Tasirin Fasahar ‘Artificial Intelligence’ a Duniyar Zamani
Duk da hasashen farfesa Stephen Hawking da gargadin Elon Musk, kan cewa fasahar Artificial Intelligence kan iya zama wata barazana ga rayuwar Ɗan-Adam a duniyar zamani, amma har yanzu masana wannan fasaha suna ƙara zurfafa bincike don tabbatar da lamarin wannan fasaha ya tabbata na wuce gona da iri.
Ko kasan nan da shekaru 20 sama da ayyuka 100 waɗanda mutane ke yi fasahar AI ce za ta maye gurbinsu? Tuƙi, aikin banki, lissafi, cinikayya da sauransu sune muhimman ayyukan da fasahar AI za ta kwace, a inda kuma tuni tana taimakawa a muhimman wurare sama da 50.
A yau, a kullum muna amfani da fasahar AI a duk wasu lamuranmu na wayoyin hannu, na’urori ko yanar gizo. Misali, a kamfanin Google akwai irinsu DeepMind, Self-driving car, Google Now, Google Search, YouTube da sauransu.
A yanzu wannan fasahar tana fahimtar irin abubuwan da ka fi so, ko waɗanda mutanen yankinka suka fi nema, ko wanda zai iya dacewa da shekarunka da dai sauransu musamman idan kana bincike a shafin Google ko neman bidiyoyi a YouTube.
Haka nan, za ka iya yin magana kai-tsaye fasahar ta fahimci me kake nema, ko me kake son ta yi maka a manhajar Google Now a wayoyin Android, ko kuma amfani da manhajar Siri a wayoyin iPhone ƙirar kamfanin Apple.
Ba wannan kaɗai ba, akwai fiƙirar motoci masu tuƙa kansu, waɗanda kawai shiga cikinsu za ka yi tare da faɗa musu inda kake so ka je, su da kansu za su tuƙa ka su kai ka wajen ba tare da samun matsala ba. Suna da fiƙirar gane komai da ke kan hanya kamar mutane, ababen hawa, alamun kan hanya da sauransu.
Akwai saƙagai waɗanda ake ƙirƙira a matakai da dama, kamar masu siffar mutum, masu aiki a masarrafa, masu aiki a cikin na’ura da kuma masu aiki a matsayin manhajoji.
Amma duk waɗannan taimako da fasahar AI take ƙoƙarin kawo wa duniyar zamani, da dama daga cikin mutane suna tsoron zurfafa bincike a kan fasahar, saboda tsoron barazanar da ake tunanin za ta iya haifarwa.
Masu hangen nesa suka ce bazaranar da fasahar za ta iya haifarwa shi ne lokacin da aka ba ta fiƙira da tunani da basira irin na Ɗan-Adam, a wannan lokacin injinan da suka fi Ɗan-Adam ƙarfi za su buƙaci yin rayuwa mai ‘yanci ta karan-kansu.
Wataƙila su iya samun shauƙi da ƙarfi wanda ya fi na Ɗan-Adam; a inda kuma shauƙi ya kasance babbar barazana ga rayuwar Ɗan-Adam wanda yake da ilimin zamantakewa da dabi’un hani ga abunda bai kamata ba, ballantana kuma inji da ba shi da wannan?
Suka ce a wannan lokacin na’urorin da suke da wannan fasaha, musamman saƙagai, za su kasance kamar ƙattin ƙauye ne – wato waɗanda jahilci, da wauta, da rashin hankali ya dabaibaye su, amma suna da matuƙar ƙarfi, ta yadda za su iya yin fashi da makami ko zalunci don ba su san illarshi ba.
Haka nan za a iya amfani da wannan fasaha ta gurɓatattun hanyoyin da ba su dace ba don gurɓata fasaha ko dabbaka raunin tunani, ko kuma amfani da ita wajen sarrafa makaman yaƙi ko kuma a matsayin makami.
Shin me kake tunanin zai faru a lokacin da fasahar AI ta samu cigaban da fiƙirarta, da basira, da karfi, da ilimi, da nazari ya yi wa na Ɗan-Adam fintinkau?
—Mohiddeen Ahmad
04/02/2022