Tarihi

Tarihin Annabi Yahya (AS) (Yohanna Mai Baftisma)



Yaya ibn Zakariyya (AS) (Da Larabci: یحیی بن زکریا ) ko kuma Yahaya (AS) Annabin bani Ba’isra’ila ne. Ya zama Annabi tun yana yaro. duk da mahaifinsa Ya tsufa kuma mahaifiyarsa bakarariya ce (Juya Mara Haihuwa) ya zo a cikin Alkur’ani, Yahya (AS) ya kasance sananne ne da Yawan Ibada da yawan kuka Saboda tsoron Allah.

Haihuwa

Annabi Zakariyya (AS), mahaifin Yahaya (AS) bai Sami haihuwa ba har ya tsufa. Watarana ya ga Maryam (AS) da ni’imar da Allah Ya yi mata, (Na Samun Haihuwar Annabi Isa AS) sai ya roki Allah da ya ba shi Da’:

“Ya Ubangijina! “A cikin Addu’arsa ya ambaci rashin magajinsa da tsoronsa daga danginsa bayan rasuwarsa. Sai Allah ya yi masa alkawari cewa zai haifi ɗa mai suna Yahya duk da cewa ya tsufa kuma matarsa bakarariya ce.

Mahaifiyar Yahaya (AS), Alisabatu, kanwar Maryamu ce (Mahaifiyar Annabi Isa AS) Wasu sun ce Sunan Yahya ya samo asali ne daga tushen hyy (ya rayu) (Larabci: ح-ی-ی ) Allah ya halicce shi da imani ko da annabci Ba wanda aka taba kira da suna Yahya kafin shi.

Annabta

Yahya (AS) ya zama Annabi tun yana karami. Ɗaya daga cikin halayensa shi ne kasancewarsa mai gaskata Annabi Isa (AS). Yahya (AS) ya bi kuma ya inganta shari’ar Annabi Musa (AS), amma lokacin da Annabi Isa (AS) ya zama annabi sai ya bi shi.

A cewar Ruwayoyin tarihi, Annabi Isa (AS) ya girmi Annabi Yahya (AS) watanni Goma Sha shida kuma shi ne mutum na farko da ya tabbatar da kuma gaskata Annabi Isa (AS). Domin ibadarsa da Da kyawun Halayensa ya rinjayi mutane da yawa su gaskata da shi.

Tabataba’i yana cewa “littafin” da aka ambata a cikin Kur’ani cewa Yahya (AS) ya umurci ya yi riko dashi shi ne Attaura

Shahada

Kamar yadda wani hadisi daga Imam Sajjad ya nuna cewa, wani sarkin Isra’ila ya kamu da soyayya da daya daga cikin ‘yan uwansa muharramai kuma yana son ya aure ta. Yahya (AS) ya yi adawa da wannan shawarar, kuma adawarsa ta kai ga kiyayyar yarinyar da mahaifiyarta a kansa. A sakamakon haka ne mahaifiyar yarinyar ta sa ‘yarta ta nemi kan Yahya (AS) a matsayin sharadin auren. Sarkin Isra’ila ya yarda ya fille kan Yahya (AS) ya aika da kansa a cikin farantin zinariya ga yarinyar.

Halayen ɗabi’a

Daga cikin sifofin Yahya (AS) an ambace su musamman: Imani da Annabi Isa (AS), jagoranci ta fuskar ilimi da aiki, Annabi ne salihi, zakka da Taimakawa bayin Allah.

A game da taqawa, an ambaci cewa ya kasance yana kuka mai yawa don tsoron Allah.

Yahya (AS) a cikin Alkur’ani

Sunan Yahya (AS) ya zo sau biyar a cikin surori hudu na Alkur’ani Labarin Haihuwarsa da kasancewarsa mai baiwar hazaka da wasu daga cikin kyawawan dabi’unsa sun zo a cikin Alkur’ani. A cikin Kur’ani 19:15, “Aminci ya tabbata a gare shi, ranar da aka haife shi, da ranar da zai mutu, da ranar da ake tayar da shi yana mai Rai.

Wurin binne shi

An samu sabani kamar inda aka binne Yahya (AS) wurin da ya fi shahara shi ne wani kabari a cikin masallacin Umayyawa, wanda ake kyautata zaton wurin ne aka binne gawar Yahaya (AS) Wacce babu kai, kuma ana kyautata zaton cewa kansa ne aka binne shi a wani masallaci da ke unguwar Zabdani a birnin Damascus. Wasu Ruwayoyi sun ce an binne kan Yahya (AS) a cikin kabari da ke masallacin Nabi Yahya a kauyen Sebastia na Falasdinu. Har ila yau Kiristoci sun gina coci a kusa da wannan masallaci mai suna Church of St. John the Baptist.

Mandaiyawa

Mutanen Mandaiyawa suna daukar kansu a matsayin mabiyan Yahya (AS). A cikin Masallacin Umayyawa da ke Damascus, akwai wani abin tunawa da aka fi sani da kabarin Yahya (AS).

Mandaiyawa mutane ne masu yaren Aramaic waɗanda suka gaskata cewa suna bin Yahaya (AS) kuma littafinsu na Yahya (AS) ne. An yi imanin cewa hijirarsu zuwa Iran ta faru ne a lokacin daular Farisa. Baya ga yahudawa suna daya daga cikin bakin haure na farko wadanda ba ‘yan kabilar Aryan ba wadanda suka je Iran daga Falasdinu. Mandaiyawa masu tauhidi ne, Suna da nasu nassi, harshe, da rubutu. An ambace su a cikin Alkur’ani a cikin ayoyi da dama.

See also  Shaka Zulu: Tushen al'ummar Zulu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button