Tarihi

TARIHIN SHIEKH MUHAMMAD NASURUDDIN ALBANI. مُحَمَّد نَاصِر ٱلدِّيْن ٱلْأَلْبَانِي الأرنؤوط)

TARIHIN SHIEKH MUHAMMAD NASURUDDIN ALBANI. مُحَمَّد نَاصِر ٱلدِّيْن ٱلْأَلْبَانِي الأرنؤوط),

Sharar Fage

Malamansa.

Babban malamin Albani shi ne mahaifinsa. Haka kuma, ya yi karatu a wurin Muhammad Saeed Al Burhani; inda ya karanci wani littafi mai suna ‘Maraqi Al Falah’ na Fikihu Hanafiyya, da ‘Shadoor Al Dhahab’, na littafin Nahawun Larabci,da wasu littafai na zamani kan lafuzza. Haka kuma ya kasance yana halartar darussan Muhammad Bahja Al Bitar, malami.

Daga baya rai da mutuwa.

Tun daga 1954, Albani ya fara ba da darussa na yau da kullun na mako-mako. A shekara ta 1960, farin jininsa ya fara damun gwamnati, kuma an sanya shi a karkashin kulawa. An daure shi sau biyu a shekara ta 1969. An tsare shi a gidan kaso fiye da sau daya a cikin shekarun 1970 ta hannun gwamnatin Baath na Hafez al-Assad Na Kasar Syria. Gwamnatin Siriya ta zargi Albani da “inganta wahabiyanci A da’awarsa wanda ya ke gurbata Musulunci da rikita Musulmi.” A cewarta.

Ra’ayi.

Albani ya kasance mai goyon bayan Salafiyya, kuma ana daukarsa daya daga cikin manyan jigogin kungiyar a karni na 20. Albani ya soki mazhabobin shari’ar Musulunci guda hudu na al’ada, ya kuma yi watsi da ra’ayin Ahlus-Sunnah na gargajiya na cewa musulmi su koma mazhabar fiqhu kai tsaye. Maimakon haka, ya shafe tsawon rayuwarsa yana nazari kan sake nazarin littattafan hadisi kuma yana jin cewa hadisai da yawa da aka karba a baya ba su da inganci. Wannan ya sa ya fitar da hukunce-hukuncen da suka yi hannun riga da mafi rinjayen Musulmi.

Tsarin Sallah (Sallah)

Albani ya rubuta littafi wanda a cikinsa ya sake fayyace ishara da sifofin da suka dace da suka kunshi ibadar sallar musulmi “Kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi wa Sallam ya yi.” Wadannan sun saba wa ka’idojin dukkan mazhabobin fikihu da aka kafa.

Kamar yadda ya bayar da hujja dalla-dalla game da Salloli da aka koya daga tsara zuwa tsara sun dogara ne akan hadisin shubuha, littafinsa ya haifar da tashin hankali. Albani ya yi bayanin yadda ake gudanar da sallar Tahajjud da Taraweeh ya saba sosai da Yadda A ka Saba.

Rigingimu

Albani yana da ra’ayoyi da dama masu kawo sabani da suka yi hannun riga da ijma’in Musulmi musamman ma fikihun Hanbali. Waɗannan sun haɗa da:

1, Ra’ayinsa na cewa mihrabobi – guraren da aka samu a masallatai masu nuni da alkiblar Makka – bidi’a ne

2, Ra’ayinsa na halascin yin sallah a masallaci da takalminsa.

3, Kiran da ya yi ga Falasdinawa da su fice daga yankunan da aka mamaye tun a cewarsa, sun kasa gudanar da addininsu a can kamar yadda ya kamata. Wannan ra’ayi kuma ya kasance da sabani a cikin harkar Salafiyya.

4, Ra’ayinsa na cewa an haramta wa mata sanya mundaye na zinariya.

5, Ganinsa na cewa ba lallai ba ne mata su rufe fuska Ba.

6, Ra’ayinsa na cewa dole ne shugaban musulmi ya fito daga kabilar kuraishawa.

See also  TARIHIN OMAR AL-MUKHTAR

TARIHIN RAYUWAR SHEIKH MUHAMMAD NASIRUDDEEN ALBANY


Muhammad b. al-Haj Nuhu b. Nijati b. Adam al-Ishqudri al-Albani al-Arnauti, Wanda Aka Fi Sani Da Al-Albani, Malamin Addinin Musulunci Ne Dan Kasar Albaniya, Kuma Mai Sa Ido, Wanda Musamman Shahararren Malamin Hadisin Salafiyya Ne.

Ga Abinda Ya Fada Da Kansa


Sunana Muhammed NasiruddeenNooh Najaatee Albany An Haifeni A Garin Ashkodera ( Wani birni ne a Arewa maso Gabashin Kasar Albania ) A Shekarar 1332H ( 1914 C.E) A Zamanin Yakin Duniya na daya, Ya fito Daga Iyalai Masu Fama Da Talauci.

Mahaifina Al- Haajj Nooh Najaatee Al-albany Yayi Karatun Shari’ah A Birnin Istanbul Na Kasar Turkiyyah daga baya ya dawo Kasarmu Ta Albania a matsayin Malamin Addinin Musulunci sai dai sakamako yadda Hukumomin kasar Albania na lokacin suke bin tsarin mulki wanda ba ruwansa da addini wajen jagorantar kasar, sai Mahaifina yaga bazai iya zama A karkashin wannan
mulkin ba sai yayi hijira tare damu iyalansa zuwa Birnin, Damascus Na Kasar ( Syria ), Inda na fara karatuna a nan nayi
Karatun Alqur’ani Mai Girma DaTajawid, Larabci, Da Fiqhun Mazahabar Hanafiyya, da sauran bangarori na Addinin Musulunci a wurin Mahaifina, Abokan Mahaifina da Sauran Malamai da dama.

