da shi a jikkunan da lafiyar mu ba. Tabbas Lamsur abu ne da yakamata mu cigaba da amfani da shi, idan har kuma bamu taba amfani da shi ba, ya kamata mu fara amfani da shi saboda bincike ya tabbatar kuma ya nuna cewa: Yana da matukar amfani a jikin mu da kuma lafiyar mu.

Ganyen lamsur nada matukar mahimmanci a jikin mutum domin yana warkar da cututtuka da dama a jikin mutum.

Akan hada ganyen lamsur a cikin abinci kamar shinkafa, faten dankali, faten tsaki da kuma sauran su domin taimaka wa jiki da lafiyar mutum amma wasu masanan ganyen sun ce ganyan ya fi amfani a jikin mutum idan aka ci shi danye, wato a kwada shi ko da dakakken kuli-kuli da kayan Lambu.

Masanan ganyen sun bayana irin amfanin da wannan ganye na lamsur ke yi a jikin mutum kamar haka;

1. Ganyan lamsur na maganin ciwon ido: Lamsur na da sanadarin dake maganin cututtukar da ke kama ido. Cin shi na da matukar Amfani.

2. Yana maganin hawan jini.

3. Cin ganyen lamsur na gyara fatar mutum. Lamsur na maganin Kyasfi dake kama fata. Ana nika shi a hada da man da ake shafawa ko kuma da ruwa a shafa a jiki. Yana gyara fata sosai.

4. Yana taimaka wa mutum cin abinci yadda ya kamata.

5. Yana maganin ciwon ciki kamar su zawo da sauransu.

6. Ganyen na kawar da ciwon zuciya.

7. Yana hana amai. Idan mutum yana yawan jin amai, lamsur na maganin shi.

8. Yana kara karfin kashi (Calcium)

9. Yana kara karfin namiji.

10. Cin Ganyen lamsur na kawar da warin baki.

11. Cin ganyen Lamsur na kawar da laulayin da mata kan ji idan su na jinin al’ada.

12. Yana rage kiba a jiki.

13. Yana warkar da rauni ko ciwo a jikin mutum.

14. Yana kawar da cutar siga.

15. Yana kara jini.

16. Yana daidaita jinin al’ada da izinin Allah.

17. Yana taimakawa masu fama da ciwon ƙoda da kuma Saifa.

18. Yana magance duk wata matsalar dake a mafitsara da izinin Allah, mace ce ke fama da ita ko namiji.

19. Yana kyautata numfashin mutum kuma yana taimakawa masu fama da ciwon Tari da Asthma (Asma).

YADDA AKE AMFANI DA SHI.

1. Za a samo ganyen lamsir sai a wanke shi sosai a tsaftace shi sai a samo lemon tsami kadan a hada shi da ganyen Lansir ɗin, sai a zuba musu ruwa kofi 3 a ciki, a dora a kan wuta abarshi yakai mintuna 30 sai a sauke kuma a tace, sai a sha kofi 2, tsakanin shan kofi na farko da na 2 a bar tazarar akalla mintuna 15.

2. A samo Ganyen Lamsir sai a tsaftace shi a cire duk wani ganye wanda ba kore ba a jikinsa, sai a yayyanka shi a zuba masa ruwa kimanin kofi 2 sai a tafasa shi, idan yatafasa sai a sauke shi a barshi yayi mintuna 5 bayan ya huce sai a tace shi a rika shan kofi 1 kullum da safe kafin aci abinci.

3. A tsaftace kuma ayayyanka ganyen lamsur din sai a sanya shi a tafasa da ruwa, sai a barshi ya huce kuma a sanya shi a cikin wuri mai sanyi kamar firjin da ta yadda zaiyi sanyi ba sosai ba, sai a rika shan kofi 1 da safe 1 da yamma.

Allah Ya Bada Sa’a

See also  Macen da ke Jinin Haila PAD Nawa ya kamata tayi amfani dashi kullum ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button