Jamb
Trending

Yadda ake karanta Past Questions

YADDA AKE KARANTA PAST QUESTIONS

Karatun Past Questions abu ne mai matuƙar sauƙi. Sai dai, ba a na karanta su ne kamar, littattafan labarai (Novels), ko Jaridu (Newspapers) ba, domin kuwa akwai abubuwa uku da ake buƙatar samu dangane da tambayoyin, wanda su ka haɗar da, karanta su, fahimtar su, da ma gwada su a aikace.

Bari mu je, kan yadda tsare-tsaren karatun su ya ke :

• Ku dinga farawa da karanta Littattafanku :

Babban kuskuren da akan samu, ga ɗalibai da dama (musamman masu karatu, domin rubuta jarrabawar JAMB), shi ne tsunduma karatun Past Questions da su ke yi kaitsaye, ba tare da samun ko da ƙanƙanin Ilimi ne, game da Topics ɗin da tambayoyin ke fitowa daga cikin su ba, ta hanyar amfani da JAMB Syllabus, na kowanne darasi (Subjects).

Zai fi kyau, kafin ku fara yunƙurin amsa kowacce irin tambaya a Past Questions, ku kasance kun yi karatu sosai, akan Topic ɗin da ta fito, daga littattafanku na karatu (textbook(s)).

• Ku zaɓi salon karatu :

Zaɓin salon karatu biyu da ku ke da shi, a ya yin nazartar past questions ɗin su ne: ku dinga amsa tambayoyin da su ka fito daga Topic guda zuwa wani, ko kuma ku dinga amsa kowacce tambaya, a lokaci guda.

• Ku karanta, ku fahimta, ku gwada amsawa, sai ku rubuta gaɓoɓi masu muhimmanci, a gefe :

Abu na farko, shi ne ku karanta Past Questions ɗin, ku kuma fahimci abin da tambayoyin su ke buƙata, sannan ku amsa su.

Ka zalika, ku tabbatar kun rubuta dukkannin wata gaɓa mai muhimmanci, ko darasin da ku ka samu, daga tambayoyin.

See also  Tambayoyin dake yawan fitowa a Jarrabawar JAMB a Chemistry tare da amsa

• Ku duba amsoshin ku :

Ku tabbatar kuna duba littattafan karatu (textbooks), domin gyara amsoshin da ku ka gaza bayarwa dai-dai, ko kuma ku ke da shakku akai.

• Ku yi ta maimaita tambayoyin da ku ka amsa :

Ka da ku ce, ”na amsa wannan tambayar, dan haka ba zan koma gareta ba”, Ku tabbatar kun cigaba da amsa tambayoyin zuwa abin da ya sauwaƙa.

Kwatankwacin Karatun Ku!, Kwatankwacin Shirin Ku Ga Jarrabawa!.

Rubutawar ✍️ : Miftahu Ahmad Panda.

08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button