Nafara sana’ar Kafinta daga baya na ci gaba da koyon Gyaran Agogo a wurin mahaifina inda na zama kwararren mai Gyaran Agogo.

Sheikh Nasiruddeen Albany yana dan shekaru Ashirin ( 20 ) ya fara shahara a bangaren Ilimin Hadisi. Sheikh Albany ya samu karbuwa da daukaka sakamakon rubutun da ya Ke Yi A mujallar Al-Manaar dake fitowa sati-sati. Sheikh Albani Ya ci gaba da neman limin Hadisi da kimiyarsa gadan-gadan duk da rashin Samun kwarin gwiwa da yake samu daga wurin Mahaifinshi, sakamakon ‘Yafi son Ya samu kwarewa akan Mazahabar
Hanabili. Saidai kuma mafi yawan litattafan da yake bukata domin karatu musamman na Hadisi da kimiyarshi basu a dakin Karatun Mahaifin Nasa, kuma bashi da halin mallakarsu a wannan lokaci sabo da haka sai ya Rinka Amfani da Dakin
Karatu mai suna “Al- Makattabah Al-Zahiriyyah”

Sakamakon Himma da Sheikh Yake da ita da kwadaituwa
wajen neman Ilimi Musamman na Hadisi, sheikh ya rinka kwashe Sa’o’i masu yawa yana karatu a cikin wannan dakin karatun don ance yakan Kwashe fiye da 12, Yana karatu da Bincike a wannan dakin karatu batare da ya ba Abinci mahimmanciba, sai dai abinda ba a rasaba, domin rayuwa ta gudana yana fita ne kadai idan lokacin Sallah yayi. Sakamakon Himmah da Mada hankali ga karatu na sheikh Albani
yasa masu kula da Dakin karatun suka ware mashi dakin na
Musamman tare da mallaka masa daya daga cikin mabudan shiga Dakin Karatun Zahiriyyah .

Sheikh yayi zurfi acikin Ilimin Hadisi kuma hakan yayi tasiri gareshi, yasa wanke mashi samun kyankyawar fahimtar sunnar Manzon Allah( SAWA) wanda hakan ya ya bashi kariya daga Makauniyar biyyah Ga Mazahabobi zuwa ga bin Qur’ani da
Sunnah a bisa fahimtar magabata na Kwarai.

Sheikh Albani ya Rinka samun Ta-ta-burza tsakaninsa da malaman wannan zamanin, musamman masu Yiwa mazahabobi makauniyar biyayyah da Sufaye da Mabiya kungiyoyin Bata, wadanda suka rika zuga Mutane tare lakabamashi sunaye don bata mashi suna. Amma a hannu daya akwai Malamai bayin Allah da suke karfafa mashi Gwiwa a koyaushe.

Sheikh Nasiruddeen Albani ya gamu da gagarumar adawa wajen
kokarinsa na karantar da Tauhidi da sunnah bisa fahimtar magabata na Kwarai. A lokacin Sheikh Nasiruddeen Albani ya Rinka koyar da Malamai da daliban Jami’a da sauranal’ummah Ilimomin Aqidah, Fiqh, Usul da Ilimin Hadisi sau biyu a Mako. Sannan kuma Mallam ya rinka tafiya Da’awah a Kasar Syria, kasar Jordan, Iraq Lebanon da sauran wurare.

Sheikh Albany ya taba kasancewa daya daga cikin Malamai a Jami’ar Musulunci ta Madina inda ya Koyar da Hadisi a cikin shekarun 1381 zuwa 1383 Hijirah.

Sheikh Albany ya fuskanci matsaloli a rayuwa wanda hakan yasa ya Rinka yin Hijirah daga Syria zuwa sauran kasashe Makota Kamar Jordan, Beirut da Hadandiiyar daular Larabawa ( UAE ????????)

Sheikh Albany ya zagaya kashen duniya dayawa domin isar da Sakon Allah ( Wa’azi ) daga cikin kasashen da yaje sun hada da Qatar, Egypt, Kuwait, Spain, United Kingdom da Hadaddiyar Daualar Larabawa. ( UAE ???????? )

Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albany ya shafe rabin karni
( Shekaru 50 ) yana koyon Ilimin Hadisi da kimiyyarsa wanda hakan yasa yazama mafi shahara a wannan ilimin cikin wannan Karnin ( Malamai sun tabbatar da hakan ) Sheikh Albani Yayi rubuce-rubuce a bangarorin addinin musulunci da dama Musamman a bangaren hadisi da kimiyarsa tare da gabatar da makaloli a wurare da yawa. A yanzu haka daliban Malam sunan a ko ina a sassan Duniya.

Allahu Akbar: Sheikh Muhammad
Nasiruddeen Albany ya rasu a Ranar
22 Jumadda Sani 1420 Hijjara
wanda yayi daida 2 Aktoba 1999 C.E
yana da Shekaru 85.

See also  Tarihin Annabi Yahya (AS) (Yohanna Mai Baftisma)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button