(DAUSAYIN RAMADAHAN) FA’IDOJI GOMA DA MAI AZUMI ZAI SAMU
1. Duk wanda yayi azumin watan Ramadhan za a gafarta masa abin da ya wuce na zunubinsa.
2. Duk wanda ya yi sallar dare a watan Ramadhan za a gabatar masa abin da ya wuce na zunubinsa.
3. Duk wata yayi Tsayuwar dare a cikin daran lailatun ƙadri za a gafarta masa abin da ya wuce na zunubinsa.
Daga cikin faidojin da mai azumi ya ke samu shi ne, ƙarin Taqwa( لعلكم تتقون) ita kuma Taqwa ita ce komai idan mutum ya sami Taqwa ya sami komai na duniya da lahira.
4. Son Allah zai ƙaru a cikin zuciyar mutum da
Girmama shi zai ƙara ƙarfi a cikin zuciyar musulmi.
5. Ƙaunar rahmar Allah da kwaɗatin samun ta zai ƙaru a cikin zuciyar musulmi da ƙara dagewa wajan neman ta da iklasi da bin Sunnah.
6. Tsoran azabar Allah zai ƙaru a cikin zuciyar musulmi da kuma yin aiki da addu’a domin wata da ake ƴanta bayi daga wuta.
7. Bin umarnin Allah, da bin dokokin sa da daɗin rai zai ƙara tasiri a cikin zuciyar sa, Zai ƙara dagewa wajan abin da Allah ta’ala yake so kuma ya yarda da shi.
8.. Nisanta daga abin da Allah ya hana, tare da jin daɗin haka, zai ƙara rage yawan sha’awar saɓo da jin daɗin aikata shi, da gujewa duk abin da zai jawo fushin Allah ta’ala.
9 . Godiya da ni’imar Allah, a zuciya da baki da gaɓɓai, da aiwatar da ita wajan yin abin da Allah ta’ala ya ke so kuma ya yarda da shi. ( لعلكم تشكرون )
10. . Hak’uri wajan bin Allah da hak’uri ga barin saɓon Allah, da hak’uri wajen ɗauke raɗaɗi da zogin jarrabawa ta ƙaddara da za ta sami mutum a kowanne hali.
إنما يوفي الصابرون أجرهم بغير حساب
Iklasi da yin abu domin Allah kawai zai ƙaru a cikin rayuwar musulmi, domin babu wanda yasan mai azumi sai Allah ta’ala, do haka Azumi alaƙa ce kai tsaye tsakanin Allah ta’ala da bawan sa, yace”( الصوم لي وانا اجزى به) Azumi nawa ne ni nake sakayya da shi “
Tuba daga laifuka da yin nadama akan wanda ya wuce da cika sharaɗin tuba tsanani da Allah. إن الله يحب التوابين ويحب المتطهرين.
Wannan shi ne Mai azumi zai auna kansa da shi bayan Ramadan domin ya ga irin tasarin da azumi ya yi akan sa.
Allah ka karɓi azumin mu, don rahmaKa da jin ƙanKa.