Tambayoyi a Musulunci

ZAN IYA SANYA ZOBEN AZURFA A DAN YATSAN DAMA?Tambaya:
Assalamu Alaikum Malam ga wata tambaya nan kamar haka: Assalam da fatan kana lpy! pls ga tambayana menene hukuncin sa AZURFA ZOBE a hanun dama shin akwai wata illa ne koh kuma manzon Allah baisaba???

Amsa:
To dan’uwa ya halatta a sanya zoben azurfa a karamin dan yatsan hagu da kuma dama, Nawawy ya hakaito Ijma’in kasancewar hakan Sunna, saidai akwai hadisi mai lamba ta: 2078 a Sahihi Muslim wanda yake nuna haramcin sanya zobe a dan yatsan tsakiya da wacce take binta, wasu malaman kuma sun dauki hanin a matsayin karhanci ba haramun ba.

Allah ya saka da alkairi.

Don neman karin bayani duba Al-majmu’u na Nawawey 4\340.

28\12\2015
‎Dr. Jamilu Zarewa.

See also  ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA CONDOM ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button